African LanguagesHausa

Zargin wai ganyen “brocoli” na warkar da cutar dajin mama ba gaskiya ba ne

Zargi: Wani labari da ke yawo a WhatsApp na zargin wai cin ganyen brocoli na iya warkar da cutar dajin mama

<strong>Zargin wai ganyen “brocoli” na warkar da cutar dajin mama ba gaskiya ba ne</strong>

Yayin da gaskiya ne sinadarin da aka fi sani da Sulforaphane (SFN), wanda ake samu daga ganyen broccoli, na iya kare mutun daga kamuwa da cutar daji, har yanzu ana gudanar da bincike kansa ba’a riga an gane irin tasirin da ya ke da shi a kan cutar ba.

Cikakken bayani

Cutar daji na mama ita ce nau’in cutar da ta fi kamari a tsakanin mata kuma a ‘yan kwanakin nan, wani sakon da ke ta yawo a whatsApp na zargin wai cin ganyen brocolin zai iya warkar da cutar.

Sakon ya kunshi adireshin wani shafi mai suna global excellence wanda ke dauke da wadansu karin bayanai dangane da yadda brocolin ke warkar da wasu karin nau’o’in cutar ta daji. Tantance ko wannan kayan lambin na iya warkar da cutar na da mahimmanci domin a wayar da kan jama’a.

Tantancewa

Broccoli kayan lambu ne daga dangin ganyayyakin da ake shukawa dan abinci wadanda ake kira cruciferous a turance, wadannan sun hada da kabeji, da kabeji mai fure da sauran makamantansu. Ana yawan zargin cewa wadannan kayan lambun na dauke da sinadarin da ke alfanu sosai a jikin dan adam.

Yana dauke da bitamin da ma wasu sinadaran da ke iya kashe irin nau’o’in da jiki ba ya so ya hana su zama wani abin da zai iya kasancewa cuta ya kuma inganta garkuwar jiki.

Dama dai jikin mutun na fitar da wadansu kwayoyin da ake kira free radicals a yayin da ya ke sarrafa abinci da sauransu. Wadannan kwayoyin ba su dadewa a jiki amma kuma suna da lahani sosai ta yadda suna iya lalata wasu kwayoyin jikin da ake bukata su ma kai ga haddasa cututtuka kamar su cutar daji.

Yayin da jikin da kan shi yana iya fitar da irin wadannan kwayoyin, abinci kamar kayan lambu irinsu brocolli na iya taimakawa domin su kan iya narkar da irin wadannan sinadaran.

Wannan ne ya sa mutane ke ganin kamar yana iya warkar da cutar daji ko ma kare jama’a daga kamuwa da ita.

Brocoli yana dauke da sinadarin sulfuraphane (SFN) wanda aka san cewa yana yaki da cututtuka kuma kawo yanzu shi ne mafi karfi a sinadaran da ake samu a ganyayyaki wanda aka sani suna iya yakar kwayar cutar daji

Shin Broccolin na warkar da cutar daji ko ma bayar da kariya daga kamuwa da cutar?

Cibiyar Cancer ta Kasa binciken da aka yi kan dabbobo ya nuna cewa sinadaran gyara jikin da ake samu daga abinci na rage kaifin kwayoyi masu lahanin da ake samu a jiki bayan ya sarrafa abinci da sauransu musamman wadanda ake danganta su da haddasa cutar daji.

Wani binciken kuma wanda ya yi bitar rubuce-rubucen da aka yi dangane da batun ya ce sinadarin SFN na iya hana cuta girma ko bunkasa, sake afkuwa bayan ya tafi ko kuma fadada zuwa sauran gabobin jiki. Yana kuma kare kwayoyin jiki masu inganci daga masu lahani ba tare da ya kashe su ba.

Wani binciken shi ma ya nuna cewa ganyen da furen shi na dauke da sinadaran da ke iya yakar kwayoyin cutar dajin

A yayin da gwajin da ake yi a dakunan gwaji da kuma a kan dabbobi sun tabbatar da wannan bayanin, ana bukatar karin bincike da gwaje-gwaje dan tantance inganci, irin matsalolin da ka iya biyo baya idan an yi amfani da shi da ma yawan da ya kamata a yi amfani da shi domin gano irin alfanun da za’a samu.

Ra’ayin Kwararru

Sunday Idoko likitan mata a asibitin Garki da ke Abuja ya ce lallai ganyen na brocoli na dauke da sinadaran da ke taimakawa wajen kare jiki daga kwayoyi masu lahani amma ba shi tabbacin zargin da aka yi dangane da tasirin shi a kan cutar daji.

“Bani da tabbacin haka. Sai dai kayan lambu ne kuma suna da sinadai masu amfani sosai a jikin dan adam,” ya bayyana

Jeremiah Agim, babban ma’aikaci/rajistra a National Hospital Abuja ya ce shi dai ba shi da abin da zai fada dangane da wannan zargin domin har yanzu ana bincike.

“Bani da abin fada, har yanzu ana matakin bincike ne. Ku duba kasidun binciken da aka bayyana a sam,” ya ce.

Arinze Obiadazie wani jami’in lafiya kuwa cewa ya yi “ba gaskiya ba ne.”

A Karshe

Duk da cewa broccoli na dauke sinadarin da aka san yana yakar kwayar cutar daji mai suna SFN, har yanzu ana gwaje-gwaje. Dan haka ba za’a iya cewa broccoli na warkar da cutar dajin ba tukuna ko ma dai kowani irin nau’i na cutar dajin.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button