Zargi: Wasu masu amfani da shafin facebook na zargin wai dakarun sojin Najeriya sun kama wata tifar yashin da ta boye manyan makamai na zamani da albarusai yayin da ta ke kan hanyar kai wa ‘yan bindiga makaman a Birinin Gwari jihar Kaduna.
Cikkaken Bayanni
Ranar 13 ga watan Yuli wasu hotuna uku da wani rahoto suka bayyana a shafin Facebook da zargin cewa sojoji sun cafke wata motar kasar da ta boye makamai, a ciki har da makamai masu linzami da harsasai a hanyar Kaduna zuwa Birnin-Gwari. Tuni wannan rahoton mai tsawon gaske wanda aka rubuta da hausa da turanci ya dauki hankali da ma’abota shafin na facebook suna rabawa suna sake rabawa zuwa sauran shafukan soshiyal mediya.
Rahoton ya ce bayan da aka juye kasar da motar ta debo, sojojin sun gano harsasai 6000, da bindigogi kiran AK 47 guda 34, da rokoki/makamai masu linzami 3, da riguna 6 na makamai masu fashewa ko kuma aiwatar kunar bakin wake, da sauran manyan makamai na zamani. Haka nan kuma rahoton ya nuna cewa wasu manyan ‘yan Najeriya ne ke bayan sakon makaman.
In ji rahoton, da ma can direban motar ya ce an biya shi nera 200,000 ya kai makaman wani gandun daji a Birnin Gwari, kuma ya tsegunta cewa wadanda suka aike shi suna biye da shi a wata mota kirar Toyota Highlander. Su kuma dakarun sojin a cewar rahoton, sun kama mutane 5 a cikin motar tare da direban, ke nan sun dauki mutane 6 sun kai su wani wuri a daya daga cikin barikokin sojin da ke jihar Kaduna dan kara musu tambayoyi.
Abatam Nwosu wani mai ma’abota 3,918 a shafin facebook ya wallafa rahoton wanda kuma aka raba sau 22. Haka nan kuma Dahiru Mukhtar shi ma mai amfani da Facebook ya wallafa labarin da harshen hausa tare da hotunan bogin da aka sa. Nan ma an sake raba labarin sau 58. A shafin Instagram wani sanannen marubucin ra’ayoyi a shafin yanar gizo Muhammad Auwal Muazu (@hausaa_fulani) wanda ke da ma’abota 560, 000 shi ma ya sa rahoton da hotunan a shafin shi.
Tantancewa
A duk shafukan da muka ambata, an wallafa rahoton tare da hotuna uku, a ciki har da wanda ya nuna irin motar da suke zargi sojojin sun kama da makaman.
Tantance hoton farko
Hoton farkon na dauke da hoton motar da ake zargi. Motar na da launin Ja da fari. Bisa dukkan alamu da daddare aka dauki hoton domin ya yi duhu kuma motar ba ta fita da kyau ba. Da muka sanya hoton a manhajan tantance hotuna na Yandex da TinEye ba mu sami wani bayani ba. Dan haka sai muka sa google. Sai dai a nan binciken ya kai mu kan ainihin shafin da ya wallafa hotunan rahoton ne tun farko, da suaran shafukan da suka dauki labarin.
Tantance hoto na biyu
Hoto na biyu ya nuna wata ma’ajiyar makaman zamani har da rokoki/makamai masu linzami. Da muka duba manhajan binciken hotuna na Yandex, mun ga cewa an yi amfani da hoton a shafuka da dama a yanar gizo. Misali akwai hoton a wani labarin da kasidar Time ta Amirka ta wallafa, inda ta bayyana makaman cikin hoton a matsayin wadanda dakarun Najeriya suka anshe daga hannun kungiyar Boko Haram a jihar Borno, wanda kuma suka bayyana wa manema labarai ranar 5 ga watan Yuni. Kasidar Time ta ce ta sami hoton daga kamfanin dillancin labarai na AFP kuma ta bayyana Quentine Leboucher a matsayin wanda ya dauki hoton.
Gidan talbijin na i24 News ma ya yi amfani da hoton, nan ma an bayyana Quentine Leboucher na AFP a matsayin wanda ya dauki hoton, sannan su ma sun danganta hoton da labarin dakarun da suka anshe makaman a hannun ‘yan kungiyar Boko Haram ranar 5 ga watan Yuni.
Tantance hoto na uku
Mun yi amfani da TinEye, kuma bincikenmu ya danganta hoton da labarai 78. TinEye ya nuna mana cewa hoton ya fara bayyana a shafukan yanar gizo ne a shekarar 2018. Manhajan Yandex ma ya nuna cewa kafofin yada labarai na kasa da kasa sun yi amfani da hoton sau da yawa, musamman a labaran da suka danganci takaita shigar bindigogi masu sarrafa kansu hanun fararen hula a Amirka.
Wani rahoton da News@Northeastern ta rubuta da taken “shin dokokin bindigan “Jan tuta” za su hana harbin kan mai uwa da wabi? Ya bayyana cewa mahukunta sun kwace makaman ne daga hanun wasu sun nuna wa manema labarai a birnin Los Angeles ranar talata 9 ga watan Oktoba 2018. Jaridar ta bayyana sunan Jae C. Hong a matsayin wanda ya dauki hoton.
Jaridar siyasa ta Politico a Amirka ita ma ta yi amfani da hoton a wani labari mai taken: “Canada ta sanya takunkumi kan amfani da bindigogin masu salon kai hari bayan da aka yi kashe-kashe a Nova Scotia,” ita ma jaridar San Franciso Chronicle wadda ta yi amfani da hoton ita ma ta ambato Jae C. Hong a matsayin wanda ya dauki hoton lokacin da ‘yan sanda suka gabatar da makaman da suka anshe ranar 9 ga watan Oktoban 2018.
Tantance Rahoton
Majiyoyin tsaro a Kaduna sun karyata rahoton, suna kiran shi labarin karya. Da ‘yar jaridar da ta rubuta wannan labarin ta tuntube mai magana da yawun dakarun Najeriya 1 Division, Col. Ezindu Idimah, ya ce an kaga labarin ne kawai domin ba su taba yin kame irin wannan ba. Jami’an ‘yan sandan Kaduna ma ta bakin kakakin rundunar ASP Mohammed Jalige sun ce binciken da suka yi bai nuna musu cewa an kama wasu a hanyar da ke tsakanin Birnin Gwari da Kaduna ba. Shi kansa Jalige ya ce wasu ne suka kaga labarin suka sa domin su kulla manakisa ko kuma su cimma wani buri.
A karshe
Rahoto da hotunan da ke yawo a kafofin sadarwa suna bayyana cewa dakarun sojin Najeriya sun kama wata motar kasa dauke da makamai na zamani karya ne domin biyu daga cikin hotunan da aka yi amfani da su an dauko ne daga wasu rahotannin da aka yi a baya, wato daya a shekara ta 2013 dayan kuma a 2015 kuma bamu samu hujjojin da za su iya taimaka mana wajen gano inda aka sami hoton motar da ake zargi an ga makaman a ciki ba.