Zargi: Bawon da ke bayan bishiyar Kashu na rage lahanin dafin maciji.

Sakamakon Bincike: BABU CIKAKKIYAR GASKIYA. Bincikenmu ya nuna mana cewa babu wata hujja ta kimiya da ke nuna cewa bayan bishiyar kashu na da wani tasiri kan dafin maciji.
Cikakken bayani
Bishiyar kashu na da mahimmanci sosai kuma ana yawan amfani da shi a yankunan da ke samun ruwan sama wadanda ke da gandun daji. Bishiyar ta yi mafari daga kasar Brazil ne amma kuma yanzu ana samun ta a kasashen duniya da yawa wadanda suka hada da Najeriya, Vietnam, Indiya, Indonesiya, Philippines, Benin, Guinea Bissau da Cóte d’Ivoire.
Yayin da ‘ya’yan itacen da ake samu a jikin bishiyar sanannu ne, bayan itacen shi ma yana da mahimmanci musamman ga kiwon lafiya
An dade ana amfani da bayan bishiyar Kashu a matsayin maganin gargajiya dan kashe kwayoyin cuta da rage kumburi da kuma rage zafin ciwo. Yana dauke da wadansu sinadaran da aka tabbatar suna iya kashe kwayoyin cuta musamman irin na bakteriya.
Kwanan nan wani sakon WhastApp da ce yawo ya yi zargin cewa idan har aka tauna bayan kashu ana iya warkar da ciwon da aka samu daga dafin cizon maciji. “Zai cire dafin da ake cikin cizon.” sakon ya ce.
Wannan zargin ba sabo ba ne, kuma ko a watan Satumban 2022 an yi yawo da sakon kuma a yanzu man gano shi ne a shafin Facebok inda wasu mutane suka wallafa. Mutanen sun hada da Balarabe Yazid, Ibrahim Danjuma Babeji, da Imajijio Ufuamaka.
An dade ana cewa bayan bishiyar cashew na iya warkar da cizon maciji kuma da yawa na ganin ana iya amfani da shi waje rage kaifin dafin maciji.
Alal misali, Haruna Abdullahi ya yi tsokaci a batun da Danjuma Babeji’s ya wallafa, ya na cewa batun ya wayar masa da kai sosai dan ya samu bayanai masu illimantarwa.
“Bayani mai illimantarwa kuma mai amfanu. Bari Allah Azza Wajalla ya albarkace ka,” ya rubuta.
A wani bayanin a shafin Uju Mmiri, Udu Ego ya bayyana gamsuear da ya yi da bayanin. “Daalu Nneoma saboda koyarwar da ka yi mana,” Mr Ego ya ce.
Wannan batun na iya janyo rudani da ma matsalar da ka iya kasancewa da hadarin gaske, shi ya sa yake da mahimmanci a tantance gaskiyae lamarin.
Tantancewa
Mu fara da lura da karin bayanan da aka wallafa tare da zargin, wanda bukata ce aka yi mai cewa a sake raba batun da wadanda ke shafukan soshiyal mediya, abun da ya nuna dalilin da ya sa sakon ya shiga ko’ina a WhatsApp.
Bishsiyar Kashu ta na girma ne a wuraren da ke da yawan ruwan sama kuma koriya ce. Sunarta ta kimiya ita ce Anacardium occidentale. Bayan itacen wanda ke da launin ruwan kasa da na toka, bayan na da kaushi sosai kuma yana dauke da sinadarin tannis wanda ake yawan amfani da shi a magungunan gargajiya.
Bayan ko kuma bawon bishiyar na dauke da sinadarai da dama wadanda suka hada da anacardic acid and cardol, wadanda aka san su saboda yadda za su iya kashe kwayoyin cuta da yadda za su iya rage kumburi.
Maganin dafi, magani ne da ake amfani da shi wajen rage kaifi da kuma illar dafin maciji a jikin dan adam bayan maciji mai dafe ya cije shi. A kan same shi ne bayan an sanya dafin dan kankani a jikin wata dabba, wata sa’a doki ko rago, sai a cire sinadarai ko kuma kwayoyin jikin daban wadanda suka bayyana a jikinta dan yin yaki da lahanin da dafin macijin ka iya janyowa. Wadannan sinadarai yawanci su ne irin garkuwar da jikin ke bukata wajen yaki da nau’in dafin macijin da aka sanya a jikinsu
Magungunan dafin sun danganci irin dafin da ake so a kashe kuma yin amfani da magungunan da ba’a riga an tabbatar da ingancin su ba, musamman wajen rage kaifin dafin na iya kai wa ga hallaka.
Wani binciken da aka yi kan beraye a karkashin jagorancin sashen illimin magunguna a jami’ar Mysore da ke Indiya, sun gano cewa ana iya amfani da bayan kashu din wajen tsayar da jini, kumburi da ma ciwon da aka ji a wajen da macijin ya kai cizo. Sai dai dafin na nan da kaifin shi sai dai ya dan dauki lokaci kafin berayen su mutu daga dafin macijin. Masu binciken sun kammala da cewa ana iya amfani da shi a matsayin irin magungunan da za’a iya bayarwa a matakin farko bayan an sami cizo daga wadansu nau’o’in macizai.
Bisa bayanan wadansu shawarwarin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) dangane da kula da wanda ya sami cizon maciji, “Yawancin magungunan gargajiya ba su da amfani kuma suna da hadari.” WHO na gargadin mutane dangane da amfani da magungunan gargajiya.
Ra’ayin kwararru
Wani likitan dabbobi, Eric Kuju, ya fadawa DUBAWA cewa yayin da aka san cewa bayan bishiyar kashu din na dauke da irin sinadaran da ke taimakawa wajen magance wadansu abubuwa, babu wani bincike ko hujar da ta nuna cewa an taba amfani da ita a dafin maciji kuma ta yi aiki yadda ya kamata.
Ya tsokaci dangane da binciken da aka yi da beraye, “ya ce binciken da sashen ilimin magunguna a jami’ar Mysore da ke Indiya ya yi a kan beraye kadai aka gwada. Binciken bai je kan dabbobin da ke da siffofi irin na dan adam kamar biri ba bare mutum.”
Ya kara da cewa, “Idan har an matsa, wata kila bayan bishiyar kashu din na iya jinkirta lahanin da dafin zai yi a jikin dan adam amma ba zai hana dafin kissa ba.”
Wata mai hada magunguna, Rachel Vincent ta fadawa DUBAWA cewa babu wani bayani dangane da irin sinadaran da yake dauke da shi wadanda za’a iya amfani da su wajen kawar da illolin dafin maciji. “Ban taba jin cewa akwai wani abu kamar haka ba,” ta ce.
Mun kuma gano wadansu shafukan wadanda su ma suka karyata wannan zargin. Shafukan sun hada da Africa Check, The Healthy Indian Project, da AFP fact-check.
A karshe
Yayin da gaskiya ne bayan bishiyar kashu na da wadansu sinadaran da ake iya amfani da su kan cututtuka, ba shi da wani tasiri kan dafin maciji. Bacin haka babu wata hujja daga binciken kimiya da ke nuna cewa bayan bishiyar na iya kawar da dafin maciji, kuma ma hukumomin da ke halata amfani da magunguna ba su bayar da izinin amfani da shi a kan dafin maciji ba.