Taron koli na Bayanan Gaskiya a Afrika ko kuma Africa Facts Summit wanda kungiyar Africa Check ta shirya ya gudana Jami’ar Amurka na kasa da kasa ta Afirka da ke birnin Nairobi na kasar Kenya.
Taron na wuni biyu wanda ya hada masu binciken gaskiyar labarai da batutuwa, masu nazari da sauran kwararrun da ke aiki dangane da tantance gurbatattun bayanan da kan yaudari al’umma a ranakun 9 da 10 ga watan Nuwamba. A kwanakin biyu an shirya taron yadda zai tattauna batutuwan da suka shafi binciken gaskiya a lokacin zabe, sanya ido kan soshiyal mediya da sauransu.
Wakilan kamfanin Meta, wanda ya mallaki kafofin sada zumunta na Facebook, Instagram da Whatsapp sun gabatar da kasida dangane da yadda kamfanoni ke shawo kan matsalar yaduwar bayanai marasa gaskiya.
A wata sanarwar babban darektan kungiyar Africa Check Noko Makgato ya fitar ya ce an shirya taron ne wa masu binciken “su yi musayar ra’ayoyi, su kara wa juna sani wajen musayar dabarun da suka ga cewa sun fi kawo nasara a irin aikin da su ke yi dan samun hanyoyi da suka fi tasiri wajen yaki da matsalar gurbatattun bayanan da ake fama da su a nahiyar.
Taron ya zo daura da bukin cika shekaru goma da kafuwar kungiyar ta Africa Check kuma an gabatar da lambobin yabo ga wadanda ayyukansu suka yi fice.
An gabatar da lambobin yabon ga mutune a kowani rukunin da aka zaba wadanda suka hada da Dan jaridan da ya yi fice wajen binciken gaskiya, wanda ya yi fice wajen aikin tantance gaskiyar bayanai, da kuma dalibin da ke koyon aikin jarida kuma yi yi fice wahen tantance gaskiyar bayanai.
Dan jaridan da masu binciken kowanensu zai sami $3000 wadanda ke biye da su za su sami $1,500 kowa sai kuma a rukunin daluban na farko zai sami $2,000 a yayinda suaran kowane zai sami $1000