Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook yayi da’awar cewa Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kashe ‘yan arewa mafi yawa mafi yawa a cikin kwanaki uku a arewacin kasar sama da abin da ‘yanta’adda suka kashe a watanni uku da suka gabata.

Hukunci: YAUDARA CE. Duk da cewa jami’an tsaro an zarge su da kashe mutane a kwanaki ukun farko na zanga-zangar basu kai mutum goma ba idan aka kwatanta da mutane 51 da aka kashe a harin kunar bakin wake.
Cikakken Sako
Wani mai amfani da shafin Facebook mai suna I Sign Against Corruption, ya wallafa wani bidiyo (shared) inda yayi da’awar cewa jami’an tsaro a Najeriya sun kashe ‘yanarewa da dama cikin kwanaki ukun farko na zanga-zangar tsadar rayuwa #EndBadGovernance fiye ma da abin da ma
yakan Boko Haram suka kashe a watanni uku da suka gabata.”
Tsokaci guda 38 da wadanda suka sake wallafa da’awar tasa su 154 ya jawo kalamai na kyama ga gwamnati, sai dai akwai wasu kamalansu suna tantama kan abin da ake fadi.
Wannan ne ma ya sanya DUBAWA shiga aikin bincike kan wannan da’awa.
Tantancewa
DUBAWA ya fahimci cewa watanni uku da ake magana a kansu sune Mayu da Yuni da Yuli, ta hanyar amfani da binciken kalmomi mun gano hare-haren da ‘yanta’addar suka kai cikin wannan lokaci. Na farko da aka fara ganowa tun bayan 2019 shine na ‘yanmata uku da suka kai harin kunar baki (suicide bombing) a garin Gwoza a jihar Borno a ranar 29 ga watan Yuni, wadanda aka nufi wurin daurin aure da asibiti da jana’iza.
Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya nunar (revealed) da cewa wadanda abin ya shafa akwai wadanda suka sami raunika sun haura 100, wadanda suka rasu kuma sun tashi daga 18 zuwa 32 ya zuwa ranar 1 ga Yuli,2024. Wata guda bayan wannan jihar ta sake samun kai harin kunar bakin wake (suicide bombing) a kauyen Kawuri a karamar hukumar Konduga a ranar 31 ga watan Yuli,2024, a wannan hari an rasa rayuka 19 da fararen hula da dama da suka sami raunika. Wannan ya sanya adadin wadanda suka rasun a wannan tsakani suka kai 51.
Adadin mutane da suka rasu a zanga-zangar tsadar rayuwa ta #EndBadGovernance ta jawo cece-ku-ce kasancewar wadanda jami’an ‘yansanda suka ce sun rasu 7 ne, abin da ya ci karo contradicted da adadin kungiyar Amnesty International, da ta ce an kashe masu zanga-zanga 13 ya zuwa ranar 3 ga watan Agusta,2024.
DUBAWA yayi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Najeriya Muyiwa Adejobi kan hakikanin adadin, sai dai har zuwa 5 ga Agusta, 2024 babu abin da aka ji daga bangaren jami’an.
Karshe
Ko da yake an samu mutamne da suka rasu yayin zanga-zangar a arewacin Najeriya yawan adadin bai haure na ‘yanta’adda ba a watanni watanni uku, don haka da’awar da aka yi yaudara ce.