Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Ibrahim Babangida, tsohon shugaban kasar Najeriya ya bayyana yiwuwar dawowar mulkin soji a Najeriya sakamakon matsanancin matsalar da tattalin arzikin kasar ke fuskanta.
Sakamakon bincike: Yaudara! Shafin ba na Babangida ba ne, ba shi ke iko da shi ba. Shafin masu barkwanci ne.
Ciakken bayani
Akwai martanoni da dama da suka biyo bayan sabbin manufofin tattalin arzikin da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa. ‘Yan Najeriya da ayawa a soshiyal mediya na korafin tashin farashin kayayyakin abinci a kasar.
Baya ga cece-kucen da ake yi a shafukan sadarwa, ‘yan Najeriya sun kuma fantsamam kan tituna dan bayyana rashin gamsuwarsu da manufofin gwamnatin da suka ta’azara matsalolin tattalin arzikin talakawa.
Ranar Litinin, wasu mazauna Ibadan jihar Oyo su ma sun fantsama kan tituna dan gudanar da zanga-zanga. Sun dauki takardun da aka rubutawa kasidu kamar: “Ku kawo karshen tsadar kayayyakin abinci da hauhawar farashin kayayyaki,” “Rashin tsaro ba gadon mu ba ne” “Shugaban kasa wannan ba kyakyawar fata ba ne, shege ne.”
Wannan zanga-zangar na Ibadan na zuwa ne bayan da aka gudanar da wata irinta, wadda ita kuma aka yi a Minna da ke jihar Neja, makwanni kadan kafin nan ita dan tsadar farashin kayayyakin rayuwa.
Wani binciken farashin kayayyaki a kasuwannin da Premium Times ta yi ya fayyace dalilin ya sa kowa ke kuka domin ta gano yadda farashin kayayyaki suka karu tsakanin ‘yan watannin da suka gabata.
To sai dai masu amfani da soshiyal mediya su ma suna amfani da wannan damar su yada labarai marasa tushe bare makama.
Wanni mai amfani da shafin X @General_Ibbro (Ibrahim B. Babangida) ya yi tsokaci dangane da batun, har da cewa ma yana zaton sojoji na iya zuwa su yi juyin mulki.
“Ina kira ga gwamnatin tarayya da ta taimakwa ‘yan Najeriya kafin abun ya zama annoba.”
Mutane sama da 300,000 sun yi ma’amala da batuin kuma da yawa sun sake wallafawa ko kuma sun yi amfani da shi cikin sakonninsu.
Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) tsohon shugaban kasar Najeriya ne daga shekarar 1985 zuwa 1993. Tun bayan da sauka daga mulki ya kafa gwamnatin rikon kwarya a shekarar 1993, tsohon shugaban kasar ya cigaba da bayar da gudunmawarsa a harkokin da suka shafi gina kasa da sauransu.
Dan haka wannan batun da ya shiga ko’ina a shafin X ya janyo rudani sosai a kan dandalin inda aka sami ra’ayoyi mabanbanta dangane da juyin mulkin da labarin ke hasashe.
Yayin da akwai wadanda ke maraba da batun, saura sun yi Allah wadai da shi, inda suka ce gwamnatin sojoji ma sai ta fi lalacewa.
An kuma wallafa wannan batun a shafin YouTube.
Saboda sarkakiyar da irin wannan batun ke tattare da shi da ma sunan wanda ake dangantawa da zargin ne ya sa DUBAWA ta kuduri aniyar gano gaskiyar lamarin.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da duba shafin dan tantance sahihancin shi. Bayanan da ke kai sun nuna cewa a shekarar 2013 aka bude shafin kuma daga Minna, jihar Neja ake amfani da shafin.
Duk da cewa wanda ke amfani da shafin ya ce shafin na barkwanci ne kuma ba IBB ke kula da shafin ba, yawancin wadanda ba su ga wadannan bayanan ba sun dauka da gaske tsohon shugaban mulkin sojin ne.
Binciken da muka kara yi kuma ya nuna mana cewa su kansu wadanda ke yada batun yawancinsu na yadawar ne saboda sun dauka shafin IBB din ne a zahiri dan haka sun yi imani da abun da ue ke fada.
Wannan ne ya janyo martani daga wajen IBB. a cikin wata sanarwa, Deyemi Saka, mai bai wa Babangida shawara kan kafofin yada labarai ya yi watsi da wannan da’awar ya kuma yi kira ga l’umma da ta yi watsi da batun.
Mr Saka ya yi bayanin cewa idan da a ce akwai damuwa irin wannan, da maigidan nasa ya yi amfani da hanyoyin da suka dace ya yi magana da shugaba Tinubu kai tsaye ba sai ya je soshiyal mediya ba.
Kadan daga cikin sanarwar na bayanin cewa:
“Janar Babangida na matukar son mulkin dimokiradiyya, ko a lokacin da ya ke shugabanci da yanzu da ya riga ya bar wurin. Ya yi imanin cewa mulkin dimokiradiyya ce salon shugabancin da ya fi kowanne dacewa kuma zabe ne kadai halattaciyar hanzar sauya gwamnati ko nuna mata goyon baya.
“Idan da Janar Babangida na da wata damuwa dangane da abubuwan da ke faruwa a kasar, da zai iya amfani da zarafin da ya ke da shi a taron majalisar kolin kasar da ya kan halarta ya bayyana ra’ayinsa, a maimakon zuwa soshiyal mediya ko ma dai bainar jama’a…..”
Haka nan kuma sashen kula da yada labaran tsohon shugaban sun dade suna fadawa al’umma cewa Janar din ba shi da shafins sohiyal mediya kamar yadda aka bayyana a nan da nan.
A waje guda kuma, DUBAWA ta taba gano shafin a matsayin shafin da ya dade ya na yaudarar ‘yan Najeriya a kan manhajar X.
Manhajar X na kwatanta shafin barkwani, wanda ake kira parody da turanci, ko kuma mai fashin baki, ko wanda ke zaman na ma’abota, a matsayin shafin “da ke bayyana kansa a matsayin wani/wata ko kungiya dan tattaunawa, ko mayar da abu ba’a ko kuma dai yada bayanai dangane da shafin..” Ta kuma kara da cewa, yayin da irin wadannan shafukan ke iya amfani da sunan wani/wata, ya kamata akwai abun da zai sanarwa mutane cewa abun da ke faruwa a shafin ba shi da alaka da wanda ake amfani da sunarsa a shafin.
Ko da shi ke, duk da cewa wannan shafin ya bayyana kansa a matsayin na barkwanci, ba kowa ba ne ya natsu ya gudanar da bincike da zai bayyana mi shi hakan.
A Karshe
Zargin cewa Babangida na da’awar cewa sojoji za su dawo su yi mulki saboda rikicin tattalin arzikin da ake fama da shi a kasar yaudara ce kawai. Ya yi mafari ne daga wani shafin X mai dauke da sunan IBB, amma kuma ba shi ne ke kula da shafin ba, ba shi ma da wata alaka da masu shafin.