African LanguagesHausa

Yaya gaskiyar abubuwan da Tinubu ya bayyana a cikin manufofin da ya gabatar?

Nan da ‘yan watanni kalilan, hukumar kula da zabe, wato Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta a Najeriya (INEC) za ta gudanar da zabe.

Za’a yi zaben shugaban kasa ranar asabar 25 ga watan Fabrairu tsakanin ‘yan takara 18 daga jam’iyyu daban-daban

Ranar 28 ga watan Satumban 2022, ta sanar a hukumance cewa ta kaddamar da yakin neman zabe, tun lokacin aka fara fitar da kudurori da manufofin jam’iyyu, wasu dama sun riga sun wallafa na su gabannin sanarwar hukumar zaben.

Da ma al’adar zaben ta tanadi kowani dan takara da ya bayyana kudurorinsa ga masu zabe da ma duk wani shirye-shiryen da su yi kan yadda za su gudanar da gwamnati idan su ka hau mulki.

Kuduri mai kyau shi ne bayyana manufofin jam’iyya ga masu zabe kafin lokacin zaben ya kai. Wannan ya kunshi bayani dalla-dalla dangane da kudin da za’a kashe kan aiwatar da manufofin da ire-iren alfanun da ake sa ran gani bayan nan. Wannan kan fadakar da illimantar da masu zabe kuma ya taimaka musu wajen yanke shawarar wanda za su zaba da ma jam’iyyar da fi dacewa da abin da su ke son gani a kasarsu.

Bola Tinubu wanda ke neman kujerar shugabancin kasar a inuwar jam’iyyar APC mai mulki tare da abokin takararsa Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno, sun wallafa ta su manufar kwanan nan wanda ya kunshi shirinsu na tabbatar da gwamnati mai nagarta.

Takardar mai shafuka 80 na dauke da taken Renewed Hope 2023 – Action Plan for a better Nigeria wato “Sabunta Kyakyawar Fata a shekarar 2023 – Shirin aikin da zai inganta Najeriya,” wanda ya mayar da hankali kan manyan batutuwan da su ka shafi tattalin arzikin da gwamnatinsu za ta duba.

Har wa yau, an dangata sassan manufar da dama da Mr. Tinubu, inda dan takarar ya rika kurin nasarorin da ya yi a jihar Legas, inda ya kasance gwamna, daga 1999 zuwa 2007. Tinubu ya cigaba da yin alkawarin cewa zai sake amfani da salon shugabancin da ya yi amfani da shi wajen gyara jihar Legas wajen gyara Najeriya.

A shafi na 11, Mr Tinubu ya yi bayani dangane da mahimmancin noma ga tattalin arziki amma kuma ya nuna dauwa dangane da habakar da ake samu a adadin mutanen da ke zama a birane.

Dan takaran ya ce daga shekarar 1960, lokacin da Najeriya ta sami ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Burtaniya zuwa yanzu, yawan al’umma ya karu daga kashi 15 cikin 100 zuwa kashi 50 cikin 100. Mutane fiye da milliyan 100 ke zama a birane da garuruwa yanzu,” a cewar takardar.

Haka nan kuma a shafin na 226, dan takarar shugabancin kasar ya ce kasa da kashi 49 cikin 100 na al’ummar ke rayuwa a kauyuka, a yayin da kashi 32 cikin 100 na filayen noma ne kadai ake nomawa.

Dangane da yawan matasa, Mr. Tinubu ya ce matasa masu shekaru 15 zuwa 35 “su ne kashi 65 cikin 100 ko kuma fiye da milliyan 130 na al’ummar Najeriyar da ake kiyaci tana da yawan miliyan 200,” ya kuma kara da cewa yawan mutanen da ba su da aikin yi ya kai kashi 33 cikin 100

To amma yaya gaskiyar wadannan bayanan da ya yi? DUBAWA ta gudanar da bincike dangane da batutuwan da Mr. Tinubu ya yi bayani a kai.

“Lokacin da Najeriya ta sami ‘yancin kai, mazauna birni na zaman kashi 15 cikin 10 na yawan al’ummar kasar baki daya. A yau, yawan al’ummar da ke zama a birni ta wuce kashi 50 cikin 100. Fiye da mutane miliyan guda ke rayuwa a birane da garuruwa.”

Tantancewa

Al’ummar da ke zama a birni na nufin yawan wadanda ke rayuwa a birane kamar yadda hukumar kididdiga ta kasa ta kwatanta.  

A ajandar zaben 2023, Mr Tinubu ya ce kasa da kashi 15 cikin 100 na yawan al’ummar ke zama birni a lokacin da Najeriya ta sami ‘yancin kai. Ya ce wannan adadin ya karu da kashi 50 cikin 100 wanda ya kai adadin mutanen birnin zuwa miliyan 100.

Najeriya ta sami ‘yancin kai daga masu mulkin mallaka na Burtaniya a 1960. Bisa bayanan da mu ka samu daga Majalisar Dinkin Duniya wanda ke nuna yanayin biranen duniya, ‘yan Najeriyar da ke zama birane a shekarar 1960 na kan kashi 15.4 cikin 100.

Haka nan kuma, bayanai daga WOrld Population Review, wanda ke bitan yawan al’umma ya nuna cewa al’ummar Najeriya a wancan lokacin ya kasance miliyan 45, da jimilar mutane 6,955,837 su na zama a birane wanda ke zaman kashi  15.41% na al’ummar. 

Bayanai daga shafin Worldometer kuma na nuna cewa al’ummar kasar a 2022 na zaman miliyan 217, da kusan miliyan 107 a birane wanda ke zaman kashi 52 cikin 100 na al’ummar a shekarar 2020.

Bayanin cewa yawan al’ummar Najeriyar da ke zama a birane lokacin da ta sami ‘yancin kai ya kasance kashi 15 cikin 100 ba gaskiya ba ne.

Bayanin cewa al’ummar ta kasu da kashi 50 cikin 100 a yanzu haka gaskiya ne

Zargi na biyu: “Ko a yau, kalilan daga cikin adadin da ke zaman rabin kason al’ummar ne ke zama a kuayuka, wadanda kuma suke samun na sa wa a bakin salati daga kasar noman da su ke da shi, kuma ta haka ne su ma suke bayar da ta su gudunmawar wajen ciyar da al’umma. To sai dai kashi 35 cikin 100 ne kadai na filayen noman Najeriya ake iya nomawa.

Tantancewa

Fannoni hudu ne aka dunkule su waje guda suka zama fannin da ake kira fannin noma a Najeriya. Fannonin sun hada da fannin noma ko kuma girbin amfanin gona, dabbobi, gandun daji da kamun kifi. A watanni uku na biyu na shekarar 2022, Hukumar Kididdiga ta Kasa wato NBS ta ce gudunmawar fannin noma ga abin da kasa ke samu kowace shekara ta kasance kashi 21.90 cikin 100

Duk da irin damar da fannin ke da shi na bunkasa, fannin noma na fuskantar kalubale da ya musamman rashin tsaron da ya hana manoma zuwa gonakinsu. Sauran kalubalen sun hada da sauyin yanayi, rashin kudi da kuma karancin irin fasahar da noman zamani ke bukata.

Kamar yadda aka riga aka bayyana, kashi 52 cikin 100 na ‘yan Najeriya ne ke rayuwa a birane a yayin da sauran kason ke zaune a kauyuka. To sai dai ba duk wadanda ke zama a kauye ne su ke noma ba.

To amma gaskiya ne cewa kashi 35 cikin 100 na filayen noman kasar ne kadai ake amfani da su?

Najeriya na alfahari da manyan filayen noman da ta mallaka. Wani rahoton da statista ta fitar a 2019 ya nuna cewa Najeriya na kusan hekta miliyan 70.8 na kasar noma inda a cikin wannan adadi hekta 34 ne ake nomawa, miliyan 6.5 na cikin wadanda suke da amfanin gona na din-din-din sai kuma wani hekta miliyan 28.6 da ke karkashin makiyaya.

Wani kiyasin da aka yi a 2018 na nuna cewa wajen kashi 78 cikin 100 na filayen Najeriya ne ake amfani sa shi wajen noma a tare da wani kashi 37 cikin 100 na filayen da za’a iya nomawa.

A yayinda babu wadansu alkaluma na shekarar 2022 da ke nuna yawan filayen noman da ake da su a Najeriyar, a watan Satumban 2022 Dr Mohammed Abubakar ya bayyana cewa kashi 56 cikin 100 na filayen noman Najeriya ba’a amfani da su yadda ya kamata a yayin da ake amfani da wani kashi 44 cikin 100.

Babu isashen bayanin da ya goyi bayan batun cewa kashi 35 cikin 100 na filayen noman Najeriya ne ba’a amfani da su.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button