|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin X ya yada bidiyo da ya nuna mutane na kauracewa muhallansu bayan farmakin Fulani masu ta’addanci inda suke ba wa Hausawa mazauna umarni su fice daga Sokoto ko kuma a halaka su.

Hukunci: Yaudara ce. Bincike da DUBAWA ta gudanar ya nuna cewa an wallafa wannan bidiyo tun a watan Mayu,2025 inda aka nuna al’umma na kauracewa muhallinsu saboda fargabar kai hari daga magoya bayan danta’addar nan Bello Turji
Cikakken Labari
A ranar 13 ga watan Yuni,2026 wani mai amfani da shafin X Drake (@DrakeOfficial06), ya yada wani bidiyo wanda ya nuna dandazo na mutane maza da mata dauke da kayayyaki a kansu suna tafe a kan hanya wacce ke zama mai yawan kura.
Drake yayi da’awar cewa wannan dandazo wasu a;l’umma ne Hausawa wadanda ke kokarin barin muhallisu bayan umarni da wasu ‘yanta’adda suka bayar cewa Hausawa mazauna Sokoto a yankin su fice daga garin.
Ga ma abin da taken labarin ke cewa “A arewacin Najeriya Fulani ‘yanta’adda sun fadawa kabilar Hausawa su fice daga Sokoto ko kuma su fuskanci yankan rago. Kalle su suna kauracewa muhallinsu dalilin Fulani masu ta’addanci.”
Wannan wallafar kamar yadda aka ajiye ta nan ya zuwa ranar 13 ga watan Yuni, ta samu wadanda suka kalla 124,000 da masu tsokaci 215 dawadanda suka sahe yadawa 1,400 da masu nuna sha’awa 2,100.
Akwai masu tsokaci mabanbanta wanda abin da suke fadi na da alaka da kabilanci, yayin da sauran kuma ke nuna takaici kan yadda gwamnati ta gaza warware matsalar.
“Kana nufin Hausawa su fice su bar Sokoto a hannun Fulani? A bar Sokoto don kawai Fulani da Sarkin Musulmi (saboda sarkin Musilmi ma Fulani ne)?”
Wannan shine ra’ayin @MaguuThegreat wanda yayi tambaya,
@Real White Aghama (@AghamaW) ya ayyana cewa “Fulani ‘yanta’’ada da sunan Islama tare da masu ba su dama da masu daukar nauyinsu su ke kawo nakasu ga zaman lafiyarmu da ci gaban ‘yanNajeriya da kasar a halin yanzu,” wannan tsokaci ya samu martani 732.
@Onlineband_it ya ci gaba da rubutu, yana mai cewa ‘Ya kamata mu bayyana diukkanin Fulaniu a matsayin ‘yanta’adda.”
Da yake alakanta abun da gazawar gwamnati, @Obaskki ya rubuta cewa ta yaya ne mutum zai bar muhallinsa saboda ‘yanta’adda sun masa kutse? Gaskiya babu makawa gwamnati ta gaza.”
@SleemMedia yayi tambaya, ne da cewa “Gwamnati bata yin komai? Wa muka yi wa laifi haka?”
Ganin yadda wannan wallafa ta kai ga mutane da dama ga kuma hadarin da ke tattare da ita na harzuwa al’umma a Najeriya. DUBAWA ta ga dacewar gudanar da binciken gano gaskiya a game da bidiyo da ma rubutun da aka yi akai.
Tantancewa
Mun bincikin asalin bidiyon don gano asalin daga inda ya bulla,
Na farko ya bayyana a ranar 4 ga watan Mayu,2025 inda aka yada shi a shafin Instagram @northern_trending_ da yada irin wannan bidiyo da aka yi wa taken kauracewa muhalli sakamakon fargabar kai harin ta’addanci daga mabiya dan’addar nan Bello Turji bisa jagorancin wani shima Kallamu, wannan ya sanya mazauna yankin kauracewa muhallinsu na garin Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni.
Fassarar abinda yake cewa ta nuna cewa “mazauna kauyuka sama da 20 suna kauracewa muhallansu saboda barazanar harin ta’addanci da Kallamu yayi wani na kusa da babban danta’addar nan Bello Turji, Wadanda suka bar muhallansu sun isa Gatawa suna neman mafaka.”
Bayan kuma kwanaki biyu a ranar 6 ga watan Mayu,2025 sai ga wani shafin Facebook mai suna “Hausawa” ya yada irin wannan bidiyo shi kuma ya ba shi wani taken na daban da cewa “Halin da akre ciki yanzu haka a Sokoto da ke zama inda Sarkin Musulmi yake.”
Wannan wallafar ta tabbatar da cewa wannan wallafa ta ci gaba da yaduwa tun a watan na Mayu,2025 kuma ana alakanta ta da jagoran ta’addancin nan Turji.
Yin kaurar da aka nuna a bidiyo ta yi daidai da rahotanni da ake yadawa a kafafan yada labarai a Najeriya a farkon watan Mayu,2025. Jaridar Punch ta ba da rahoto a ranar 5 ga watan Mayu,2025 cewa hare-haren da magoya bayan danta’addar nan Bello Turji ke kaiwa ya sanya mutane kauyika kimanin 20 kauracewa muhallansu a kauyikan jihar Sokoto. A cewar jaridar ta Punch mutanen kauyikan da suka baro muhallansu sun nemi mafaka ne akaramar hukumar Sabon Birni.
Wani bincike kan yadda aka samu mutanen sun yi kaura zuwa Sabon Birni ya tabbatar da cewa harin na Bello Turji a watan Mayu,2025 ya sanya mutane da dama kauracewa muhallansu a lardin Gatawa.
Mahukunta a yankin sun tabbatar da lamarin a wannan lokaci sai dai bayanansu bai kebe wata kabila ba. Rahoton na jaridar The Punch ya tabbatar da cewa an kai da jibge dakarun tsaro a wannan yanki da ke cikin yanayi na tashin hankali.
Mun kuma yi bincike don ji ko akwai wani sako daga mahukunta a gwamnatin Sokoto da jami’an ‘yansanda da sojoji ko wasu jami’an tsaron a dangane da da’awar mutumin da ke zama barazana a baya-bayan nan amma babu abin da aka samu.
A Karshe
Dauk da cewa akwai bidiyon da @DrakeOfficial06 ya fitar wanda na gaske ne,
Anma ba kwananan nan aka yi shi ba ko wata barazana ga Hausawa da ke zaune a Sokoto. Shi wannan bidiyo an yi shi tun a 2025 lokacin da wasu mutane ke barin garinsu a jihar Sokoto.
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.
