Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: “Matar Nwabali”ta bayyana maigidanta a wani hoto da yayi fice.
Hukunci: Yaudara ce. An dauko hoton ne daga shafin Instagram na danwasan kwallan kafar aka yi masa wata kwaskwarima aka baza shi don nishadantarwa.
Cikakken bayani
Bayan da aka bayyana Stanley Nwabali a matsayin dan wasan da yafi iya murza leda a wasa wato “Man of the Match” matsayin da aka ba wa mai tsaron gidan na Super Eagle bayan wasan kusa da na karshe da suka buga wanda ya ba su nasarar zuwa wasan karshe a wasan zakarun nahiyar Afurka da aka buga a baya-bayan nan na (AFCON), masoya sun rika furta kalamai na jinjina ga danwasan ana tsaka da haka ne, sai aka ga bayyanar wasu hotuna guda uku na wata mata tare da Mista Nwabali inda aka bayyana matar a matsayin mai dakinsa, hotunan da suka bazu a shafin Facebook.
Da fari an yada (shared) hotunan a shafin Amanda Chisom inda aka makala masa taken “Goodnight from first and only wife, Mrs Chisom Okolo-Nwabal.” wanda ke zama gaisuwar bankwana daga uwargida kuma mata guda wato Mrs Chisom Okolo-Nwabal. Tun daga ganin wannan wallafa a ka rika yada hotunan ana bashi take daban-daban.
Misali matar Stanley Nwabali’ ta bayyana mijinta. Wani kuma na cewa ka da a tsallaka mata iyaka “Chisom matar danwasan Super Eagles ta bayyana mijinta tare da shata iyaka.
Ganin yadda wannan hoto ya karade shafukan sada zumunta, yayin da wasu ke nuna shakku wasu kuma na cewa babu shakka haka ne abin da aka gani a hotunan ( photographs,) da dama sun karbi hotunan a matsayin na gaskiya. Ganin kimar wanda aka alakanta a hoton, dama yadda hoton ke yaduwa a shafukan sada zumunta yasa DUBAWA ya bincika.
Tantancewa
Da kallon fari wani na iya amincewa cewa danwasan kwallon kafar ya dauki hoton ne da matar, sai dai idan aka yi wa hotunan kallo na tsanaki da kallon Mista Nwaballi zai fahimci babu wata alama ta cewa hoton na miji da mata ne, kazalika dukkanin hotunan uku babu wanda ya nuna cewa miji da mata ne a hoton, baya ga yadda fuskarsa ba ta nuna wata alama ta soyayya ba ga kuma hannayensa a aljihu duk kuma da cewa sun tsaya kusa da juna, babu wata alama da ta nuna daya ya raba jikinsa da danuwansa a hoton.
Wasu daga cikin hotunan da suka yadu a soshiyal mediya.
Mun duba shafin Instagram na Mista Nwabali ko da za mu iya gano hoton da wannan mata da a ke cewa “uwar gidansa ce” anan ne muka gano asalin hoton wanda shi kadai (ne a jiki. Ya wallafa hoton na farko (first image,) da yake dauke da jaka hannunsa guda a aljihu, a ranar biyu ga watan Janairu, 2023, wanda ke nufin sama da shekara guda kenan.
Haka kuma ya wallafa hoto na biyu a ranar daya ga watan Janairu, 2024, hoton da ya dora hanunsa daya a kan daya, ya rubuta “barka da sabuwar shekara 2024” Ya kuma wallafa hoto na uku third image a gefen wata farar mota a ranar daya ga watan Yuli, 2023.
Da kuma muka duba wasu hotunan da aka wallafa a shafin na (Amanda Chisom’s blog ) mun gano hotuna da dama na dankwallon mai tsaron ragar Super Eagles , inda ake zargin ya tsaya daukar hoto da wasu mata da dama kamar anan (here, here, here, da here.) wasu na nuna yadda suke son sa wasu kuma na nuna cewa shi masoyinsu ne.
Shi dai Nwabali ya fito ne daga wasu iyalai mabiya addinin Kirista ya fara buga kwallo a Kulob din Go Round FC a matsayin dan wasan gaba, daga nan ya tafi Kulob din Enyimba da Lobi Stars da Katsina United da Chippa inda anan ne kawo yanzu yake taka leda. Babu wata kafa ta intanet ko shi da kansa da ya bayyana cewa yana da aure ko ba shi da shi,
A karshe
Binciken da muka gabatar mun gano cewa an dauki tsofaffin hotuna ne na danwasan aka yada su don kawai sharholiya. Da’awar da aka yi yaudara ce.