African LanguagesHausa

Babu “Killer Sweet” ko Kuma Alawa mai Kissa Kamar Yadda Wani Sakon WhatsApp Ke Zargi

Zargi: Wani sakon da ke yawo a Whatsapp na jan kunnen jama’a dangane da wata alawa da ake kyautata zaton ya na  dauke da guban da ke hallaka jama’a

Kusan kowane yaro na sha’awar alawa. Sai dai an sami sabon bayanin da ke kara firgita jama’a dangane da irin illolin da alwar za ta iya yi wa kananan yara.

A wani gajeren bidiyon da ke yawo a manhajan Whatsapp, an ga wani mutun wanda ba’a bayyana ko shi wane ne ba, yana gargadin cewa iyaye mata su hana yaransu sayen alawa.

Yayin da ya ke bayanin da yarbanci, mutumin ya ce wata sabuwar alawa mai suna “killer sweet” ta bayyana. Ya yi zargin cewa alawar ta na kashe mutane kuma ta na janyo ciwon ciki wa wadansa ‘yan makaranta wadanda aka gan su suna kuka a wani dakin maganin da aka nuna a bidiyon.

Wannan sakon lallai ya tayar da hankalin iyaye abin da ya sanya suka rika tura sakon sau da yawa zuwa ga ‘yn uwa da abokan arziki domin kare rayukan jama’a. Duk da cewa bidiyon mutumin bai bulla a sauran kafofin sadarwa banda WhatsApp ba, Kafofin sadarwa da dama wadanda suka hada da taskokin blog, YouTube, Facebook, Twitter da Instagram, sun yi amfani da bangaren bidiyon da ya nuna hoton daliban da ake zargi suna fama da ciwon ciki.

Sai dai ashe duk wadanda suka yi amfani da hoton yaran sun yi bayanai mabanbanta ne dangane da abin da ke faruwa. Wadansu na gagadin cewa alawar ta kasha yara, a yayin da wadansu kuma ke cewa yaran sun ci guba a dalilin alawar. Duk da cewa ana wa batun kallon magana ce kawai ta fatar bakim DUBAWA na ganin cewa wannan babban dalili ne na fayyace gaskiyar lamairin.

Tantancewa

Rahotanni daban-daban daga kafofin yada labarai masu nagarta sun bayana cewa akwai alawar da ta janyo ciwon ciki a dalubai 46 a jihar KwaZulu-Natal a Afirka ta Kudu ranar 31 ga watan janairu. To sai dai sunan alawar ba “killer Sweet” ba ne kamar yadda mai bidiyon nan ya bayyana. Sunan alawar “XPOP ENERGY RED DRAGON,” wanda kamfanin Richester Foods ke sarrafawa.

Bayan da aka danganta ciwon cikin daluban da kamfanin Richester Foods, babban darektan kamfanin Hussein Cassim a wani rahoton da aka sanya a tashar News24 ya ce kamfanin tana daukan matakan da suka dace wajen shawo kan matsalar, kuma ta kaddamar da bincike can matsalar.

To Amma da gaske ne wai dalibai 46 sun yi ciwon ciki?

A wata sanarwar manema labarai da ta wallafa, sashen kula da lafiya na jihar Kwa-Zulu Natal ta tabbatar cewa daya daga cikin asibitocin da ke karkashinta a gundumar Ilembe ta duba kananan yara 46 daga makaratar firamaren gwamnatin yankin, bayan da suka yi kukan ciwon ciki, amma kai tsaye ta yi watsi da labarin cewa yaran sun mutu.

Sashen Lafiyar ya ce “ ba mu riga mun kai ga gano dalilin da ya sa yaran suka kamu da irin wanann ciwon ba amma likitoci sun duba yaran sun basu magunguna sun koma gida a ranar babu wanda ya kwana a asibiti.”

Sakamakon da kamfanin sarrafa abinci na Richester Food ya samu dangane da batu

Bayan da kamfanin ya gudanar da bincike a cikin gida, ya wallafa matakan da ya dauka a shafins hi na Facebook, inda ya jaddada cewa alawar kamfanin na XPOP Energy ba shi ne ya yi sanadiyyar ciwon cikin wadannan yaran ba.

“Tun shekarar 2017 mu ke saida alawar XPOP Energy kuma ba mu taba samun matsala ba ko korafi a tsawon shekaru biyar din da mu ke sarrafawa al’umma na saye,” kamfanin ya rubuta.

Wanda ya yi wannan zargi ya yi amfani da bidiyon wadannan yaran ne wadanda kawo yanzu ba’a tabbatar cewa alawar XPOP ce ta janyo mu su ciwon cikin ba.

A Karshe

Duk da cewa dalibai 46 sun je asibiti da ciwon ciki a jihar KwaZulu Natal ba wata kwkwarar hujjar da ta danganta ciwon cikin na su da alawar XPOP Energy Red Dragon. Banda haka, alawar ta dade a kasuwa ba sabuwa ba ce tun 2017 aka fara saida ta.

Sashen kula da lafiya na KwaZulu Natal ta bayar da tabbacin cewa babu dalibin da ya hallaka.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button