Zargi: Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki Bola Tinubu ya ce fannin ma’adinan da ke karkashin kasa kawo yanzu gudnmawar shi ga abin da kasa ke samu kowace shekara a Najeriya bai kai kashi daya cikin 100 ba.
Da gaske ne
Cikakken bayani
Ranar alhamis 10 ga watan Nuwamba Bola Tinubu dan takarar kujerar shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar APC ya yi zargin cewa fannin ma’adinan da ke karkashin kasa kawo yanzu gudnmawar shi ga abin da kasa ke samu kowace shekara a Najeriya bai kai kashi daya cikin 100 ba.
Tinubu ya yi wannan bayanin lokacin da ya ke jawabi a taron babban zauren mahawarar gabanin zabe, tare da masu ruwa da tsaki a fannonin ma’adinai da sarrafa kayayyakin gona a Lafiya, jihar Nassarawa.
Lokacin taron, dan takaran ya nuna takaicinsa dangane da yadda Najeriya ke da arziki da kuma al’umma mai hazaka da kuzari ga kuma kasar noma ruwa, da ma sauran ma’adinai.
A nan ne ya ce fannin ma’adinan kasa da kashi daya cikin 100 ne kadai ke shiga abin da kasa ke samu kowace shekara wato GDP.
Bisa bayanan hukumar kididdiga ta ksa NBS, ana iya samun GDP ne idan aka hada darajar abin da kasa ke samu daga kayayyaki da ma ayyukan da take yi dan samun abin da za’a yi amfani da shi a kasar da wanda za’a fitar.
Lokacin yakin neman zabe, ‘yan siyasa sun saba amfani da alkaluma dan jan ra’ayin jama’a kuma yana da mahimmanci a rika tabbatar da gaskiyar abin da su ke cewa, shi ya sa muka ga ya dace a tantance wannan batun
Tantancewa
Mun fara binciken da duba yawan ma’adinan karkashin kasar da aka samu a Najeriya, akalla a cikin shekarar 2021.
Na farko, mun nemi shaida daga rahoton ma’adinai na shekarar 2021 daga Hukumar Kididdiga ta Kasa inda mu ka ga cewa a ma’adinai baki daya a karshen 2021 an sami 89,482,541.07, wanda ya nuna an sami kari na kashi 39.19 cikin 100 daga 2020 wanda ya tsaya a kan ton miliyan 64.29
Rahoton wanda ya fito a watan Yulin 2022 ya kara da cewa ma’adinai irinsu farar kasa, Granite da laterite su ne aka fi haka a cikin shekarar 2021.
Mene ne darajar wannan idan aka juya shi zuwa kudi? Nawa ne baki daya kudin da za’a samu har a hada a cikin jimilar kudin da kasa ke samu kowace shekara?
Domin amsa wadannan tambayoyin mun cigaba da nemo wasu karin hujjojin.
Bisa bayanan NEITI rahoton bitar da aka wallafa a 2020 (Ana kan jiran na 2021) GDPn Najeriya ya kasance Nera triliyan 152.32 a shekarar 2020 kuma gudunmawar fannin ma’adinai na zaman Nera biyiyan 686.64 wanda gaba daya ya kama kashi 0.45 cikin 100
A 2021 a cear bayanan Bankin Duniya da kuma nazarin da Trading Economics su ka yi, GDPn Najeriya ya karu da billiyan 440.78 na dalar Amurka abin da ya kai Nera triliyan 173.5 amma kuma baki daya idan aka kwatanta da tattalin arzikin duniya wannan na zaman kashi 0.05 cikin 100 ne kacal.
Bacin wannan karin da aka samu, rahoton tattalin arzikin da Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar a kwata na uku na shekarar 2021 ta tabbatar da cewa fannin ma’adinan ne bai tabuka komai ba wajen bunkasa inda ya sami dalan Amurka 0.01 wanda ke zaman Nera 4.4
To ko mene ne darajar wannan adadi da CBN ta bayar?
Dataphyte, wadanda su ka yi nazarin rahoton Hukumar Kididdiga ta Kasa sun nuna cewa gudunmawar fannin ma’adinan ga abin da kasa ke samu kowace shekara ya karu daga biliyan 368.9 a 2019 zuwa triliyan 1.101 a 2021. Wannan na nufin gudunmawar fannin ga GDP ya ma kari ne daga kashi 0.26 cikin 100 zuwa 0.45 cikin 100 a 2020.
A 2021 duk da an hako ton 89,482,541.07 gudunmawa ga GDPn kasar wanda ya tsaya kan dalan Amurka biliyan 440.78 wada ke zaman triliyan 173.5 a nera ya kasance kashi 0.63 cikin 100 ne kacal
A watan Maris 2022, babban sakatare/ CEO na NEITI Dr Ogbonnaya Orji, shi ma ya tabbatar da cewa fannin ma’adinan Najeriya ba ya taka rawar gani domin gudunmawarsa ga GDP bai kai kashi daya cikin 100 ba, duk da cewa ya tashi daga kashi 0.18 cikin 100 a 2018, zuwa 0.29 cikin 100 a 2019
A Karshe
Bisa bayanan da muka samu daga majiyoyi daban-daban zargin Bola Tinubu na cewa fannin ma’adinai na bayar da kasa da kashi guda cikin 100 a jimilar abin da kasa ke samu kowace shekara gaskiya ne