Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wata kafa mai suna CareerNG a shafin Facebook ta yi da’awar cewa Julius Berger na daukar ma’aikata.
Hukunci: Karya ce! Yadda takardar neman daukar ma’aikatan da ta fito daga kamfanin BUA Group ta nunar, na dauke ne da wani link da zai sadar da mutum zuwa wani shafi na neman visa wanda ba shi da wata alaka da Julius Berger ko BUA.
Cikakken bayani
Daukar aiki ta kafar intanet ya zamo sanannen abu, sai dai kamar sauran abubuwa da ake yi a kafar, neman aiki na tattare da wasu tarin kalubale sai mutum yayi taka tsantsan.
Kafar CareerNG a shafin Facebook ta wallafa wani bayani (posted) inda take nuna cewa Kamfanin BUA na daukar aiki. Har ma yana cewa “Wannan ita ce dama a gareka kayi aiki tare da kamfanin Julius Berger, ana tattara takardun wadanda za a dauka aiki. Ka turo naka yanzu..” Wannan wallafa ta samu wadanda suka nuna sha’awarsu (Likes) 9,500 da masu tsokaci (Comments) 1,000 da wadanda suka sake yadawa (shares) 158 tun bayan da aka ba da wannan rahoto a ranar 13 ga watan Fabrairu 2024.
Mun lura da irin karbuwa da wannan sako ya samu kuma wadanda suke tsokaci sun karkata da amincewa da sakon, ga kuma a zahiri banbanci tsakanin rubutaccen sakon da sanarwar da ke makale hakan ne ma ya sanya muka shiga aikin bincike don gano gaskiyar labarin.
Tantancewa
Mun lura cewa ko da yake ance wadanda za su dauka aikin Julius Berger ne takardar sanarwar kuma ta nunar da cewa kamfanin BUA Group ne. Da muka latsa ( link) sai ya kai mu ga “Damarmakin samun aiki a Canada da daukar nauyin visa na 2024,”wanda baki daya ba shi da wata alaka da batun na daukar aiki.
Mun duba don gano sahihancin wallafar ta hanyar amfani da (Scam Adviser) wanda ya nunar da cewa akwai alamar tambaya kan link din.
A cewar Scam Adviser “Wannan shafi babu alamun gaskiya a tattare da shi, shafi ne da ke iya bacewa a ko da yaushe, zai iya kai ka ga wasu shafuka da ba su kai niyar ziyarta ba, duk wasu bayanai da ka sanya a shafin kana cikin fargaba.”
Da muka ziyarci shafin BUA (website ) muka kalli hoton da aka wallafa a shafin da ke cewa kamfanin na BUA na daukar aiki sai muka ga cewa kamfanin a shafinsa na intanet ya tallata wasu kujeru ne kawai da za a iya nema ga masu son aiki a kamfanin. Mun kuma leka shafin kamfanin Julius Berger (website) ko za mu ga yana neman ma’aikata anan ma sai muka lura cewa a shafin a kwai wani gurbi da aka nuna guraben aiki amma idan ka latsa babu inda zai kaika.
Don samun bayanai kan yadda ake neman aikin a shafin na intanet da samun kariya ta bayanai da ake sakawa sai mutum ya nemi fejin kamfani nagartacce.
A Karshe
Bayanan da aka sanya a wallafar da sanarwar neman aikin ba su dace da juna ba, sannan link da zai kai ka ga bayanan da kake nema ba na gaske ba ne, Har ila yau babu wata sheda da ta nuna cewa kamfanin na Julius Berger na daukar aiki.