African LanguagesHausa

A Shafukan Sada Zumunta, An Yi Amfani Da Wani Tsohon Bidiyon Dakarun Amurka da Kanada Suna Wasannin Motsa Jiki a Sunan Wai Dakarun Rasha da Yukirain ne

Zargi: Wani mai amfani da shafin Facebook ya hallafa wani bidiyon da ya yi suna, wanda ke dauke da wata wasar da dakarun sojojin Amurka da Kanada suka yi tsakaninsu yana zargin wai dakarun Rasha da Ukraine ne.

Wani mai amfani da shafin Facebook da sunan Topic News ya wallafa wani bidiyo da ke zargin wai dakarun Rasha da Yukirain ne ke wasannin motsa jiki duk da yakin da ke tsakanin kasashen biyu. Mai amfani da shafin ya wallafa bidiyon da gajeren tsokacin da ke cewa: “Wasar Rasha da Ukraine.”

Bidiyon mai tsawon minti uku ya nuna dakaru biyu sanye da rigunan sojoji suna gogayya a wasan yayin da sauran dakarun su ke sowa suna jinjina mu su.

Mutane fiye da milliyan uku suka kalli wannan bidiyon, mutane dubu 62 kuma su ka nuna alamar amincewa da bidiyon, a yayin da wasu fiye da dubu uku su ka yi tsokaci. 

Ga yawancin wadanda suka kalla bidiyon labari ne mai sosa rai ganin sojojin bangarorin biyu suna ma’amala da juna cikin raha da annashuwa bacin yanayin yakin da su ke ciki.

Maryjane Fernandez, daya daga cikin wadanda suka yi tsokaci kan batun ta ce abun farin ciki ne ganin yadda dakarun Rasha da na Yukirain ke wasa da juna a maimakon kashe juna.

Wata mai suna Alicia Ello ita ma mai tsokaci ta ce irin wannan hadin kan abun sosa rai ne. 

Wadansu ma sakonnin taya murna suka rubuta, kamar yadda wani Neru Bacuki ya rubuta: 

“Dakarun Rasha da Yukirain. Yana da kyau yadda mu ka gan ku kuna wasa da juna. Allah ya albarkace ku.”

Yayin da batun ya ke da sosa rai musamman ga wadanda ke sha’awar ganin an sami zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu, tun da aka fara yakin Rashar da Yukirain ake samun bayanai marasa gaskiya, shi ya sa DUBAWA ke so a tantance gaskiyar wannan zargin.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da binciken bidiyon a cikin manhajar tantance bidiyo na InVid. Sakamakon binciken ya nuna cewa an fara wallafa bidiyon ne ranar 22 ga watan Maris na shekarar 2012 a YouTube, inda aka yi mi shi taken “31 Canadian Brigade.” 

Bidiyon na ainihi ya yi cikakken bayani dangane da abun da ke kunshe a bidiyon inda ya ce gasar jani-in-ja-ka ne tsakanin sojojin Kanada da Amirka.

“Kafin tafiyar rundunar dakarun Kanada da ke rukunin 31 wadanda suka fito daga sansanin Atterbury, Indiana sun tarar da dakaru Amurka su na gudanar da wani salo na wasan ja-ni-in-ja-ka. Wannan wasa ya baiwa dakarun Kanadan sha’awa sosai har su ka nemi su ma su kara. 

Daga karshe dai wani matashi daga cikin dakarun na Kanada ya ce shi ma zai shiga a yi wasan da shi. Master Corporal John Celestino daga rundunar Windsor ya kara da daya daga cikin dakarun Amirka a wasan da suka ce lallai wasan motsa jiki ne wanda ke aiki sosai a kafafu.”

Baya ga wannan rubutun da ya bayyana takamaimai abin da ke faruwa a hoton bidiyon, su kan su sojojin da ke cikin hoton na sanye da tambarin tutocin kasashen su a hannuwan rigunan da suke sanye da su.

A Karshe 

Ainihin bidiyon na dauke da dakarun Amurka da na Kanada ne suna wasannin motsa jiki a shekarar 2012, ba dakarun Rasha da Yukrain ba kamar yadda wadanda suka wallafa hoton su ke so jama’a su yarda. Dan haka wannan zargin karya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button