Zargi: An wallafa wani bidiyo na sarauniya Elizabeth na biyu mai rasuwa tana jefa wa wasu kananan yara wadanda ake zargi ‘yan Afirka ne abinci a kasa.
Bincikenmu ya nuna mana cewa matar da ke cikin hoton ba sarauniya Elizabeth na biyu ba ce kuma kananan yaran ba ‘yan Afirka ba ne. Don haka wannan zargin ba gaskiya ba ne
Cikakken bayani
Rasuwar sarauniyar Ingila ya janyo martanoni kyawawa da marasa dadi daga mutane a duk fadin duniya.
Ta kasance sarauniyar Burtaniya daga ranar 6 ga watan Fabrairun 1952 har zuwa rasuwarta a ranar 8 ga watan Satumban 2022. Wuni guda bayan da aka sanar da rasuwarta wani bidiyon da wani mai suna Kelly Muwana ya raba har wata Egemba Uzoamaka ta sake rabawa mai taken “Mun yafe amma ba mu manta ba” ya nuna wasu mata biyu wadanda ke sanye da fararen riguna suna jefawa yara abinci a kasa a yayin da su kuma yaran ke kokuwar dauka.
Wannan bidiyon ya harzuka jama’a sosai inda a wajen yin sharhi ko tsokaci, wasu har suna cewa dama ba su gani ba.
Cynthia Anyanwu ta rubuta: Da ma ban ga wannan ba, ina matukar bakin ciki,” yayin da Obianuju ita kuma ta rubuta “ashe shi ya sa wadansu mutane su ke fushi.”
Shi kuwa Prince Okoye a waje guda cewa ya yi …..duk da haka mun yafe. Allah ya kiyaye hanya. Amma ta yaya zan gayyaci wannan bidiyon.
Sharhin da Kelly Muwana ya yi sadda ya wallafa bidiyon ya ce “Sarauniya mai rasuwa da kakanninmu.”
Wasu ne suka bukaci da mu tantance gaskiyar wannan batun, amma bacin haka mu kan mu muna so mu gano gaskiya saboda irin matsalar da labarai irin wannan ka iya janyowa.
Tantancewa:
Da muka yi binciken mahimman kalmomi mun ga cewa bidiyon ya yi yawo sosai cikin manhajojin YouTube, TikTok da taskokin blogs da ma sauran dandalolin sada zumunta na soshiyal mediya.
Bayan nan mun tantance hoton cikin manhajojin gano asalin hotuna da bidiyoyi inda mu ka gano an yi amfani da bidiyon a suffofi daban-daban. Ga bayani kadan daga cikin wadanda mu ka gano.
Wani bidiyo mai tsawon minti 43 wanda shafin Cool Facts su ka wallafa a YouTubu shekaru uku da suka gabata ya bayyana cewa bidiyon da wani kamfanin fina-finai na Lumiere Brothers ya dauka na wata mata ‘yar asalin Faransa ce wadda ke jefawa kananan yara abinci a yankin Indochina
A yayin da wani kuma wanda aka wallafa bara mai suna Olden Days ya nuna cewa wannan ya afku a shekarun farko na 1900 lokacin da kasar Vietnam ke karkashin jagorancin Faransa.
Bisa bayanain da ke cikin Olden Days wani mai suna Gabriel Veyre ne ya dauki hoton diyar gwamnan wani yankin Vietnam da matarsa suna jefawa kananan yara sulallu.
Shafin Histroy Upscaled wani shafin tarihi shi ma ya wallafa wannan labarin kamar yadda aka gani a bayanin Olden Days. Bidiyon ba shi da wani sauti illa muryoyin yaranya yayin da su ke rububin kwashe sulallan da ake jefa mu su.
Sigar farko na bidiyon ya bulla ne shekaru 10 da su ka gabata kamar yadda ativinnumotmaelandi suka gano, wanda kuma aka yi wa taken “Matan yankin Indochina su na jefawa mata shinkafa.”
Mun kuma gano binciken da aka yi na tantance gaskiyar batun a shafukan binciken gaskiya na Altnews da Politifact wadanda su ma suka karyata wannan zargin.
A Karshe
Bincikenmu ya nuna cewa matan da ake zargi tana jefawa kananan yara abinci a bidiyon da ke yawa ba sarauniya Elizabeth na biyu ba ce. Ainihin bidiyon inda aka samo wannan banganren da ake yawo da shi ya nuna cewa abin ya faru ne a yankin da ake kira Indochina a baya, lokacin da yankin ke karkashin mulkin Faransa, wanda kuma a zamanin yanzu aka fi sani da kasar Vietnam a yankin kudu maso gabashin Asiya