African LanguagesHausa

Cin abinci mai lafiya da motsa jiki na iya rage hawan jini

Zargi: Wani mai amfani da shafin Facebook na zargin wai yawan motsa jiki da rage yawan gishiri da maggi a abinci ba zai rage hawan jini ba

Sakamakon bincike: Karya. A cewar kwararu a kiwon lafiya, idan har mutun yana cin irin abincin da ya dace yana iya rage hadarin da ke tattare da hawan jini.

Cikakken bayani

Hawan jini yana faruwa ne sadda karfin gudanar jini ya karu ta yadda ya ke sanya matsin lamba a kan bangon jijiyoyin da ke daukar jini ya kuma wuce adadin da ake bukata.

Bisa bayanan Cibiyar Kula da Cututtuka (CDC) hawan jinin mutun kan canja sau da yawa a rana guda saboda ya danganci abubuwan da mutun ke yi.

Ana kiyasin cewa mutane biliyan 1.28 wadanda ke zaman magidanta masu shekaru tsakanin 30 da 79 a duniya baki daya ke dauke da cutar hawan jini; kusan kashi biyu cikin uku na wannan adadin kuma na rayuwa ne a kasahe masu mafi karanci da matsakaicin albashi.

Kwanan nan wani shafi a Facebook mai suna My Health Expert, ya wallafa wani labarin da ke cewa ko da an rage cin gishiri, da maggi an kuma fara zuwa motsa jiki sosai, ba za’a iya rage hawan jini ba.

Labarin wanda aka wallafa da wani adireshi tare da bidiyon da ke da tsawon minti guda da dakiku 14 mai bayanin yadda wata mata ta daina cin gishiri da maggi da sauran wadansu kayayyaki amma duk da haka cutar hawan jinin na ta ba ta sauya zane ba.

Mai maganar ta bayyana yadda ta rika shan wadansu hade-haden gargajiya wadanda su ma ba su ba ta irin suayin da ta ke si ba sai da ta sami wani magani na musamman wanda ya warkar da cutar na ta.

Daga ranar 5 ga watan Maris 2023 kusan mutane 285 sun latsa alamar amincewa da labarin na like, mutane 165,000 sun kalla kuma akwai bayanai kusan 31 a karkashin labarin.

Yanayin yadda mutane suka rika mu’amala da labarin ne ya sa muke so mu tantance gaskiyar wannan batun domin rashin fahimtar gaskiyar lamarin na iya sanya rayuwar mutane cikin hadari.

Tantancewa

Mun fara da bin adireshin da aka hada da labarin na Facebook wanda ya kai mu ga bayanin wani mai suna “Bishop” wanda ya dauki maganin da aka ambata kuma bayan kwanaki shida, hawan jininsa ya sauka.

Mai binciken ta lura cewa hoton mutumin da aka yi amfani da shi yana bayar da shaida, hoton wani sanannen malamin addini ne mai suna Hezekiah Oladeji, babban mai wa’azi a cocin da ake kira CAC, ba wani mai suna Injiniya Ade Smith kamar yadda aka bayana a labarin ba.

Daga nan sai masu binciken suka tuntubi dan malamin addinin wanda bai so a bayyana sunarsa ba, domin ya tantance mana wanda ke cikin hoton. Ya tabbatar mana cewa mahaifinsa ne amma sunan da aka  sa ba nasa ba ne. Daga nan ya gargadi jama’a da su guji fadawa tarkon mazambata da masu yaudara su kuma kai karar shafin.

Ra’ayin kwararru

Mun tuntubi wani likita a Rufina Catholic Center da ke jihar Ogun, Dr. Opeyemi Amosu wanda ya bayyana mana cewa babu maganin da ke warkar da hawan jini.

Ya ce, “ har yanzu ana binciken gano maganin da zai warkar da cutar.”

Ya cigaba da cewa hawan jinin da za’a iya gyarawa, abun da ke nufin ana iya ragewa ko a kara kamar kwayoyin halitta. Wadanda ba za’a iya gyarawa ba kuma ana iya kula da su ta yadda ba zasu wuce mizanin da ake bukata ba. Misali na mutanen da ka iya samun wannan nau’in shi ne mutanen da ke shan taba da wadanda ke da maikon da ake kira cholesterol da yawa. Shi dama cholesterol maiko ne da ke cikin kwayoyin jikin mutun wanda ke taimakawa wajen sarrafa wasu sinadaran da jiki ke bukata. Jiki na sarrafa iyakacin maikon cholesterol din da ya ke bukata dan haka ba’a so ya yi yawa a jiki.

“Ana iya lura da hawan jini ta yin amfani da magani, rage cin gishiri da motsa jiki. Ka da ku bari wani ya yaudare ku dangane da maganin da ke warkar da cutar. Kula da ita kawai ake iya yi da zarar mutun ya kamu da ita,” ya kara da cewa.

Wata kwararriyar a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya ko kuma Federal Medical Centre da ke Jabi, Tessy Ahmadu, ta ce hawan jini kan zo da shekaru ne wata sa’a, wasu lokuta kuma gado ne sa’anan wata sa’a ya kan zo idan mace na da juna biyu. 

Ta kuma bayyana cewa “Yayin da muke kara girma, jijiyoyin jininmu kan rage karfi. Ba’a iya maganin hawan jini baki daya sai dai a kula da shi ta hanyar cin abinci mai kyau da kuma motsa jiki, idan har juna biyu ne ya yi sanadin hawan jini, yawanci daga haihuwa ya ke tafiya.” 

A Karshe

Bincikenmu ya nuna mana cewa babu wani maganin da zai iya warkar da hawan jini, ana iya kula da shi a sanya ido yayin da ake kiyaye irin abincin da ake ci ta hanyar rage gishiri, da sauran abubuwan da ke kara dandanon girki da kuma zuwa motsa jiki a kai- a kai.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button