Getting your Trinity Audio player ready...
|
‘Yancin aikin jarida na da mahimmanci ga mulkin dimokiradiyya. A tsarin mulkin dimokiradiyya irin na Najeriya, wajibi ne kafafen yada labarai su kasance masu ‘yancin walwala, ta yadda ‘yan jarida za su yi aiki ba tare da fargabar wani hari ba.
Babu al’ummar zamanin da za ta iya rayuwa ba tare da kafafen yada labarai ba kuma babu wanda zai iya sakewa yadda ya kamata idan har kafafen yada labarai ba su da ‘yancin walwala. Wannan ‘yancin walwalar ‘yan jaridan da na kafafen yada labarai ne zai taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu ba tare da barazana ko kutse ba.
Bisa bayanan kundin da ke nazarin yanayin ‘yancin walwalar ‘yan jarida a duniya na 2023 wanda da turanci aka fi sani da World Press Freedom Index, Najeriya ta kasance kasar da ta fi hadari da wahala wa ‘yan jarida, wadanda kusan kowani lokaci ana sanya mu su ido, ana kai my si hari, sa’annan a kan kama su ba tare da kwararan dalilai ba kamar yadda aka gani lokacin zaben 2023.
Da ma dai akwai abubuwa da dama da kan kasance kalubale ga samar da ‘yancin ‘yan jarida a Najeriya.
Dan haka abun mamaki ne a ce Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris ya fadi cewa akwai ‘yancin aikin jarida a mafi yawancin yankunan Najeriya kuma ma ba’a taba kama dan jarida ba tun bayan da gwamnatin Tinubu ta fara aiki.
Ministan ya bayyana hakan ne lokacin wata ganawar da ma’aikatar ta sa ta shirya tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Muhalli da UNESCO dan gudanar da bukin ‘Yancin Walwalar Kafafen Yada Labarai na Duniya 2024 ranar uku ga watan Mayu.
A cewar ministan, “Ni ban taba ganin wani, tun bayan da wannan gwamnatin ta fara aiki, alal misali, wanda aka taba kulle shi a gidan kaso ko kuma ya shiga buya saboda ‘yancin aikin jarida ba.
“Mun san cewa hakan ya taba faruwa a wannan kasar a baya. Wasu shekaru gommai da suka wuce, mun san cewa lokacin kafin ka yi rahoto sai ka bar kasar. Zan iya fada muku cewa ‘yan jarida a Najeriya yawanci suna da ‘yanci, amma wannan ‘yancin zai fi karfi ne idan har ana kamanta gaskiya ana kuma gudanar a abubuwa a bayyane, a yanayin da muke rahotanni….”
Lokutan da aka musgunawa ‘yan jarida a karkashin jagorancin gwamnatin Tinubu
A ‘yan shekarun baya-bayan nan, ‘yan jarida a Najeriya baki daya sun fuskanc kame-kame, dauri, kotu, muzgunawa, zargin kotu da duka.
Kafin uku ga watan Mayun 2024, sadda ministan ya yi wannan furucin, an dauki rahotannin lokutan da aka kama ‘yan jarida ba tare da kwararan dalilai ko ma la’akari da tanadin doka ba. Misali, ranar 21 ga watan Fabrairun 2024, Kasarahchi Aniagolu, wani dan jaridan da ke aiki da jaridar The Whistler, ya shiga hannun ‘yan sanda wadanda suka kama shi, suka yi masa duka sa’annan suka kulle bisa zarginsa da daukar rahoto ba tare da izininsu ba.
Haka nan kuma ranar 115 ga watan Maris 2024, Segun Olatunji, Eduta da FirstNews, shi ma jami’an sojoji sun kama shi sun kulle. Ya shiga hannun sojojin ne saboda wani rahotan da ya wallafa dangane da wani jami’i daga Hukumar Leken Asirin Ma’aikatar Tsaro (DIA) wanda ke karkashin ma’aikatar tsaron Najeriya, wanda ake zargi da bayar da kwangiloli ba tare da bin ka’ida ba.
Bacin haka, Daniel Ojukwu, wani dan jaridan da ke aiki da Gidauniyar Bincike Mai Zurfi Na Aikin Jarida shi ma an kama shi ranar daya ga watan Mayun 2024, kwanaki biyu kafin ministan ya yi wannan furucin na cewa ba’a taba kama dan jarida ba tun bayan da Tinubu ya karbi madafun iko.
Ranar ce kuma ranar ‘Yancin Aikin Jarida na Dunya, sadda al’ummar kasa da kasa ta taro dan yin bukin ‘yancin walwalar ‘yan jarida ko’ina a duniya. Sa’annan rana ce da ke wa jama’a tuni dangane da mahimmancin kare hakkin ‘yan jarida da tabbatar da cewa suna da zarafin dauko rahotanni ba tare da tsoron danniya ko tashin hankali ba.
Tsakanin 29 ga watan Mayun 2023, sadda Tinubu ya dare karagar mulki, da Mayun 2024, an sami rahotanni da yawa na lokutan da aka tsare ‘yan jarida ba bisa ka’ida ba.
A cikin wannan lokacin ‘yan jarida fiye da 12 wadanda aka sani, jami’an tsaro ko sun kama su, ko sun tsare su ko kuma dai sun ci zarafinsu yayin da suke gudanar da aikinsu.
A wani lokacin ma, an kama ainihin shugaban kamfanin wallafa jaridan ne Precious Eze Chukwunonso, ranar 27 ga watan Mayun 2024. An kama Chukwunonso na kusan makwanni uku bayan da aka yi korafin rahoton da aka wallafa.
‘Yancin aikin jarida a Najeriya da kundin nazarin yanayin aikin jarida a duniya
A cewar kundin nazarin ‘yancin aikin jarida na World Press Freedom Index 2024, ‘yancin aikin jarida shi ne damar da ‘yan jarida da ma a al’umma baki daya ke da shi na zaba da, hadawa da yada labaran da ke da mahimmanci ga al’umma wanda ba ruwan shi da siyasa, tattalin arziki, shari’a ko zamantakewa, ba tare da barazana ga lafiyarsu ta jiki da ta kwakwalwa ba.
Walwalar gudanar da aikin jarida a Najeriya ya kara lalacewa a ‘yan shekarun da suka gabata. Makin da aka baiwa aikin jarida cikin walwala a kasar ya sauka daga 65.9 cikin 100 a shekarar 2013 zuwa 51.03 cikin 100 a shekarar 2024 (Inda 0 ke nufin tabarbarewa 100 kuma nasara)
Makin da Najeriya ta samu tsakanin 40-55 na nuna cewa aikin jarida na da sarkakiya.
Idan ana la’akari da kasar a matakin yanki, Najeriya na daga cikin kasashen da ke baya a wajen walwalar aikin jarida a yankin yammacin Afirka. A cikin kasashen, wani sakamakon binciken da aka yi na nuna cewa Najeriya na zaman kasa ta 14 cikin 16.
Bisa bayanan nazarin da kungiyar ‘Yan Jarida Mara Iyaka wato Reporters Without Borders a turance, yawancin hare-hare, da tsare mutane ba tare da wani dalili mai kwari ba, da kuma harbin da aka yi a kan ‘yan jarida kwanan nan a yankin Yammacin Afirka a Najeriya suka faru, musamman a lokutan zabe. Kusan ‘yan jarida 20 da kafofin yada labarai ne aka kai wa hari lokacin zabukan da aka yi a watannin Fabrairu da Maris na 2023.
Laifuffukan da aka yi a kan ‘yan jarida yawanci ba’a hukuntawa, ko da kuwa an gane wadanda suka aikata an kama su. Babu wani tsari na kasa da ke tabbatar da kariyar ‘yan jarida. Mahukunta na yawan sa musu ido kuma nan da nan sun yi musu barazana.
Bisa la’akari da wannan ne, za’a iya cewa yanayin ‘yancin walwalar aikin jarida a Najeriya ya yi kasa sosai.
Duk da cewa babu kasar da za’a ce ba ta da na ta matsalar idan ya zo batun ‘yancin walwalar aikin jarida, muna fatan ganin Najeriya ta dauki mahimman matakai wajen inganta kariyar ‘yan jarida ta yadda za su yi aikinsu yadda ya kamata — ba sani ba sabo.
Abin da kwararru ke cewa kan ‘yancin walwalar ‘yan jarida a Najeriya
DUBAWA ta yi magana da Busola Ajibola, kwararriya kan bunkasa kafofin yada labarai kuma mataimakiyar darektan Cibiyar ‘Yan Jarida, Sabbin Dabaru da Cigaba (CJID) dangane da ‘yancin walwalar ‘yan jarida a Najeriya.
Ta bayyana cewa da ma Najeriya na da tarihin muzgunawar da ‘yan sanda ke wa ‘yan jarida da kuma kama su ba tare da kwararan dalilai ba. Wannan yanayin ne ke yawan sa tsoro, abin da kuma ke hana su fitowa su kalubalanci abubuwan da ya kamata a ce sun kalubalanta, wanda kuma ya kai ga koma baya a yanayin walwalar gudanar da aikin jarida.
A cewar madam Ajibola, “Akwai wadansu tanade-tanaden doka da ba’a fayyace sosai ba, wadanda kuma ‘yan sanda ke yawan amfani da shi su ci mutuncin ‘yan jarida. Misali shi ne dokar laifin yanar gozo wanda ake kira Cybercrime Act. Duk da cewa an kwaskware wannan dokar, ‘yan sanda na cigaba da amfani da shi su zalunci ‘yan jarida.
“Akwai kuma batun bata suna, inda dan jarida zai rubuta labarin da ke da mahimmanci sosai saboda tasirin da ya ke da shi a akn al’umma ko kuma dai wani jami’in gwamnati, sai ‘yan sanda su juyya su kira shi bata suna. Wadannan dokoki ne da aka san ‘yan sanda na amfani da su wajen cin zarafin ‘yan jarida.
“Dangane da dokar intanet, a wannan shekarar kadai, Press Attack Tracker na CJID, wanda ke bin diddigin hare-haren da ake wa ‘yan jarida ya yi rahotanni kan lokuta 11 da ‘yan sanda suka gayyaci ‘yan jarida ko kuma suka zarge su da bin mutane a shafukan intanet ko kuma dai suka kama su suka kulle babu gaira ba dalili. Sun yi nasarar kama Daniel Ojukwu, wani dan jarida tare da Gidauniyar Bincike Mai Zurfi a Aikin Jarida (FIJ), kuma sun tsare shi na kusan kwanaki 10. Sun yi kokarin kama Nurudeen Akewusola na ICIR, amma ayyukan kungiyoyin farar hula sun hana hakan faruwa. Wadannan ne abubuwan da mek fuskanta a Najeriya,” a cewar Madam Ajibola.
A karshe
Sabanin abin da ministan ya bayyana, akwai ‘yan jarida da dama wadanda ko an kama su, ko an tsare su, ko kuma dai an ci zarafinsu tun bayan da shugaba Tinubu ya fara mulki. Baki daya dai ‘yancin walwala na aikin jarida na tabarbarewa, kuma aikin jarida na kara wahaka sakamakon thare-haren da ake kai wa kan ‘yan jarida, kutse na harkokin siyasa da barazana.
Wannan rahoto an fitar da shi ne karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 karkashin shirin kwararrun masu gano gaskiya labari na Kwame Karikari da hadin giwar Dataphyte a kokarin da ake yi na mutunta fadin gaskiya a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a Najeriya.