African LanguagesHausa

Weah ya amince ya sha kaye! “Boakai ya sami mafi yawan kuri’u”

Getting your Trinity Audio player ready...

Tun kafin hukumar zabe ta NEC ta sanar da wanda ya yi nasara a zaben kasar Laberiya, shugaba George Weah ya fito ya taya abokin hamayyarsa, shugaban jam’iyyar UP, amb Joseph Boakai murna a matsayin zababben shugaban kasa. Mr Weah ya taya shi murna ya kuma wallafa sakon taya murnar a shafin faccebook din fadar shugaban kasa 

“Sakamakon farko da aka sanar a yammacin yau, duk da cewa ba’a kammala irga kuri’un ba, na nuna cewa Joseph N Boakai ya ba ni rata sosai da ba zan iya kamowa ba. ‘Yan mintoci kadan da suka wuce, na yi magana da zababben shugaban kasar dan in taya shi murna in kuma tabbatar mi shi da cewa zan ba shi hadin kai wajen yin duk wani aikin da ya ke so mu yi dan inganta kasar mu ta gado wato Laberiya. Ina mika sakon taya murna ta ga Boakai da magoya bayansa, da wadanda suka shirya masa yakin neman zabe. Allah shugabancin shi ya kawo dimbin nasarori wa ‘yan Laberiya, Allah kuma ya sa kasarmu ta sami cigaba a karkashin jagorancinsa,” Weah ya bayyana.

Shugaban kasar, da ya ke jawabi ya yi kira ga magiya bayansa na jam’iyyar CDC cewa su karbi sakamakon da aka bayar su koma su yi shirin tinkarar zabukan shekarar 2029 sadda suke da wata damar ta maido iko a hannun jam’iyyar ta su.

“Ina kira a gare ku duka da ku yi misali da ni ku yi na’am da sakamakon wannan zaben. Ku koma gida kuna la’akari da cewa burin mu wa Laberiya harin yanzu na da kwari. Ba mu da yawa a wannan lokacin amma za mu sake samun wata damar. Gobe, mu cigaba da duk ayyukan da muka saba yi kullun sa’annan ku zo ku same ni a hedikwatar jam’iyya inda za mu yi waiwaye adon tafiya kan irin rawar da muka taka sa’annan mu yi shirin yadda za mu sake dawowa a shekarar 2029.

“Yau, CDC ta rasa zabe, amma Laberiya ce ta yi nasara. Wannan lokaci ne na shan kaye cikin mutunci, lokaci ne na daraja kasarmu a kan jam’iyya, da kuma kishin kasa a kan son kai. Zan cigaba da kasancewa shugaban kasa har zuwa lokacin da za’a mika mulki kuma zan cigaba da aiki dan inganta Laberiya. Mu manta da banbance-banbancen da aka rika fama da su lokacin yakin neman zabe mu zo mu hada kai mu zama tsintsiya madaurinki daya.”

Sakon ya zo sa’o’i kadan bayan da shugaban Hukmar Zabe na NEC ya sanar da sakamakon zaben a zagaye na biyu na zaben da aka gudanar ranar Talata.

Tsohon mataimakin shugaban kasar wanda shi ne shugaban jam’iyyarta UP, Joseph Boakai ya sha gaba a zaben na zagaye na biyu.

Kawo yanzu dai, Mr Boakai ya sami kuri’u 814,428 na yawan kuri’un da aka jefa, abun da ke nufin kashi 50.64 cikin 100 kuma mazaba daya ce rak ba’a riga an bayyana sakamakonta ba. 

Shugaba mai mulki, George Weah shi kuma ya sami kuri’u 793,910, wanda ke zaman kashi 49.36 cikin 100 na kusan kashi 99.98 na kuri’un da aka riga aka irga.

Kafin a bayyana sakamakon a hukumance, DUBAWA ta dan gudanar da bincike kan makomar siyasar Laberiya yanzu da aka sami wannan sakamakon.

‘Yan Laberiya sun jefa kuria a karo na biyu ranar 14 ga watan Nuwamba, dan zaban shugaban kasar da zai jagorance su na tsawon shekaru shida masu zuwa. An kai ga yanke shawrar zuwa zagaye na biyu na zaben ne saboda an gaza samun shugaba daya a cikin ‘yan takarar 20 din da suka tsaya a zagayen farko na zaben ranr 10 ga watan Oktoba ta yadda sakamakon zai cika sharuddan da kundin tsarin mulkin kasar ta tanadar a  kundin tsarin mulkin Laberiya  na shekarar 1986 

Me Kundin Tsarin Mulkin Ya ce? 

Sashi na 83 na kundin tsarin mulkin Laberiya ya ce 

“(a) Zaben shugaban kasa da mataimakinsa da mambobin majalisar dattawa da na wakilai a jihohi 53 da ke jamhuriyar zai gudana ne ranar Talata ta biyu a watan Oktoba na kowace shekarar da ake zabe.”

(b)  In ban da shugaban kasa da mataimakinsa, duk sauran wadanda za’a zaba za’a ayyana sakamakonsu ne bida la’akari da duk wanda ya sami mafi yawan kuri’u ko da kuwa da mafi karancin rinjaye ne.

Zaben shugaban kasa da mataimakin shi kuwa dole ne sai akwai mafi yawan rinjaye na duka kuri’u masu sahihancin da aka kada. Idan har babu dan takarar da ya sami mafi yawan rinjaye, dole a je zagaye na biyu na zaben ranar talata na biyu a wayta mai kamawa. “Yan takarar da suka fi samun kuri’u ne za su kasance kan kuri’un zaben da za’a yi a karo na biyu.

Batun zaben 10 ga watan Oktoba: 

Kamar yadda Hukumar Zabe ta Kasa ta sanar ranar 24 ga watan Oktoban 2023, An=mb Boakai da shugaba mai ci George Weah ne suka sami mafi yawan kuri’u a zagayen farko na zaben da aka yi ranar 10 ga watan Oktoba. A zagayen farko shugaba George Weah ya sami kuri’u dubu dari takwas da tamanin da bakwai (804,087) wanda ya bashi kashi 43.83 cikin 100 na jimilar kuri’un da aka kada yayin da shi kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai wanda ke jam’iyyar adawa ta UP ya sami kuri’u dubu dari bakwai da chasa’in da shida da dari tara da sitin da daya, (796,961) wanda ya ba shi kashi 43.44 cikin 100. 

Jim kadan bayan da aka sanar da sakamakon zagayen farko na zaben, jam’iyyun biyu suka shiga neman kuri’u suka kuma fara kulla dangantaka da kananan jam’iyyu dan yin dammarar tinkarar zaben zagaye na biyu. Bisa dukkan alamu dai jam’iyyar adawa ce ta di samun goyon baya daga kananan jam’iyyun da ba su yi tasiri sosai a zaben ba. Wuni biyu bayan zagaye na biyu na zaben, Ms Davidetta Lansanah-Browne ta sanar da zababben shugaban kasa.

Sakamako daga zagaye na biyu na zaben.

Sakamakon Hukumar Zabe ta Kasa na nuna cewa Ambasada Boakaiya sami kuri’u 814,428, wanda ya ba shi fiye da kashi 50 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada yayin da shi kuma George Weah ya sami kuri’u 793,910, kenan kashi 49.36 cikin 100. 

An sami sakamakon ne daga rumfunan zaben kasar 5,889. Haka nan kuma daga cikin mutane sama da miliyan biyun da suka yi rajistar zabe, wato 2,471,617 mutane sama da miliyan daya da rabi wato 1,634,126 suka yi zabe.  Yanzu da Weah ya amince ya sha kaye, Joseph Boakai zai jagoranci kasar na tsawon shekaru 6 masu zuwa.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button