African LanguagesHausa

Bacin Zargin Mahukunta, Kananan Jami’an ‘Yan Sanda na Shirin Shiga Yajin Aiki

Ranar litini 15 ga watan Maris, mahukuntan jami’an ‘yan sanda suka yi watsi da rade-radin cewa kananan jami’ansu na shirin zuwa yajin aiki har ma suka ce labaran karya ne kawai irin na “Fake News”

Bacin duk yunkurin da manyan jami’an ‘yan sanda su ka yi wajen yin watsi da batun cewa kananan jami’ansu za su shiga yajin aiki, wata takarda da ta shiga hannun jaridar PREMIUM TIMES ta nuna cewa da gaske ne ‘yan sandan na shirin kaddamar da yajin aikin.

Takardar da PREMIUM TIMES ta gani wanda aka yi wa taken “Yunkurin Kananan Jami’an ‘Yan Sanda na Shiga Yajin Aiki,” ya yi bayanin cewa jami’an sun yanke shawarar shiga yajin aikin ne bayan da aka ki aiwatar da sabon tsarin albashin da zai tabbatar da karin da aka yi mu su, da rashin makaman aiki na kwarai wadanda za’a yi amfani da su wajen yaki da miyagun ayyuka da ma dai rashin kulawan da jami’an ‘yan sandan ke fuskanta a yanayin aikin na su.

Takardar ta ce tun da dadewa Speto-Janar na ‘Yan Sanda ya ba da umurnin biyan albashin wanda ke karkashin sabon tsarin da ya tanadi sauwake mu su kudin haraji. Bacin haka, Hedikwatar ‘Yan Sandan ta riga ta gama raba duk kayayyakin aikin da ta yi alkawari.

Sai dai manyan jami’an ‘yan sandan sun yi watsi da wannan labarin su na kiran shi “fake news”

“Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya na so ta bayyana karara cewa ba abin da wannan takardar ta kunsa banda karya. Yunkuri ce kawai irin ta masharranta da wadanda ke neman batawa ‘yan sanda suna, da yaudarar al’umma ta yadda batun zai haddasa rudani,” a cewar Muyiwa Adejobi mai magana da yawun ‘yansandan a cikin wata sanarwar da ya sanyawa hannu.

Sai dai kwanan watan da ke kan takardar 15 ga watan Maris 2022 ne wanda ya nuna cewa mahukuntan ‘yan sandan na sane da yunkurin yajin aikin na kananan jami’an.

Sakon wanda ke dauke da lamaba CB: 4001/DOPS/FHQ/ABJ/Vol ya umurci duk wadanda ke rike da mukaman da su ka hada da mataimakin Speto Janar da Kwamishanonin ‘yan sanda da su kaddamar da shirin fadakarwa dangane da lamarin a wuraren aikin da ke karkashin su.

“Ya kamata ku shawarci duk mambobin da ke aiki yanzu da su yi hattara a wannan mawuyacin lokacin da mu ke fuskanta, ku kuma fada musu cewa mahukuntan ‘yan sanda na yunkurin inganta yanayin kula da ‘yan sanda a kowani mataki.”

Sakon ya kuma umurci ‘yan sanda da su guji irin trujiyar da za ta kai ga zubar da kimar ‘yan sanda a idon jama’a tunda dama can ba’a mata kallon kirki.

Takardar ya yi kira ga mataimakan Speto-Janar din da Kwamishonin’yan sanda da “su dauki sakon da mahimmanci” su kuma sanar da su da zarar sun sami sakon.

A karkashin mulkin Olusegun Obasanjo ne ‘yan sanda su ka yi yajin aiki wanda har ya kai ga tsige Speto-Janar din wancan lokacin Musiliu Smith.

Mr. Smith wanda ya kama aiki ranar 29 ga watan Mayu 1999 ya bar mukamin ranar 2 ga watan Fabrairun shekarar 2002. Yanzu shi ne Chairman na Hukumar ‘Yan sanda.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button