African LanguagesHausa

 Zaben 2023: Duk abin da ya kamata ku sani kan watsa sakamakon zabe kai-tsaye

A watan Fabrairun 2023 ‘yan Najeriya za su sake jefa kuri’ar da za ta zaban mu su sabbin shuwagabanni. Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC za ce a shirye ta ke kuma ta hakikance kan amfani da sabuwar hanyar zaben da aka gabatar kwanan nan mai suna BVA.

Lallai BVA ya kawo sauyi sosai a yadda ya shafi fasahohin da ake amfani da su wajen gudanar da zabe da ma watsa sakamako. Ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, ranar da za a yi zaben shugaban kasa ne zai kasance karon farko da za’a yi amfani da wannan fasaha a kasa baki daya bayan da aka yi amfani da ita a zabukan gwamnonin da aka yi a jihohin Osun da Ekiti.

Watsa sakamakon zabe Kai-Tsaye

Tun ba yau ba Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ke yunkurin sauya yadda ake gudanar da zabe daga yin shi yadda ake yi gwari-gwari da hannu zuwa amfani da sabbin fasahohin da ake da su. A yanzu haka zaben yana da matakai hudu: Na farko ya kunshi samar da kudin rajistar bayyanan duk wadanda su ka cancanci kada kuri’a, tantancesu ta yin amfani da fasahar tantance bayanan, kada kuri’a da fasahar da kuma watsa sakamakon kai tsaye.

Mataki na hudun, wanda shi ne watsa sakamakon zaben ya kunshi tura bayanai dangane da zaben daga wuri guda zuwa wuri guda ta yin amfani da yanar gizo dan tabbatar da cewa sakamakon na da nagarta kuma ya isa a kan kari.

Duk da cewa wasu sun dauki shafin da INEC ke bitar sakamakon zabe mai suna IReV, a matsayin abu daya ne da wanda ke watsa sakamakon kai tsaye, ba daya bane suna da banbanci duk da cewa akwai wasu wuraren da su ke da kama.

IReV ya kunshi wallafa kofin takardun da ke dauke da sakamkon wuraren zabe wadanda ake kira Form EC8A, wadanda da ma ake wallafa a kowani wurin zabe da suna Form EC60E. Alakaluman da a kan sanya a takardun ba dan sanar da sakamakon zabe illa dan jama’a su gani. Duk wanda ke da rajista a shafin INEC zai iya shiga ya ga wannan sakamakon a shafin na IReV

Yaya Ake Watsa Sakamakon?

A maimakon na’urar da ke karanta katin zabe na Card Reader da aka yi amfani da ita a baya, za’a rika amfani da fasahar BVA wadda za ta tantance masu zabe. Wannan fasaha za ta iya mafani da duk bayanai da aka dauka dangane da mutun wajen bayyana ko ya cancanci ya kada kuri’a.

Da zarar an kammala zabe an fara tara sakamakon kowani rumbun zabe, shugaban zai irga duka kuri’un – masu kyau da marasa kyau a gaban jama’a. Daga nan za’a rubuta sakamakon cikin takardar da ake kira Form EC60E. Bayan nan sai a dauki hoton form din a tura ofishin karamar hukumar inda za’a hada da wadanda za su shigo daga duk rumbunan zaben da ke karamar hukumar. Daga nan kuma sai a tura Jiha inda daga nan ne bayan an hada nan ko’ina za’a sanar da sakamakon karshe.

Rashin fahimtar da ake wa batun watsa sakamakon zaben kai tsaye

Yayin da hukumar zaben ke kawo sabbin dabaru na shawo kan matsaloli, ana cigaba da samun wasu karin matsalolin wadanda ka iya hadasa husumi tsakanin masu zabe, Dubawa ta gano wadansu daga cikinsu ta kuma yi karin bayani..

  1. Babu Zabe Ta Yanar Gizo-Gizo

Wadansu masu zabe suna ganin kamar sabuwar fasahar da aka kawo na nufin ba sai sun je rumbun zabe sun kada kuri’a ba, za su iya yi a gida. Har zuwa lokacin da muka buga wannan labarin hukumar zaben ta iya tsara yadda za ta tura sakamakon zabe kai-tsaye ne kawai a shafinta na IReV yadda masu sha’awar gani za su duba a kan lokaci amma ba wani a yi zabe a shafinta ba. Ko irin rajistar da a kan fara a shafin da aka fi sani da CVR, kashin farko ne kawai ake iya yi, sauran sai an je ofishin INEC. Dan haka ba za’a iya yin zabe daga gida a yanar gizo ba dole sai an je rumbun zabe.

  1. IReV dan ganin sakamako ne ba dan watsa sakamako ba

Shafin ganin sakamakon zabe na IReV an yi shi ne dan tara sakamakon zabe kadai. A shafin ana iya ganin takardun da ke dauke da alkaluman da aka samu daga duk rumbunan zaben kasar. Sai dai ba nan ne na karshe ba duk suna taimakawa ne wajen tara alakaluman da za’a bayyana a karshe.

  1. Rashin service/network mai kyau ba zai gurgunta shirin watsa sakamakon zaben ba

Ana ganin kamar wuraren da ba su da service sosai za su fiskanci matsalar tura sakamakon. Yadda tsarin ya ke daga an tura sakon zai tafi babu wata matsalar da za’a samu

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button