African LanguagesHausa

Zargin wai daya daga cikin yaran shugaban kungiyar ASUU ta kammala jami’a a Amurka ba gaskiya ba ne

Zargi: Wani mai amfani da shafin Facebook na zargi wai diyar Emmanuel Osodeke, shugaban kungiyar ASUU ta kammala makaranta kwanan nan daga jami’ar Chicago da ke Amurka.

Zargin wai daya daga cikin yaran shugaban kungiyar ASUU ta kammala jami'a a Amurka ba gaskiya ba ne

Mr Osodeke da kansa ya fadawa DUBAWA cewa ba shi ma da ‘ya na mace bare har a ce ta kammala jamai’a. Da muka kara bincike kuma mun gano cewa yawancin hotunan da aka yi amfani da su a labarin, an dauko su ne daga wurare daban-daban aka kaga labarin

Cikakken bayani

Yayin da ake cigaba da tattaunawa dangane da yajin aikin da kungiyar ASUU ta dukufa tana yi, wata mai amfani da shafin Facebook mai sunan Ekiti Princess ta wallafa wadansu hotuna tana zargin wai diyar shugaban kungiyar ASUU ce a bukin kammala makarantarta na jami’a a jami’ar Chicago.

Labarin wanda mutane da yawa suka rika sake rabawa da abokansu a shafukan sada zumuntar na zagin shugaban ASUUn ne a fakaice da sunan taya shi murnar cewa ‘yarsa ta kammala jami’a alahli kuma gatse ne ake mi shi a kan cewa hakan ya faru yayin da dubban yaran talakawa ke zaune a gida ba makaranta.

Labarin na dauke da hoton wata yarinya cikin rigunan bukin kammala makaranta tsakanin wadanda ba ‘yan Najeriya ba, sa’anan shi kan sa Mr Osodeke na cikin hoton.

Hoton na dauke da bayanin da ya kwatanta wadanda ke cikin hoton kamar haka: Wannan ita ce Juliana Chidera Victor Osodeke, diyar Emmanuel Osodeke mai shekaru 21 na haihuwa wadda kwanan nan ta kammala makaranta daga jami’ar Chicago da ke jihar Illinois a Amurka.

Wannan labaro dao ya tayar da mahawara tsakanin masu amfani da shafin, wato da wadanda ke ganin ke ganin bakin Mr Osodeke da kuma wadanda ke shakkun sahihancin labarin. Shi ya sa DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiyar batun.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da tuntubar Mr Osodeke ta wayar tarho kuma kai tsaye ya karyata wannan zargin yana mai cewa:

“Ba ni da ‘ya mace. Dan haka dan me za’a ce ‘yata ta kammala makaranta bayan ba ni da wata ‘ya ba mace? Ta yaya zan iya biyan kudin makrantar milliyan 10 da albashi na nera dubu dari hudu kowani wata? Kun gani wadannan duk dabaru ne da gwamnati ke amfani da wasu wajen hadasa husumi a maimakon samar da maslaha ga matsalar da ake fuskanta. Wannan abin tausayi ne,” a cewarsa.

Rediyon BBC Pidgin ta ba da tabbacin hakan a wani labarin da ta wallafa a shekarar 2021.

Baya ga haka mun dauki hotunan da aka wallafa mun sanya cikin manhajar tantance hotuna. Bayan da mu ka kammala, sakamkaon ya nuna mana cewa hoton farko ya fara bulla a duniyar soshiyal mediya ne a shekarar 2014 a shafin My School Gist inda shafin ke yabawa Anita Osariemen Omonuwa bayan da ta kasance mace mai bakar fata na farko da ta kammala jami’ar Reading a Burtaniya da sakamako mai kyaun gaske.”

Hoto na biyu kuma ya yi mafari ne daga wani shafin da ya kwatanta daliban da ke cikin hoton a matsayin rukunin daliban farko na wadanda su ka kammala karatun digiri na biyu albarkacin tallafin da su ka samu daga gidauniyar tsohon shugaban Amurka Barack Obama, tsakanin shekarar 2018 zuwa 2019, daga Harris Schoool of Public Policy wato Makarantar koyon Manufofin Gwamnati ta Harris da ke jami’ar Chicago

Duk da cewa mun ga hoton Mr Osodeke a cikin hotunan da aka wallafa, bincikenmu bai nuna mana wani abu takamaimai ba. Dan haka  sai mu ka sake dubawa, a nan ne muka gano cewa an manna hoton shugaban ASUUn ne cikin wani hoton bukin kammala karatun da aka yi kwanan nan a jami’ar ta Chicago a jihar Illinois, Amurka.

Yayin da muke binciken wannan zargin Ekiti Princess wadda ta fara yada labarin a Facebook ta sake yin wani tsokaci kan labarin da ya tabbatar mana cewa batun ba gaskiya ba ne.

Ta ce: “Kun ga yadda mutane da yawa suka dauki wannan batun a matsayin labarin gaske. Idan dai har wannan labarin karya ne ina baiwa ‘yan Najeriya hakuri.

“Amma ina rokon gwamnati da ta yi wani abu dangane da wannan yajin aikin da ake fama da shi, bari Allah ya cigaba da taimaka mana a wannan kasar.

“Ina neman gafararku ‘yan Najeriya.”

A Karshe

Bacin binciken da mu ka yi da ya nuna mana cewa an dauko hotunan ne daga shafuka daban-daban aka kaga labarin, mun kuma yi waya da shugaban kungiyar ta ASUU wanda ya fadawa DUBAWA karara cewa ba shi ma da ‘ya na mace daga cikinsa. Dan haka zargin wai ‘yarsa ta kammala makaranta a Turai ba gaskiya ba ne

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button