Bayan da DUBAWA ta gudanar da bincike kan wadansu jerin ayyukan zambar da aka gudanar ana amfani da wata yarinya ‘yar shekaru 9 na haihuwa wajen yaudarar jama’a, masu aikata zambar, Nativ Halev sun cire bidiyon mai sosa rai na yarinyar mai suna Alexander daga shafin su.
Bidiyon Alexander wanda da shi ne babban hoton da ke shafin ba ya wajen kuma. Dama da dai bidiyon ya gwado ‘yar yarinyar tana kuka tana neman taimako. “Ba na so in mutu,” ta ke cewa a yayin da hawaye ke zuba a fuskarta. Da wannan kuwa ta sosa ran jama’a da yawa wadanda ba su ji ba su gani ba wajen bayar da gudunmawar kudi mai yawan gaske wanda a binciken da DUBAWA ta gudanar, ta gano cewa ya kai dalan Amurka dubu dari bakwai, wato $700,000
Manyan shafukan soshiyal mediyan da su ka hada da Facebook, Youtube da Google Ads sun dauki nauyin yada bidiyon kyauta sun dauka labarin da gaske ne. Duk da haka, DUBAWA ta gano cewa ba da dadewar nan ba aka kirkiro Netiv Halev a matsayin kungiya mai zaman kanta wadda za ta rika taimakawa marasa lafiya da iyalansu.
‘Yan Najeriya sun mayar da martani dangane da wannan zambar inda suka nuna takaicinsu da tausayi wa yarinyar da aka yi amfani da ita. Sai dai binciken DUBAWAr ta sake gano cewa Alexander ba ita kadai ba ce akwai irinta, wato yara kanana da dama da ake amfani da su wajen zambatar jama’a.