African LanguagesHausaMainstream

Zanga-zangar Saliyo: Ofishin jakadancin Amurka bai yi amfani da kananan jirage marasa matuka na “Drones” ba, don fallasa ‘yan sanda

Zargi: Ofishin jakadancin Amurka ta tura kananan jirage marasa matuka masu kyamerori sama da 300 don si fallasa duk ‘yan sandan da ke yunkurin hana masu zanga-zanga gudanarwa cikin kwanciyar hankali

Zanga-zangar Saliyo: Ofishin jakadancin Amurka bai yi amfani da kananan jirage marasa matuka na “Drones” ba, don fallasa ‘yan sanda

Karya ne! ba mu taba sa irin wadannan jiragen ba a cewar jami’in ofishin jakadancin Amurka

Cikakken bayani

Wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Abdulai Jalloh ya wallafa wani labari a shafin da ake kira “Friends Who Like Radio Democracy 98.1 FM” wato abokai wadanda ke son rediyon dimokradiyya ta 98.1 FM – tare da hoton irin kananan jiragen nan marasa matuka wadanda aka fi sani da drones, yana zargin wai ofishin jakadancin  Amurka a Saliyo tare da wani babban jirgin ruwan tsaron kan iyaka sun tura jiragen sama da 300 domin su gano duk ‘yan sandan kasar, wadanda za su yi kokarin dakatar da masu zanga-zanga daga gudanarwa a ranakun da aka tsayar wato 8, 9 da 10 na wazan Ogostan 2022

Wannan zargin na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wasu bangarori na kungiyoyin matasar da ke kasar suka sanar cewa za su gudanar da zanga-zanga ko kuma ma za su hana wa kansu fita zuwa ko’ina dan nuna adawa da hau-hawan farashin kayayyakin masarufi a kasar.

A yayin da hakan ya kasance gaskiya, kuma ma an tabbatar cewa wasu matasan da ke nuna rashin amincewarsu da yanayin tsadar rayuwan sun yi barazanar fita su yi zanga-zangar a kan tituna, ba za’a iya cewa ofishin jakadancin Amurka ya taka wani rawa a shirye-shiryen zanga-zangar ba. To sai dai ganin yadda zargin na Facebook ya zama sanadin cece-kuce, DUBAWA ta yanke shawarar gano gaskiyar wannan batu dan tantance ko lallai ofishin jakadancin Amurkar na da hannu a zanga-zangar.

Me ya sa tantance wannan zargin ke da mahimmanci?

DUBAWA reshen da ke binciken gaskiyar bayanai na Cibiyar Aikin Jarida, Sabbin Dabaru da Cigaba wato CJID (Centre for Journalism, Innovation and Development) na ganin ya kamata a tantance wannan zargin domin yana iya lalata dangantakar da ke tsakanin Saliyo da ofishin jakadancin Amurka. Bisa la’akari da tanadin yarjejenyar Vienna dangane da hulda ko dangantaka ta diflomasiyya, bai kamata ofishin jakadancin Amurka ya sanya baki a siyasar cikin gida na kowace kasa ba, kuma wannan har da Saliyo. Saboda haka idan har akwai labarin da ke zargin ofishin da tura jirage marasa matuka lokacin zanga-zanga zai sabawa yarjejeniyar idan har ya kasance gaskiya.

Tantancewa 

Domin tantance gaskiyar wannan bayanin, DUBAWA ta fara da duba shafin ofishin jakadancin Amurkar da ma sauran shafukanta na soshiyal mediya a Saliyo dan ganin ko akwai wani martani da ofishin ya mayar dangane da zargin.

Ba mu komai kamar haka ba!

Ganin cewa babu wata sanarwar da ta karyata wannan zargin a hukumance, DUBAWA sai ta tuntubi Alhassan Jalloh ta wayar tarho, wanda shi ne mai kula da harkokin da suka shafi manema labarai a ofishin jakadancin Amurkar na Saliyo, don jin ko zai amince ko kuma zai yi watsi da zargin.

Mr Jalloh ya nisanta ofishin jakadancin da labarin jirage marasa matukan da aka yi a facebook, abin da ya kira “Fake News”.  “Wannan labarin karya ne, kuma ba shi a shafinmu na Facebook,” ya ce. Ya kuma kara da cewa ofishin jakadancin Amurka ba za ta iya shiga harkokin siyasar cikin gida na wasu kasashe ba.

DUBAWA ta kuma tambayi Mr. Jalloh ko ofishin jakadancin zai dauki mataki  dangane da wannan batun amma ya ce a’a inda ya ce “wannan abu ne da ba za mu iya sa ido a kai ba,” ya ce.

DUBAWA ta bi diddigin zanga-zangar na wuni ukun da wasu bangarorin matasa su ka sanar za su gudanar a kasar wadda tuni ta riga ta rikida ta zama tashin hankali, mutane da dama sun rasa rayukansu wasu kuma har da dukiyoyi. Sai dai ba mu ga wata alamar jirage marasa matuka kamar yadda labarin na Facebook ya yi zargi ba.

A Karshe

Zargin cewa ofishin jakadancin Amurka da ke Freetown babban birnin Saliyo ta tura kananan jirage marasa matuka masu daukar hoto su yi leken asiri a zanga-zangar da matasa su ka shirya a ranakun 8, 9 da 10 na watan Ogosta karya ne. Binciken da DUBAWA ta yi kafin zanga-zangar da lokacin da ake yin ta duk sun nuna babu irin jiragen da labarin na Facebook ya yi zargi. Hakanan kuma mai hulda da ‘yan jarida da kafofin yad labarai a ofishin jakadancin Amurkar Alhassan Jalloh ya karyata zargin karara inda ya ce ofishin ba za ta iya yin kutse a harkokin siyasar cikin gidan kasar ba bare har ta yi yunkurin yin katsalandan a harkokin ‘yan sandan kasar ta Saliyo

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button