African LanguagesHausa

Shin wadanan mata na zanga-zanga ne don adawa da shirin maza na auren mace guda a Finland kamar yadda ake fadi?

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Mata a kasar Finland sun yi zanga-zanga kirjinsu zindir saboda maza na auren mace daya kawai, yayin da ake kara samun yawaitar mata a kasar. 

Shin wadanan mata na zanga-zanga ne don adawa da shirin maza na auren mace guda a Finland kamar yadda ake fadi?

Sakamakon bincike: Karya ne! Sabanin da’awar da aka yi, matan da aka gani a bidiyon na zanga-zanga ne saboda ci da gumunsu wajen bayyanar da tsiraicin jikinsu inda suke neman a ba su kariya. Babu wata alaka ta zanga-zangar da maza. Ba a fahimci bidiyon ba saboda banbanci na harshe.

Cikakken Sakon

Ana samun labarai a shafukan sada zumunta wadanda ke zama ba masu dadi ba kan mata. Wasu lokutan saboda yadda wasu suka yi amanna, mace na da rauni ko kuma rashin fahimta. Musamman a kasashen Afurka inda ake tsammanin ganin matan sun mika wuya ga mazajensu. Ko ma a wasu lokutan kannensu ko ‘ya’yansu.

Yayin da a kasashe da suka ci gaba matan ke fafutika ta sauya wannan fahimta, wasu da ke amfani da shafukan sada zumunta na zuwa da labarai da za su nunar da mazan ke kan gaba  ba za a iya sauya su ba, ko ma rayuwar matan na a hannunsu.

Wannan na iya zama misali kamar irin bidiyo da mai amfani da shafukan sadarwar@CadreShangri yayi ne. 

A wannan bidiyon an ga mata na tafe kirjinsu a bude suna dauke da alluna da aka yi rubutu a jikinsa a harshen Faransanci. An kuma jiyo matan na magana da harshen na Faransanci . A babban kyalle dauke da rubutu an sanya ( “Non a l’hypersexualization. Liberons Les Tetons!”) ma’ana dai suna adawa da ci da gumin mata ta hanyar bayyanar da tsiraicinsu.

Ga wadanda basu fahimta ba, wannan wani abune da ke da alaka da batun jimi’ai, alakar mace da namiji ko jinsi.

Wani mai amfani da shafin na X ya rubuta a bidiyon, “Mata a kasar Finland na adawa da tsarin maza na auren mace guda. Suna bukatar mazajen su rika auren mata sama da guda, ganin yadda matan ke kara yawa cikin al’umma ba tare da mazajen da za su aure su ba.”

Wannan mutum ya kara da cewa “A cewar ZimStats, idan kowane dan kasar Zimbabwe zai auri mace guda daya, za a bar mata 700,000 ba tare da mazaje ba! Wannan abin dubawa ne!”

A ba shi amsa da aka yi, Cadre yace , “Ina bibiyar dubban tsokaci da aka yi maka da miliyoyin martani. Ni kawai na ga fushi yadda mata ke bayyana ra’ayinsu. Duk da haka menene matsala, idan matan sun nemi maza su auri sama da mace guda? Mu fara tattaunawa yanzu.” 

Yayin da shafin DUBAWA cikin hanzari ya duba jinsin wannan mai amfani da shafin na X, mutumin na da ra’ayin goyon bayan auren mace sama da guda daya.

Kawo lokacin hada wannan rahoto wannan bidiyo da aka wallafa ya samu wadanda suka kalle shi (views) daga miliyan biyar zuwa miliyan bakwai, an sake yadawa (repost) sau 6,000. Ya kuma samu masu nuna sha’awa (likes) 17,000. Wasu kuma cikin raha sun nuna sha’awarsu ta zuwa kasar Finland don su auri mace.

Tantancewa

Kasancewar harshen Faransanci ba shine babban harshe da ake amfani da shi ba a Finland, shafin DUBAWA ya yi mamakin me yasa a alluna da ke kan titin rubutunsu ya kasance a harshen Faransanci baya ga matan da ke kururuwa da harshen. Wannan ya sanya mu gudanar da bincike.

Da fari DUBAWA ya yi kokarin gano asalin bidiyon ta hanyar amfani da fasahar (INVID verification plug-in.) Mun lura cewa an wallafa wannan bidiyo a shafin (website) shekaru hudu da suka gabata, aka sake wallafawa shekara guda da ta gabata.

Abin da aka rubuta kawai shine (“We need to support this strike.” ) Ma’ana “akwai bukatar tallafawa wannan yajin aiki” Babu wani karin bayani kan asali ko dalilin zanga-zangar.

Karin wasu abubuwan da aka gano ya nunar da cewa abin da mai amfani da shafin na X ya wallafa (posted ) ya kwafo ne daga asalin bidiyon wanda ya fito daga wani shafin Instagram da ba a tantance ba.

Yayin da yayi rubutu cikin harshen Farsi fassara a harshen Ingilishi na cewa.”Kamar a kasar Poland mutane na zanga-zangar adawa da zinace-zinace saboda rashin jima’i, sannan alamu sun nunar da cewa babu mutumin da zai gamsar da mu. Shin akwai wanda ya san yadda za a samu bizar kasar Poland?”  

An wallafa a shafin Twitter a watan Agusta, 2021, yayin da kuma an kwafa ne daga shafin Instagram da aka wallafa a watan Yuli na wannan shekara.

DUBAWA ya lura cewa wannann bayani da aka wallafa an rika maimata wallafa shi ( reshared) sau da yawa. Duk wallafar da aka yi sai a ba ta da’awa ta daban (narratives.) wasu na cewa a bidiyon a kasar Finland, wasu na cewa mata masu zanga-zanga a Venezuela. Duk dai kowane bidiyon da aka wallafa sai a ce maza na raguwa yayin da mata ke bukatar wadanda za su gamsar da su ke raguwa. Za a iya ganin wasu nan (here) da ma nan  (here.)

A wani labarin DUBAWA yayi nazari a kan bidiyon. Wasu matan dauke da alluna, babba a cikinsu shine da aka rubuta (“Non a l’hypersexualization. Liberons Les Tetons!) wanda ya nuna harshen Faransanci, idan aka yi fassararsa na nufin a dakata da ci da gumin mata, a kyale nonon mata ya sarara.”

Wani daga cikin allunan da aka rubuta an sanya (“mon corps est sexuel sije veux politique sije veux couvert sije veux nu si je veux”) ma’ana jikina na jima’i ne idan ina bukata, na rufe idan ina bukata, na tafi tsirara idan ina bukata.”

Wasu daga cikin abubuwan da aka rubuta kan allunan, na nuni da bukatar mata a kyale su  da ‘yancin amfani da jikin yadda suke so musamman matancinsu. A kwai kuma wata mace da ta sanya hula da ke da alama ta ‘yanfafutukar kare hakkin mata, wata kuma hadi da alama ta duniyar Venus.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button