African LanguagesHausa

Tsoffin hotuna ne aka yi amfani da su a sunan sabon harin da aka kai wata al’umma a jihar Neja

Da’awa: Wasu shafukan sada zumunta sun yi amfani da wani hoto wajen kwatanta harin da aka kai al’ummar Madaka da ke jihar Neja.

Hukunci: Hoton da aka yi amfani da shi wajen kwatanta harin da aka kai kwanan nan a kan al’ummar Madaka da ke jihar Neja ba shi da alaka da harin. Wannan bayanin yaudara ce kawai.

Cikakken bayani

Ranar 21 ga watan Maris 2024, abun takaici ya faru a al’ummar Madaka wadda ke karamar hukumar Rafi a jihar Neja. Kamar yadda rahotannin suka bayyana dangane da harin da ‘yan bindiga suka kai wata ‘yar kasuwar da ke kauyen. Wannan harin ya kai ga hallakar wani adadi mai yawa na ‘yan kasuwa da kwastamomin da ba’a bayyana ba.

Bayan wannan harin ne wani hoto ya bayyana ya fara yawo a kafofin sadarwa na soshiyal mediya da zargin cewa abin da ke cikin hoton yanayin da ya kasance ke nan a kauyen bayan da aka kai wannan mummuman harin, har ma da zargin da ke cewa sama da mutane 30 suka hallaka. Hoton ya kuma gwado wasu gawawwakin da aka nade cikin likafani ana kokarin shirin yi musu sujada kafin a bizine su.

Wani mai amfani da shafin X I.G Kagara, wanda ya wallafa hotonya ce ana shirya gawawwakin ne dan a rufe su duka a tare a wani wuri da ke daga wajen al’ummar.

Ibrahim Kagara, wani shi ma mai amfani da shafin wanda shi ma ya wallafa wani hoto makamancin wannan, ya bayyana takaicinsa dangane da wannan jarin inda ya sanar cewa an ma rufe wadanda suka riga mu gidan gaskiyar bisa tanadin addinin musulunci.

Mutane kusan 3,000 suka kalli hotunan an kuma sake wallafa su sau 47, tare da tsokace-tsokace da ke bayyana takaici, makoki da addu’o’in Allah ubangiji ya sa sun hutawa. DUBAWA ta gudanar da bincike dan tantance gaskiyar wannan batun.

Tantancewa

Ta yin amfani da manhajar tantance hotuna, DUBAWA ta gano cewa an yi amfani da wannan hoton da ke yawo sau da yawa a shafin Facebook tun shekarar 2021. Bacin haka, 

Labarin da aka sa a shafinFACEBOOK Kwanan WataMAJIYABayanin da aka yi tare da hoton
Labari 1Maris 16, 2022Nafisa LabarinaWadannan gawawwaki ne na mutane 42 wadanda ba su ji ba su gani ba, ‘yan bindiga suka kashe su da harbin bindiga a karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina.
Labari 2Maris 16, 2022Ummi RahabWadannan gawawwaki ne na mutane 42 wadanda ba su ji ba su gani ba, ‘yan bindiga suka kashe su da harbin bindiga a karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina. Bari ubangiji ya jikansu da rahama, Amin, mu kuma idan lokacinmu ya yi Allah sa mu cika da imani. Amin. 
Labari 3Yuli 28, 2022Zuwaira JuwairiyaWadannan gawawwaki ne na mutane 42 wadanda ba su ji ba su gani ba, ‘yan bindiga suka kashe su da harbin bindiga a karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina. Bari ubangiji ya jikansu da rahama, Amin, mu kuma idan lokacinmu ya yi Allah sa mu cika da imani. Amin. Ka da ku manta ku raba da kungiyoyi akalla biyar dan a yi ‘yan uwanmu musulmi addu’a.
Labari 4Yuni 12, 2021Yusuf Ridwan Mai FataAllah ya ba mu zaman lafiya a Zamfara, Allah ya kawo mana zaman lafiya a Zamfara.
Jaddawalin shafuka da labaran da aka wallafa da hoton tun shekarar 2022

Baya ga wadannan wadanda aka wallafa a shafin Facebook, Cibiyar Bincike Mai Zurfi na Kasa da kasa a aikin Jarida (ICIR) ita ma ta wallafa wannan hoton a shafinta da taken cewa “‘yan sanda sun karyata zargin cewa mutane 60 sun hallaka a harin zamfara, sun ce ‘30 kadai’ suka hallaka.”

Wannan rahoton ya fito ne ranar 12 ga watan Yunin 2021, ya kuma yi bayani dalla-dalla kan yadda aka kashe mutane 60 a karamar hukumar Zurmi da ke jihar. Wannan kan shi ya nuna cewa hoton ba shi da wata alaka da abun da ya faru a jihar Neja.

A karshe

Hoton da aka yi amfani da shi wajen kwatanta kisar da aka yi a al’ummar Madaka a jihar Neja yaudara ce. Tsoho ne kuma ba shi da wata alaka da abun da ya faru a jihar Neja.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button