African LanguagesHausa

Gaskiya ne! Brig.-Gen. Olakunle Nafiu shi ne sabon shugaban hukumar NYSC

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar NYSC

Gaskiya ne! Brig.-Gen. Olakunle Nafiu shi ne sabon shugaban hukumar NYSC

Hukunci: Gaskiya ne, Binciken Dubawa ya gano cewa Shugaba Tinubu ya sauya shugabancin hukumar ta NYSC.

Cikakken Bayani

Hukumar matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) hukuma ce ta Najeriya dake kula da matasa shirin yi wa kasa hidima da gwamnati ta tilasta wa duk matasan da suka kammala karatun a makarantun gaba da sakandire.

Shirin na da manufar bunkasa sana’o’i, da kuma cudanya tsakanin al’ummar Nijeriya mabanbanta. 

Hukumar NYSC na karkashin jagorancin Darakta Janar (DG), wanda ke da alhakin kula da ayyukan hukumar da aiwatar da manufofinta.

A baya-bayan nan dai an yi ta yawo da wani labari a shafukan sada zumunta dake cewa Shugaba Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar NYSC, kamar yadda muka zakulo a nan da nan da kuma nan.

Wasu daga cikin wadannan da’awar sun tayar da kura, kasancewar labarin na zuwa ne yayin da matasan masu yi wa kasa hidima ke kokawa akan rashin biyansu sabon alawus na naira 77,000 da gwamnati ta amince a fara biya, watanni biyar da suka gabata.

A kan haka ne Dubawa ta yi bincike domin tabbbatar da sahihancin labarin, da kuma samar da bayanai da za su rika taimaka wa ‘yan Najeriya yanke shawara akan abubuwan da suka shafi rayuwarsu.

Tantancewa

Binciken da Dubawa ta yi ta gano cewa wannan labarin gaskiya ne, kamar yadda gidan radiyon Nijeriya FRCN ya wallafa a shafin sa na yanar gizo.

“Shugaba Tinubu ya nada Kunle Nafiu Darakta Janar na NYSC” inji FRCN.

Tuni dai da sabon shugaban na hukumar matasa masu yi wa kasa hidima Brig.-Gen. Olakunle Nafiu, ya karbi aiki a matsayin darakta janar na hukumar NYSC na 23.

Gaskiya ne! Brig.-Gen. Olakunle Nafiu shi ne sabon shugaban hukumar NYSC
  • Yayin da sabon shugaban NYSC ke karbar ragamar aiki daga tsohon shugaba

A cikin jawabin da ya gabatar a lokacin da ya karbi ragamar aiki a hannun DG mai barin gado na hukumar, Brig.-Gen. Yu’shau Ahmed, Kunle Nafiu ya ce zai mayar da hanlai wajen inganta jin dadi da walwalar matasa masu yi wa kasa hidima.

“Za mu yi aiki tuƙuru don tabbatar da cewa hidimar da za su yi wa kasarsu, na ɗaya daga cikin abubuwan da ba za su manta da su ba a rayuwarsu” a cewa DG Nafiu.

A Karshe

Gaskiya ne, an nada sabon shugaban hukumar matasa masu yi wa kasa hidima Brig.-Gen. Olakunle Nafiu kamar yadda kafafen yada labarai daban-daban suka ruwaito.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »