African LanguagesHausa

Tura sako zuwa 8014 ba ya aiki; Ga yadda za ku gano runfar zabenku ta intanet

Zargi: Domin gano runfar zaben da mutun zai je ya jefa kuri’arsa, ku tura lambobi taran da ke kan katin zabenku (PVC) zuwa 8014

<strong>Tura sako zuwa 8014 ba ya aiki; Ga yadda za ku gano runfar zabenku ta intanet</strong>

Bincikenmu da bayanan da mu ka samu daga INEC sun nuna mana cewa wannan lambar ba ta da dangantaka da INEC kuma ba ta taimakawa wajen gane rumfunan zabe.

Cikakken bayani

Har yanzu jama’a na zuwa karbar katunan zabensu gabanin kuri’ar da za’a yi na zaben sabbin shugabani ranar 25 ga watan Fabrairu.

Bisa la’akari da haka ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta sake bude sabbin wuraren karbar katunan zaben a birnin tarayya Abuja saboda a hanzarta raba katunan tunda lokaci ya kusa.

Sai dai yayin da ake karbar katunan, wanda ake sa ran wa’adin yin hakan zai cika ranar 25 ga watan Janairu, wani sakon WhatsApp ya yi bayanin cewa idan har mutun ya tura lambobi taran da ke kan katin zabensa zuwa wata lamba, wato 8014 zai sami sako da adireshin inda ya kamata ya je ya jefa kuri’arsa.

Sakon wanda ke da burin baiwa jama’a karfin gwiwar zuwa su yi zabe ya kuma yi gargadin cewa rashin sanin rumfar zabe bai kamata ya kasance dalilin da mutun ba zai je ya jefa kuri’arsa ba.

“Batun “ban san rumfar zabe na ba” ba zai kasance dalilin rashin yin zabe ba. Tura sako da lambobin taran da ke kan katin zabe tuwa ga lambar waya 8014, nan da nan za’a turo adireshin runmfar zaben da ya kamata ku jefa kuri’ar ku, “ a cewar sakon.

Yayin da zaben ke matsowa kusa, wadanda suka cancanci kada kuri’a na gaggawar samun bayanan da suka danganci ‘yancin su ta yadda zai taimaka mu su wajen yanke shawara, shi ya sa muka dauki nauyin tantance gaskiyar wannan batun.

Tantnacewa

Rumfar zabe ko kuma Polling Unit (PU) kamar yadda aka san shi da turanci wurin da duk wanda ya cancanci kada kuri’a ya kan je ya yi rajista dan ya yi zabe. Dan gano wadannan wuraren akwai wata manhajar da aka yi tanadi, wadda ke bayyana duk wuraren da aka kebe a matsayin rumfunan zabe. Da zarar ka rubuta sunan Jihar, Karamar Hukuma ko Unguwa, sunayen rumfunan za su fito sai ka zabi naka.

Ba INEC ce ta bayar da wannan lambar ta 8014 ba

Mun tuntubi Kwamishinan Yada Labarai da Illimantar da masu zabe, Festus Okoye wanda ya bayyana mana cewa ba hukumar ba ce ta fitar da wadannan lambobi domin hukumar ba ta taba fitar da lambobi irin wadannan ba.

“Ba mu fitar da wannan ba,” Mr Okoye ya fadawa daya daga cikin masu binciken mu.

Babban sakataren shugaban hukumar INEC Rotimi Oyekanmi, yayin da shi ma ya ke amsa tambayar mu ya wallafa wani sako a shafin tiwita daga shafin INEC wanda ke bayani dalla-dalla kan yadda za’a iya gano rumfunan zabe.

“Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta sake sassauta matakan karbar katin zabe a matakin unguwanni. Duk wadanda su ka riga su ka yi rajista suna iya tura sako zuwa kowanne daga cikin lambobin da aka bayar dan gano wuraren da ya kamata su je su anshi na su.

Lambobin sun hada da 0906-283-0860 da 0906-283-0861. Duk wanda ke bukatar sani zai tura sunar jiha, karamar hukuma da unguwa, zuwa wadannan lambobin.

Mene ne wadannan lambobi kuma yaya su ke aiki? 

Mai bincikenmu ta bi duk umurnin da aka bayar a cikin sakon da ya bukaci da a tura lambobi taran da ke kan katin zabe zuwa 8014 sai dai amsar da ta samu ba shi da wani dangantaka da rumfunan zabe.

Daga baya kuma sai ta sami wani sako daga wata lambar ta daban (9001) wanda ke magana dangane da wani sabis na waya da ta ke bukata, wanda kuma ake cazar Nera 50. Sakon ya kuma kara da cewa ana iya nuna amincewa da latsa lamba 1 ko kuma lamba 2 dan nuna rashin amincewa.

Bayan da ta amince, sai aka turo sakon taya murna mai cewa an sami sakonta kuma nan ba da dadewa ba za’a turo mata sakon tabbatar da hakan.

Sa’o’i 24 bayan nan ba ta sami sakon tabbacin ba. Duk da cewa ba za mu iya sanin sabis din da lambar ke bayarwa ba, mun dai tantance cewa ba ta da wata alaka da rumfar zabe ko ma katin zabe.

A Karshe

Bincikenmu da bayanan da mu ka samu daga INEC sun nuna mana cewa wannan lambar ba ta da dangantaka da INEC kuma ba ta taimakawa wajen gane rumfunan zabe.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button