African LanguagesHausa

Yadda Wadansu Shafukan Twitter da Facebook suka wallafa hotunan bogi dan yi wa dan takarar shugabancin Najeriya Kamfe.

Zargi: Wani bidiyon da ya gama ko’ina a soshiyal mediya ya gwado wasu taurarin kasa da kasa na Hollywood rike da kasidun da ke goyon bayan dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Leba, Peter Obi

<strong>Yadda Wadansu Shafukan Twitter da Facebook suka wallafa hotunan bogi dan yi wa dan takarar shugabancin Najeriya Kamfe.</strong>

An gyara wannan bidiyon ne. An yi amfani da manhajar da a kan yi amfani da ita wajen cire abin da ake so daga ainihin bidiyon dan a gyara sautin maganar da ke kai a sanya labarin da ba daidai ba a yaudari jama’a. ‘Yan wasan wannan bidiyon ba su yi wa Peter Obi bidiyo ba.

Cikakken bayani

Bidiyon ya fara ne da Idris Elba sananan dan fina-finan nan dan asalin Burtaniya yana dariya tare da Matthew McConaughey- mai shekaru 53 na haihuwa shi ma dan fim, ba’amurke yana rike da wata takarda da ke cewa “A, ya yi ma’ana. Ku zabi Peter Obi a 2023.”

Na tsawon minti 1 da dakiku 53 a bidiyon manyan ‘yan Hollywood din ne suka cigaba da bayyana, irin su Tom Cruise, Doug Liman, Gerard Butler da 50 cent duk rike da wannan kasaidar mai goyon bayan Peter OBi.

Yayin da ‘yan Najeriya ke tinkarar zabukan shugaban kasa ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, bidiyon jiga-jigan fina-finai a matakin kasa da kasa suna marawa Peter obi – Wanda ke takara a karkashin inuwar jam’iyyar Leba – baya dole zai tayar da hankalin jama’a tun da ya nuna cewa jam’iyyar na samun goyon baya a matakin kasa da kasa kuma ana mata kallon jam’iyyar da za ta baiwa kowa mamaki.

To sai dai yanayin kasidar ta sanya alamar tambaya. Bacin haka, ba’a bar taurarin fina-finan sun yi magana ba illa dai wani sautin da aka sanya, wanda ya nuna cewa an an yi amfani da bidiyon ne kawai a yada labari na bogi.

Sai dai mutane biyu masu kima a idon jama’a ne suka wallafa bidiyon a shafukansu wadanda aka tantance da alamar nagarta kuma suna da mabiya da yawa kuma shafukan na dauke da bayanan da ke nuna jam’iyyar da suke marawa baya.

Charles Oputa wanda aka fi sani da Charly Boy yana da mutane 247,000 da ke bin shafin shi na Tiwita. Da ya sanya bidiyon ranar 21 ga watan Nuwamba, mutane 1,222 suka yi tsokaci a kai wasu 7,082 su ka sake rabawa da na su abokan sa’annan wasu 14,800 kuma su ka yi ma’amala da bidiyon.

Mawakin ya kuma yi tsokaci tare da bidiyon da ya wallafa inda ya ce: “Abin sha’awa, yakin neman zaben Peter Obi ya shiga matakin kasa da kasa, da taurarin talbijin a Amurka da ma ‘yan fim a Hollywood suna jagora.”

Mike Asukwo shahararren mai zane-zane irin na barkwanci, shi ma a sanya bidiyon a shafin sa yana cewa “Ina so ne kawai in sake yin alfahari da dan uwa na.” A lokacin da muka rubuta wannan labarin, mutane sama da 5,600 sun kalli bidiyon, an tsokaci kusan 171 kuma shafuka 515 sun sake raba labarin.

Shafin wani mai suna Lu Benson ya yi addu’a cikin harshen Pidgin ya na bukatar mafarkin (nasarar Peter Obi) ya zama gaskiya saboda ‘yan Najeriya sun jimre da yawa.

Ya ce: Allah na roke Ka ka mayar da wannan mafarkin gaskiya. Mun wahala sosai mana.

Wani shafin mai suna Awele Ideal, na wata ce wadda bidiyon ne ya ba ta sha’awa kuma ta bukaci da a tura mata.

Bidiyon ya cigaba da jan hankalin jama’a har ma a manhajar tiktok. Wani shafi mai suna @@sheks_bibi shi ma ya wallafa bidiyon tare da taken “Peter Obi shugaban kasa 2023 #peterobi #2023election #vote.”

Irin sharhin da jama’a suka rika yi a karkashin bidiyon ya nuna cewa mutane da yawa sun yarda da abin da bidiyon ke fada, dan haka DUBAWA ta yanke hukuncin binciken gaskiyar wannan labari.

Gaskiyar Labarin

DUBAWA ta fara da suba bidiyon inda ta gano ainihin adireshin da aka wallafa bidiyon a shafin YouTube. Wata mai suna Eva Luca ce ta wallafa kwafin bidiyon watanni ukun da suka gabata. Sai dai akwai banbanci a abin da ke rubuce kan kasidar da suka rije. Ainihin abin da ke kan kasidar umurni ne na yadda za’a iya amfani da bidiyon inda aka ce “Bayani, hoto ko kuma tambarinku a nan” wanda ke nufin ana iya editing a sa duk abin da ake so a kai.

‘Yan fim kusan 39 aka sanya a bididyin wanda aka fara wallafawa ranar 23 ga watan Yuli abin da ya kunshi abubuwan da aka riga aka bayyana. Bidiyon ya kuma kara da bayar da bayani dalla-dalla na yadda za’a iya gyara hoton a sanya abin da ake so a sanya.

Duk yunkurinmu na gano manhajar da aka yi amfani da ita dan gyara bidiyon ya ci tura duk da cewa akwai manhajoji da dama wadanda za’a iya amfani da su wajen yin hakan.

Inda bidiyoyin su ka fito

DUBAWa ta gano bidiyoyin daban-daban a tsarinsu na asali, dukkaninsu na gan wata tashar YouTube mai suna WIRED wata kasidar Amurka “wadda ke fayyace yadda fasaha ke tasiri kan kowane bangare na rayuwa -kama daga al’ada, kasuwanci, kimiya zuwa zane,” bisa bayanan da aka sanya a shafin kamfanin.

Tashar na gabatar da wani shiri mai suna Autocomplete Interview inda ake kawo masu nishadantarwa a Amurka su bayar da amsoshi ga tambayoyin da ma’abotansu masu amfani da manhajojin binciken intanet su ka fi bida a kansu.

Domin kwatance mun dauki hoton Terry Crews wani sanannan dan fim kuma mai gabatar da shirye-shirye a talbijin a Amurka daga bidiyoyi ukun da aka yi wato daya daga ainihin tashar ta WiRED, daya daga shafin Eva Luca wadda ta bayyana yadda za’a iya amfani da bidiyon, sai kuma wanda aka sauya aka sanya batun kamfe din Peter Obi.

A Karshe

Bidiyoyin bacin yadda masu fada a ji ne suka wallafa shi a shafukansu, gyara bidiyon aka yi domin samun damar baza labaran bogi. ‘Yan fim da ke cikin ainihin bidiyon farko ba su nuna goyon bayansu ga Peter Obi ba.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »