African LanguagesHausa

#Zaben 2023: Muhimman sauye-sauye a dokar zaben Najeriya

Yayin da ‘yan Najeriya da dama ki jiran zaben shugaban kasa wanda ake sa ran gudanarwa ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) da sauran masu ruwa da tsaki na cigaba da fama da alhinin zuwan ranar.

Daga farko an yi zaton za’a tafiyar da zabukan daidai kamar yadda aka gudanar da wadanda aka yi a baya sai dai kwaskwarimar da aka yi wa dokar zabe – wadda aka zartar da ita ta zama doka a shekarar 2022 – ta kawo wasu sabbin sauye-sauye a yanayin siyasar Najeriya. Dokar ta tayar da zaune tsaya har ma ta yi sanadin da wadansu ‘yan siyasa suka ajiye ayyukansu domin cimma burinsu na siyasa. Banda haka dokar ta  kuma kawo cigaba wajen gudanar da zabe cikin aminci da nagarta saboda sabbin kayayyakin aiki na zamani da aka kawo wadanda zasu taimaka wa tsarin zaben da ma yadda za’a tura sakamako.

Shugaban hukumar zaben, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bukaci duk ‘yan jam’iyya da su yi kokari su yi nazarin tanadin dokar. A wannan bayanin, DUBAWA ta mayar da hankali kan wasi daga cikin wadannan sauye-sauyen da dokar zaben ta kawo fagen siyasar Najeriya

  • Wa’adin yakin neman zabe

Jam’iyyun siyasa da ‘yan takara za su yi kaddamar da yakin neman zabe ne kadai kwanaki 150 kafin zaben sa’annan ya kamata ya kammala sa’o’i 24 kafin a fara zabe. Wannan na nufin cewa an haramta yakin neman zabe kusa da rumfunan jefa kuri’ar. Jam’iyyu na da isasshen lokacin da za su rinjaye jama’a kafin ranar zabe amma duk wani yunkuri na gudanar da kamfe a wajen da ake zabe ya sabawa dokar zaben na 2022.

  • Idan yawan kuri’u ya gota yawan mutanen da suka yi zabe

Idan har aka ga cewa yawan kuri’un da aka irga ya wuce na yawan mutane da suka yi zabe a rumfar zabe, za’a soke sakamakon ne kai tsaye a duba. Yanzu da akwai na’urori irinsu BVN, shugaban zabe a rumfar zai iya tantance sunayen wadanda suka yi rajista kafin a tura sakamakon. Wannan babban cigaba ne daga tanadin da ake da shi a tsohuwar dokar, Inda daga zarar kuri’un sun wuce adadin wadanda suka yi rajista sai a soke sakamakon baki daya. 

  • Cibiyar bayanan masu jefa kuri’a

A tsohuwar dokar, sunayen wadanda suka yi rajista a kan rubuta ne a cikin takardun da ake ajiyewa a Hedikwatar ko kuma ofisosin hukumar zaben da ke yankuna. To amma wannan sabuwar dokar ta yi amfani da sabbin fasahohi ta hanyar bayar da cibiyar bayanai inda sunayen duk wadanda suka yi rajista zai shiga. Va’a yi watsi da salon ajiye takardun ba amma wadanda ake ajiyewa a cikin komfutar ta fi saukin samu daga ko’ina a kasar.

  • Tsarin zabe mai amfani da fasaha

Idan ana batun cigaba na fasaha, sabuwar dokar ta tanadi amfani da na’urorin zamani wadanda suka hada da na’urorin da ke karanta bayanan kan katin masu zabe, na’urorin zabe masu kwakwalwa da suaran na’urori na fasaha wajen tantance masu zabe. Haka nan kuma ana iya tura sakamakon ko’ina ko sadda ake zaben ko bayan an gama ta 

  • Kudaden  INEC 

Bayan da aka samar da Hukumar Zabe mai zaman kanta duk wani kudi da take bukata wajibi ne a bata akalla shekara guda kafin zabukan. Za’a sami wadannan kudaden ne daga tanadin da gwamnatin tarayya ta yi na bayar da tallafa da wadansu gudunmawar daga waje. Bayan haka, dokar ta tanadi baiwa hukumar  ikon cin gashin kanta a fannin kudi abun da ke nufin cewa hukumar na iya karbar kudi kai tsaye daga kungiyoyin da ke daukar nauyin zaben, ba kamar dokar da ba inda duk wani kudi da za’a ba ta sai an sami amincewar ma’aikatar kudi.

  • Zaben fid da gwani a kan kari

Jam’iyyun siyasa da ‘yantakarar kowane mukami dole su gudanar da zaben fid da gwani su kuma baiwa hukumar sunan gwanin da suka zaba akalla kwanaki 180 kafin zaben. Bisa tanadin sabuwar dokar, wanda ya banbanta da toshuwar dokarmai cewa ‘yan takara na iya jira har sai kwanaki 60 kafin zaben sa’annan su tura sunayensu.

  • Masu rike da mukaman gwamnatin da ke so su tsaya takara

Kafin wani wanda kerike da mukamin gwamnati ya cancanci tsayawa takara ko wakili a zabe, dole ne ya/ta yi murabus daga mukamin gwamnatin da yake/take rike da shi. Wannan nasashi na 84(12) na sabuwar dokar. To sai dai wannan na daga cikin batutuwa mafi sarkakiya -duk da cewa ya sami karbuwa sosai –  a cikin dokar saboda ya hana ‘yan siyasa rike mukaman gwamnati na wani tsawon lokaci da ma dai damar samun mukaman gwamnati yadda suke so ba tare da ba saura suma sun dana ba. 

  • Mutuwar dan/’yar takara

Mutuwar wanda/wadda ke takara kafin a sanar da sakamko na daya daga cikin abubuwan da aka duba saboda ya kasance daya daga cikin batutuwa masu sarkakiya a tsohuwar dokar. Sabuwar dokar ta ce idan haka ya faru, za’a dage zaben a sake shirya gudanar da shi bayan kwanaki 14 idan dan takarar ya rasu kafin a fara zaben. A waje guda kuma, idan dan takarar ya mutu bayan zabe kafin a sanar da wanda ya yi nasara, za’a dakatar da zaben na kwanaki 21 ba kari.

Idan hakan ya faru ga wanda ke takarar neman kujerar majalisa ne, za’a yi sabon zabe. Daura da haka, jam’iyyar da abun ya shafa dole sai ta sake yin zaben fid da gwani, ta kuma gabatar da sunayen sabbin ‘yan takaran ga hukumar zabe akalla kwanaki 14 da rasuwar dan takarar. A zabe na mukaman da ke mataki na zartarwa ko kuma kananan hukumomin da ke birnin tarayya, abokin takarar zai maye gurbin dan takaran da ya rasu, sai jam’iyya ta sake  zaben wanda zai tsaya takarar da shi/ita

Bayanan kwararru

Caleb Ijioma, wani dan jarida wanda ya sanya ido a zabuka da dama ya yaba da wannan sabuwar dokar saboda irin mahimman sauye-sauyen da ta kawo ga tsarin zabe a Najeriya.

Ya yi imanin cewa dokar za ta tabbatar da adalci a zaben. “Yanzu za’a iya tilastawa ‘yan siyasa da hukumar zabe su tabbatar da cewa an kamanta adalci sa’anan an yi zaben cikin walwala,” ya ce. 

“Daya daga cikin sauye-sauye mafi mahimmanci ita ce naurorin zabe da tura sakamako kamar yadda aka bayyana a sassan  47  da 59 (2). Kai tsaye za’a rika ganin sakamako da zarar aka tura su zuwa cibiyar bayanan INEC.”

“Haka nan kuma sashi na 51 ya sake gyara ma’anar samun sakamakon zaben da ya nuna adadin masu rajista bai kai yawan kuri’un da aka jefa ba, kuma wannan ya karawa masu zabe karfin gwiwa.”

Mr Ijioma ya bayyana cewa zabukan da aka yi daga baya-bayan nan sun gyaru sosai, kuma wannan ya fara kawo “daidaito a lamuran da suka shafi siyasarmu.”

Ya ce, “Zabukan da aka yi bayan da aka zartar da sabuwar dokar zabe sun fi wadanda aka yi a shekarun baya inganci. Wannan dokar ta kara kawo gaskiya a tsarin zabe. Yanzu masu zabe ba sai sun jira na wani tsawon lokaci kafin su sami sakamakon zabe ba.”

Austin Aigbe, wani babban jami’i a ofishin Cibiyar tabbatar da Cigaban Dimokiradiyya ta CDD, ya kara fayyace wasu daga cikin abubuwan da dokar zaben ta kawo.

Ya bayyana cewa tsarin BVAS wanda ke amfani da yatsu da wasu siffofin jiki wajen ganewa da banbanta jama’a, wanda dokar ta amince da shi ya kawo wani abun da aka rasa a zaben 2019 inda har ma masu zabe kan iya sa hannu kan wata ‘yar takarda idan katinsu ya sami matsala.

Ya ce, “da zaben 2023 da dokar zaben 2022, babu amfanin na’urorin smart card readers wato masu karanta bayanan da ke jikin katin masu zabe. Kuma mun ma wuce matakin tantance zanen yatsu. Yanzu ana iya sanin abin da ake kira tantance siffofin fuska. Idan har ba’a iya daukar hoton yatsu bam ana iya amfani da sifar fuskar mutun.”

Mr Aigbe ya kuma sake yabawa da shafin da aka kaddamar na bayyana sakamako, inda za’a iya ganin sakamako kai tsaye duk a dalilin na’urorin da dokar zaben ta amince da su. Shi ya sa ma ya kwatanta wannan matakin a matsayin wata hujja ce da ta nuna cewa hukumar zaben ta dauki nauyin da ya rataya a kanta, na gudanar da zabe cikin adalci, da gaske.

“Lallai hukamar INEC ta kara matakin bayyana gaskiya. Da zarar rumfunan zabe suka bayyana sakamakonsu, za’a dauki bayanan ta yin amfani da BVA ta yadda duk masu zabe za su gani. Wadanda suka jefa kuri’unsu za su iya rubuta sakamakon ta yadda anjima bayan an sanya sakamakon a intanet kowa zai iya zuwa ya duba ya gwada ya gani ko an wallafa daidai. Ta haka duk wanda ya ga cewa akwai sabani tsakanin wanda ya dauko daga rumfar zabe da wanda ke cikin intanet zai iya jan hankalin jama’a a san abun da za’a yi nan take.”

A Karshe

Yanayin fahimta da fadakarwa gabanin zaben 2023 ya faru nuna sabon sauyi a Najeriya. To sai dai ana bukatar aiki sosai dangane da ilimantar da masu zabe musamman a yankunan karkara, domin su fahimci tanadin dokar zabe da yadda aka gina ta a cikin kundin tsarin mulkin kasar. Fadakar da jama’a dangane da dokar yana da mahimmanci ga gudanar da zabe mai bayyana gaskiya da kuma daukaka muhimman hakkokin bil adama.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button