African LanguagesHausa

Soyayyar Intanet: Hanyoyi takwas na kauce wa ‘yan damfara

Getting your Trinity Audio player ready...

Biyo bayan gano da bincike (investigation) kan fitaccen dan damfarar nan ta hanyar soyayya a shafin Twitter Iriodalo Obhafuoso (Odalo) wanda ke yaudarar mata su tura masa kudi saboda yana da wata cuta da ka iya halaka shi. DUBAWA ya fitar da wasu hanyoyi da za a iya gano ‘yandamfarar da kauce masu.

Damfarar Intanet (Internet fraud) na nufin duk wata dabara da za a iya amfani da email ko adireshin intanet (websites) ko wani dandali na musayar sakonni a yaudari mutum don ya tura wani sako ko a angiza mutum ya aikata zamba a wata cibiyar kudade ko dai wasu abubuwan masu alaka da hakan.

Mayaudarin kan iya samunka a kafar sadarwar zamani ko dandalin masoya ko manhajar wasanni da shafukan intanet. Ko su tura ma sakonni ko email.

Suna buya ne da yin amfani da wasu hotuna ko bayanan mutum na karya, a lokuta da dama su yi amfani da wani fitaccen mutum. Sun kware wajen iya nuna cewa kai mutum ne na musamman ta yadda za ka amince da alakar.

Da zarar ka amince da su sai cikin ‘gaggawa’ su tambaye ka ka ba su wani abu ko kudi don taimaka masu. Ko su nemi ka yi masu wani abu. Kamar samar masu da asusu ko aika masu da kudi. Mazambacin kan iya tsayawa shekaru don neman a amince da shi. A batun na Odalo ya tsaya tsawon mako guda.

Abubuwan fargaba:  Alamu da ya kamata a lura

Su kan nuna cewa suna kaunarka sai su fara abubuwa cikin sauri. A labarin na Odalo wacce ta fada tarkonsa , a lokacin da take ba da labari, ta ce sai ya fara bayani kan “batun lafiyarsa” bayan mako guda na tattaunawa ba kakkautawa.  

Mayaudarin kan iya nuna alamu, ka sakankance cewa kai mutum ne na musamman, ya nuna maka ka zama mai sirri ya tabbatar da cewa ka aminta da shi. Su kan sa ka kadaita daga iyalanka da abokai.

Za su yi ta zuwa da uzuri kan dalilan da ya sanya ba za su hadu da kai ba kai tsaye ko su nuna kansu a kamera. Za su ce ba sa kasar ko suna wajen da ba internet ko fasahar da ke inda suke ba ta aiki. Wasu lokutan abin da suka fada maka ya sha banban da abin da ke rubuce a bayanan shafinsu. Masu damfara na iya cewa ka basu wasu hotunanka na sirri ko bidiyo da za su iya amfani da su su damfare ka. Nan da nan sai su nuna maka sun yi fushi idan suka nemi abu kaki yi. Suna iya barazanar yanke alakar.

Har ila yau ‘yandamfarar ba sa son tattaunawa da abokanka ko iyalai. Muddin ka ga alama ba sa son alaka da mutanen da kake rayuwa tare da su kai tsaye to ka zama cikin taka tsan-tsan.

Wani abin lurar kuma shine idan ka ga hoton mutumin yayi kyau matuka da alamu na kwarewa wajen yin sa, alamu ne na cewa sun dauko daga rumbun ajiya na shafukan intanet ko shafukan sada zumunta na wasu fitattun ‘yankwalisa. Ka yi amfani da dabarun gano asalin hoto don tantancewa. 

Lura da banbanci na lokacin wurare, shi ma abu ne da za a iya amfani da shi don gano dandamfara. Ka lura sosai idan mutum ya ce karfe kaza yanzu ka ga kuma bai dace da lokaci ba a wajen da ya fada maka. Wannan na nuni da cewa suna magana ne a wata kasa ta daban don kaucewa gano su.

Hanyoyi da za ka kaucewa fadawa tarkon su

  1. Abu na farko da za ka yi shine ka amince da abin da zuciyar ka ta nutsu da shi, ka da ka shiga rudani za mo mai taka tsantsan wajen kulla alaka ta kafar intanet, da zarar baka gamsu ba, ja da baya ka yi duba na tsanaki kan lamarin.
  2. Tantance bayanai: Yi amfani da dabarun iya gano asalin hoto don fahimtar ko da an sato hoton ne daga shafin sadarwar intanet na wani mutum ne. 
  3. A guji yada bayanan kai: Kaucewa yada wasu bayanai na sirri  kamar adireshi na gida da lambar waya ko wasu bayanan banki  ga mutumin da kawai ta intanet kuka hadu, duk yadda ka kai da amincewa da shi kuwa. Babu batu na ba da hotuna ko wasu hotuna na sirri. Ka da ka dauki hoto na nuna fuskarka. 
  4. Yi taka tsan-tsan da labaran ban tausayi: ‘yan damfara sun kware wajen kirkirar labarai na ban tausayi ta yadda za su yaudari wanda ya fada komar su saboda tausayi. Ka kula sosai idan mutum da kake magana da shi ya fiya nuna cewa ya fuskanci wata jarrabawa ko kawai ya ce yana da wata bukata ta gaggawa kan sha’anin lafiya.
  5. Kar ka taba tura kudi: Ko wane irin dalili ya fada kuwa, kar ka tura kudi ko wani taimakon kudi ga mutumin da ka hadu da shi ta intanet. Masoya na hakika basa rokon kudi, musamman idan baku taba haduwa ba, ka yi tambaya kan duk abin da baka gamsu da shi ba. 
  6. Ka yi tambaya: Ka bukaci hotuna ko wasu karin shedu kan wani labari da aka fada maka, ga misali a labarin na Odalo da wacce ta fada tarkonsa ta nemi hotonsa a asibiti, ta nem kai masa ziyara da zarar ya fara dagiya anan za ta gane akwai shirin zamba anan.
  7. Tattauna da abokai da iyalai: Tattauna da iyalai da abokai kan wata sabuwar alaka da ka kulla ta kafar intanet. Za su iya taimaka maka muddin suka gano wasu alamu na mazambata da kai baka gano ba.
  8. Dora ayar tambaya kan hotuna da bidiyo: A wannan zamani da ya cika da hotunan karya ka tabbatar da ka tantance hotuna da bidiyo da ka gani. Ana iya yi masu siddabaru don kawar da hankalin masu kallo. 

Ka da ka yi gaggawa.  Mazambata suna so ayi komai cikin gaggawa. Ka dauki lokaci ka yi tunani kafin yanke shawarar kulla alakar kudi ko wata alaka da mutum ta kafar intanet. Soyayyar gaskiya kan dauki lokaci, ta kan kullu idan akwai aminta da mutuntawa. Ka zama mai sa idanu kada ka bari shauki ya rika dibarka, idan za ka yanke hukunci kan alaka da mutane ta kafar intanet musamman a kafafen sada zumunta irin na Twitter.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button