Getting your Trinity Audio player ready...
|
Yayin da ake bukin ranar mata ta duniya Mariya Shu’aibu ta yi ma nazarin rayuwar mata a Kano – waiwaye da hanyoyin da suke bi wajen inganta rayuwarsu
Shekaru 30 da sanya hannu kan yarjejeniyar Beijing wadda ta fadada hakkokin mata da sauran harkokin da suka shafi mata da ‘yan mata ana iya cewa an sami sauyi a jihar Kano. A shekarun baya, jin ra’ayin mace ko a ce mace na samun albarka a kasuwancinta, tana tsayawa takara ko ma wadda ke da da iko a kan rayuwarta abu ne mai wahala sai dai watakila a mafarki.
Al’adun gargajiya, rashin samun ilimi, da kalubalen da ke tattare da irin tsarin rayuwar da ta ke gudanarwa sun hana mata damar taka rawa a wuraren daukar matakai. Amma yanzu akwai sauyi, ko da yake a hankali yak e zuwa, ana iya ganin wasu alamu a bayyane. Yanzu haka ‘yan mata da dama na makaranta, mata da yawa sun samu ‘yancin neman kudi, kuma kariya ta shari’a akan cin zarafi ya karu.
Sai dai duk da haka, tafiyar ba ta kare ba. Har yanzu akwai mata da dama da ke fama da irin kalubalen da iyayensu da kakanninsu suka fuskanta—cin zarafi, rashin wakilci a siyasa, da kuma al’adun da ke hana ci gaba.
Yayin da duniya ke bikin Ranar Mata ta Duniya ta 2025, lokaci ya yi da za a yi nazari: Har yaushe matan Kano suka zo matakin da ake a yau? Wadanne gwagwarmaya aka yi wajen samun nasara? Kuma menene ke ci gaba da hana a samu daidaito na gaskiya?

Ilimi: Warware Sarkar Auren Wuri
A baya, ilimin ‘yan mata a Kano an rika masa kallon gata — wato wani abun da za a iya sadaukarwa don auren wuri ko ayyukan gida. Amma a cikin ‘yan shekarun nan, sauyi ya fara shiga. Iyaye, suna samun kwarin gwiwa daga labarun nasara da kuma manufofin gwamnati da ke karfafa ilimin ‘yan mata, suna fahimtar amfanin barin ‘ya’yansu mata su kammala karatu ko da kuwa zai dauki lokaci.
Yau, matasa mata a Kano sun daina kammala daga sakandare; suna zama likitoci, injiniyoyi, da lauyoyi. Sai dai wannan ci gaban bai kai ko’ina ba. A karkara, talauci da takunkumin al’ada har yanzu suna hana ‘yan mata damar karatu. Dan haka, yaki da jahilci bai kare ba, amma nasarorin da aka samu sun sauya rayuwa kuma suna cigaba da yin hakan.
Daga Kasuwanni zuwa Ofisoshin Manyan Hukumomi
Mata sun shafe shekaru yanzu suna sauya dabarun kasuwanci, kuma matan Kano su ne ginshikin kasuwanci na gargajiya — suna sayar da abinci, zane, da kayan gida a kasuwanni masu cike da hayaniya. Amma samun rancen kudi, jagoranci, da kuma hanyar shiga hanyoyin kasuwanci ya kan kasance da wahala. Wannan abu ne da ke sauyawa sannu a hankali.
Daya daga cikin manyan labarun nasara ita ce ta Farida Musa Kalla, wacce ta kafa FMK Clothing, daya daga cikin manyan kamfanonin kaya a Kano. Farida ta fara daga tushe (da N600,000 da mahaifiyarta ta bata domin ta sayi mota, amma ta ajiye kudin a banki kuma ta fara sayen kayan sawa don siyarwa) tun tana daliba ta na sayar da kayan zanen gida a makaranta har zuwa lokacin yi wa kasa hidima (NYSC) Ta yi fuskantar matsin kudi da kalubalen al’ummar da ke hana mata tafiyar da manyan kasuwanci, amma da hakuri da kwazo, ta gina FMK Clothing zuwa wani babban suna a Kano, kuma da haka tana tabbatar da cewa mata na iya cin nasara a harkar kasuwanci.
Labarai irin na Farida hujjoji ne na juriya da kwazon matan Kano, wadanda da dama yanzu suna amfani da shirin microfinance, horon sana’a, da kuma dandalin sada zumunta don habaka kasuwancinsu. Sai dai har yanzu matsaloli na nan — samun rance babbar matsala ce, kuma ra’ayin al’umma yana ci gaba da rage girman kasuwancin da mata ke iya yi.

Yaki da Cin Zarafin Mata
Yanzu ba’a yin shiru ko jin nauyin magana dangane da cin zarafin mata a Kano, a baya ya kasance sirrin da akan boye, sa’annan yawanci wadanda aka ci zarafinsu bas u da wurin kai kuka, kuma masu laifi suna yawo da ‘yanci ba tare da hukunci ba. Amma yau, abubuwa sun sauya. Kungiyoyi kamar Ma’aikatar Kula da Harkokin Mata, FIDA (Kungiyar Lauyoyin Mata), da CITAD (Cibiyar Fasaha da Cigaban Al’umma) sun shiga gaba wajen yaki da cin zarafi a Kano. Ta hanyar bayar da taimakon shari’a, wayar da kai, da amfani da fasaha, suna tabbatar da cewa wanda aka ci wa zarafi yana samun adalci. Cibiyar Waraka Sexual Referral Centre ita ma ta zama haske ga wadanda aka ci zarafi, tana bayar da kula ta lafiya, taimakon shari’a, da shawarwari. A waje guda kuma, CITAD ta kirkiri hanyoyin fasaha da ke ba mutane damar kai rahoton cin zarafi cikin sirri da kwanciyar hankali.
Duk da haka, tsoro da kunya har yanzu suna hana mutane da yawa magana, kuma jami’an tsaro da yawa ba sa daukar mataki da sauri. Yakin neman adalci bai kare ba, amma ci gaban da aka samu yana bayyane.
Mata a Siyasa: Har yanzu suna neman kujerun mukamai
A shekarar 1995, ra’ayin mace tana rike da mukamin siyasa a Kano abu ne mai wahala. Yau, mata da dama suna shiga siyasa, amma adadinsu har yanzu kadan ne sosai. Ra’ayoyi na gargajiya, matsalar kudi, da siyasar da maza suka mamaye na hana mata shiga mukaman shugabanci. Wadanda suka samu nasara sun yi hakan ne da matsanancin gwagwarmaya. Amma nasararsu ta bude kofar dama ga matan da ke tasowa masu sha’awar siyasa. Kalubalen yanzu ba karfafa mata su tsaya takara ne kadai ba — amma tabbatar da cewa suna da kayan aiki da goyon baya don su samu nasara da jagoranci mai nagarta.

Mene Ne Na Gaba? Hanyar samun daidaito na gaskiya
Duk da ci gaban da aka samu, aikin bai kare ba. Yakin kare ‘yancin mata a Kano dole ne ya ci gaba da sabon kuzari da jajircewa. Ga abubuwan da suka kamata a yi gaba:
- Karfin Aiwatar da Dokoki: Dole a tabbatar dokokin kare hakkin mata suna aiki, ba wai a rubuce kawai za su cigaba da kasnacewa ba a tabbatar an aiwatar.
- Sauya Al’adu: Dole ne a jawo malamai da shugabannin gargajiya domin canza al’adun da ke hana ci gaba.
- ‘Yancin Tattalin Arziki: A samar da karin kudade, jagoranci, da horo ga mata ‘yan kasuwa.
- Karin Wakilci a Siyasa: A samar da jagoranci da tallafi domin mata su shiga siyasa kuma su yi nasara.
Lallai matan Kano sun yi nisa, amma hanyar zuwa daidaito har yanzu tana kan gina ta. Shekaru talatin da suka wuce sun tabbatar da cewa sauyi yana yiwuwa — amma sai da jajircewa, fafutuka, da aiki. Yayin da muke bikin Ranar Mata ta Duniya ta 2025, muna girmama matan da suka fafata don ci gaba da wadanda har yanzu ke ci gaba da gwagwarmaya, suna kin amincewa da takura. Gobe na wadanda suka shirya kalubalantar al’ada ne — kuma matan Kano suna tabbatar da cewa sun shirya karbe wannan dama.