African LanguagesHausa

Yaudara! Mutumin da ya bayyana cewa ya mayar da kansa kare ya sanya kaya na musamman ne ba karen ya zama a zahiri ba

Getting your Trinity Audio player ready...

Zargi: A shafin Facebook wani mutum ya wallafa bidiyon wani mutum wanda ake zargi da ya sauya halittarsa zuwa ta kare a kan kudi Dalar Amurka 14,000.

Yaudara! Mutumin da ya bayyana cewa ya mayar da kansa kare ya sanya kaya na musamman ne ba karen ya zama a zahiri ba

Sakamakon binciken:  Labarin da aka wallafa karya ne, bincike ya gano cewa Toco mutumin da aka ce ya sauya kansa dan asalin kasar Japan wanda ya sanya “kaya na musamman mai kama da kare” wanda ya siya a kan Dalar Amurka 15,000.

Cikakken sakon

EmmyG, Wanda ke amfani da shafin Facebook a baya-bayan nan ya rarraba wani bidiyo cewa wani mutum da ya sauya halittar daga mutum zuwa kare a kan kudi Dalar Amurka 14,000 ya bayyana a karon farko a bainar jama’a.

A wani bidiyo mai tsayin  dakika arba’in da hudu an ga wata mata da ba a bayyana sunanta ba ta tana tsaye  da karen a inda mutane ke wucewa. 

Bayan da aka wallafa wannan bidiyo a ranar 29 ga watan Yuli, 2023 ya ja hankali na masu kallo miliyan uku da dubu dari uku da wadanda suka nuna sha’awa (like) 18,000 da wanda suka raba 4,900 da mabanbantan masu tsokaci 4,800.

Sauya halitta ba sabon labari ba ne a duniyar labarai, sai dai sauya halittar dan Adam zuwa dabba baki daya abu ne da zai ja hankalin al’umma kamar Michael Egbayelo, wanda ya nuna tantamarsa kan sahihancin wannan labari.

A bangaren yin tsokaci ya ce “Wannan labari ba gaskiya ba ne, babu wata fasaha a duniya da za ta rage tsawon dan Adam sai dai in datse gababunsa aka yi, ta yaya ne za a rage tsayi dan Adam zuwa na kare?”

Kamar Mr. Egbayelo wani mai amfani da shafin,  Emmanuel Austin Emeka, ya ce ba zai amince da wannan labari ba a matsayin na gaskiya.

“Ban amince da wannan labari ba, wannan dai wani nau’ine na kare ……………ba za mu amince da duk labarai da ke shafukan sada zumunta ba.”kamar yadda ya rubuta.

Duba da yanayin daukar hankali na labarin da irin hadari da irin wannan labarin yaudara ke da shi ya sanya DUBAWA ya shiga aikin bincike don gano sahihancin labarin.

Tantancewa

Bayan nazari kan wannan bidiyo DUBAWA ya gano dabi’u wadanda suka saba wa kare . alal misali yana rigingine yana tsalle da kafa sabanin ya tsaya a kafar yayi gudun, sannan babu alamar motsi  ko bude baki duk da bukatar ganin yayi hakan da macen ta yi. 

Ganin wadannan shedu na farko da muka gano ya sanya mun shiga aikin bincike gadan-gadan ta hanyar amfani da Google. Inda muka gano wallafa da dama kan wani “Toco” wani mutumin kasar Japan da labarinsa yayi shuhura a 2022 bayan da ya siyi rigar da in an sanya za a yi kama da kare a kan kudi sama da Dalar Amurka 15,000 “a kokarin  bayyana tamkar dabba.”

A cewar Mirror, kafar yada labarai da ke a Birtaniya ya kashe kimanin kudi Yen miliyan biyu kudin da yayi daidai da Fam  £12,480 don yayi kama da dabba da ya fi kauna wato kare.”

Wannan shine abin da ya dade yana mafarki a rayuwarsa Toco “ya sayi kayan da in an sanya za a yi kama da dabba daga cibiyar Zeppet da ke kasar Japan da ta yi suna wajen samar kayan kirkira da abubuwan da ake bukata a fina-finai.”

A wasu labaran kuma an nunar da cewa yana da subscribers wadanda suke bibiyar shafinsa na Youtube wadanda yawansu ya kai dubu hamsin da daya da dari shida ya kira wannan tasha da suna “I want to be an animal.” “ Ina so na zama dabba.”

A karin bayani ga me da ita ya rubta”Ina so na zama dabba, ta yadda zan zama nau’in karen  collie na daban!” Wannan tasha za ta rika wallafa maku hotunan bidiyo na ban mamaki na’uikan karnukan na collie.”

Toco ya bayyana a karon farko sanye da kayan da ke kama da kare a ranar 12 ga watan Afrilu na shekarar 2022. Kaw yanzu ya wallafa bidiyonsa sanya da wadannan kaya sau  37.

His latest upload, “Dogs and people’s reactions to seeing a realistic dog costume!” made him go viral again. Presently, it already has over 6 million views.

Abin da ya wallafa a baya-bayan nan “Karnuka da abin da al’umma ke cewa bayan sanya kayan da idan an sa za a zama tamkar kare!” Bidiyon a wannan karo ma ya sake karade shafukan sada zumuntar  ”

A karshe

Kamar yadda rahotanni suka nunar Toco dan kasar Japan ne da ke da burin zama dabba. Ko da dai yayi kama da wata dabba ya cimma burinsa na siyan wani nau’in kaya mai kama da kare . Ba da labarin cewa wani ya mayar da kansa kare a don haka labarin karya ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »