Getting your Trinity Audio player ready...
|
Gabatarwa
Azumin watan Ramadan na daga cikin ayyukan da Allah Ya wajabta wa bayinsa, kuma rukuni ne daga cikin rukunan Musulunci guda bıyar, kamar yadda ya tabbata a Hadisin da Abdullahi bin Umar (RA.) ya rawaito:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce. “An gina Musuluncı akan abubuwa guda biyar, Shaidawa babu abin bautawa da gaskıya sai Allah, da kuma shaidawa Annabi Muhammad Manzon Allah ne, da tsayar da sallah, da bada zakkah, da aikin hajji, da azumin watan Ramadan. Buhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Abubuwan da ba sa karya azumi
A yayin al’ummar musulmi a fadin duniya ke wannan azumin na watan, akwai abubuwa da dama da mutane ke tunanin suna karya azumi sai dai a hakika ba su karya azumin.
Wannan ya sa Dubawa ta tuntubi Hamdany Abdullahi, wani malamin addinin musulunci a Nijeriya, domin ya yi mana bayanin wasu abubuwan da mutane ke tunanin suna karya azumu amma kuma ba sa karya azumin.
Ga jerin wasu abubuwa 10 da malamin ya yi bayanin cewa ba sa karya azumi:
1. Shakar turare
Ba ya karya azumi kasancewar ba abinci ne ba kuma ba abin sha ba.
2. Fitar jini a hanci/haɓo
Jinin da yake fita a baki haka kawai wanda ake kira habo, ba ya karya azumi
3. Cirewar hakori
Idan lalura ta rashin lafiya ta sa aka cire hakorin mai azumi ko kuma hakorin ya cire da kansa, azuminsa na nan. Sai dai idan tsananin ciwo ya sa mai azumi azumi karya shi da kansa.
4. Yin allura
Allura ta kasu kashi biyu: Akwai ta rashin lafiya wadda likitoci ake yi ta rashin lafiya ita wannan ba ta karya azumi. Sai dai akwai wata allura da take iya zama madadin abinci, lokacin da aka yi wa mutum ita zai ji kamar ya ci abinci, wannan ita ce ke karya azumi.
5. Sanya maganin ciwon idanu
Ba laifi bane kuma ba ya karya azumi don mutum ya saka magani a idanunsa domin samun sauki.
6. Yin amfani da man wanke baki
Yin buroshi ko kuma wanke baki da mai ciki har da mai dandano, ba ya karya azumi sai dai idan mutum ya hadiye shi har ya shiga cikin ciki.
7. Yin Amai
Wannan shima malamai sun yi fatawa cewa ba ya karya azumi, sai dai idan mutum ne ya kirkiro amai da kansa to zai karya masa azumi kuma sai ya rama daya.
8. Amfani da inhaler ga masu athma
Malamai sun ce shima ba ya karya azumi. Malamai sun bada fatawar cewa ba abinci ba ne iska ce ake shaka domin samun sauki ga masu rashin lafiyar athma.
9. Yin mafarki har a samu fitar maniyi
A nan ma mafi rinjayen malamai sun ce idan mutum ya kwanta ya yi mafarki ko da ya tashi ya ga maniyyi ya fita, to azuminsa yana nan wankan janaba kawai zai yi ya ci gaba da azuminsa.
10. Sumbata/Runguma tsakanin ma’aurata
Wadannan duk ba sa karya azumi a fatawar da malamai suka bayar, sai dai idan zai kai ga barna (kusantar juna) malamai sun bada shawarar a guje hakan.