Getting your Trinity Audio player ready...
|
Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da kawancen kasashen Afrika da yankin Caribbeans da na yankin Pacific (OACPS) da Najeriya ke zama mamba a baya-bayan nan sun kulla wata yarjejeniya da ake kira Yarjejeniyar Samoa.
Yarjejeniyar ta Samoa ta kunshi yadda kasashen na Tarayyar Turai 15 za su yi alaka da kasashe 79 na Africa da yankin Caribbea da Pacific .
Yarjejeniyar an fara ta a 1959 da kulla yarjeniyar Yaounde wacce daga bisani aka yi mata kwaskwarima da a baya-bayan nan aka samar da yarjejeniyar Cotonou, sai dai wannan yarjejeniya ta zama mara tasiri da muhimmanci a 2020, shekaru 20 bayan kulla yarjejeniyar.
Har ila yau bayan da yarjejeniyar Yaounde ta kammala wa’adinta gamayyar kungiyoyin sun kara mata zango har zuwa Oktobar 2023, tabbasa hakan ya faru kafin a baya-bayan nan a samar da yarjejeniyar Samoa.
Dalilan samar da Yarjejeniyar Samoa
Yarjejeniyar ta bijiro da abubuwa da suke da buri da manufa aka kuma kafa su karkashin dokoki na alakar kasashen da ake son cimmawa. Wannan ya hadar da:
- A samar da shugabanci nagari a kafa ginshikai na dimukuradiyya da za ta kare hakkin bil Adama.
- A samar da zaman lafiya a samu tsaro mai dorewa cikin kasashe da ke zama mambobi na kungiyar.
- Akafa alaka ta ilimi da lafiya da ba da kulawa ga jinsi da kare hakkin bil Adama.
- A bunkasa harkokin kasuwanci da karfafa gwiwar harkoki na zuba jari da samar da basuka don raya kasa.
- A samu hadin kai kan batun sauyin yanayi da kare muhalli da fafutuka kan tsare-tsare.
- A kawo karshen kwararar baki ba bisa ka’ida ba, da bin hanyoyi na halak wajen shige da ficen baki.
Najeriya da Yarjejeniyar Samoa
Najeriya mamba ce a kawancen na EU/OACPS wani bangare na yarjejeniyar ta Somoa, wacce ke duba wasu batutuwa da suka shafi kasar don nema mata mafita.
Cikin abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa sun hadar da samar da kudade bashi da samar da horon kwarewa ga ‘yankasar da wani taimako na ci gaba, Yana kuma duba yadda za a inganta batu na ilimi da lafiya da samar da ababen more rayuwa cikin alakar.
Ta hanyar wannan yarjejeniya Najeriya za ta amfana a kasuwannin kasa da kasa, ta samu kudaden shiga ta hanyar kasuwancin da zaa a rika ratsa iyakoki.
Najeriya za ta iya amfana ta hanyar tattalin arziki da ababen more rayuwa da ma tunkarar kalubale da ke fuskantar duniya kamar na sauyin yanayi da tsaro.
Wannan abune da zai yiwu ta hanyar alakar Najeriyar da Kungiyar Tarayyar Turai EU da sauran kasashen na OCAPS. Kasancewar ba Najeriya ita kadai bace a wannan yarjejeniya, sai dai mataki da take kai muhimmi ne a yankin da take.
Haka kuma kasancewar Najeriya tana da hannu a wasu yarjejeniyoyi kafin wannan, yarjejeniyar ta Samoa ba za ta zama kalubale a gare ta ba.
Yarjejreniyar na barazana ga dokoki na Najeriya
Yayin da wasu batutuwa a duniya ke kara samun karbuwa a wasu yankuna, a wasu yankunan kuma ana watsi da su, irin wadannan abubuwan sun hadar da misali auren jinsi da sauya halittar mutum da zubar da ciki da auren wuri.
A Najeriya har yanzu batu na auren kananan yara ana ci gaba da magana a kansa, su kuwa batu na sauya halittar mutum ya fuskanci turjiya ga mafi akasarin al’umma, haka batun yake ga sauran abubuwa da suka shafi zamantakewa da al’ada kamar batun mata masu neman mata da maza masu neman maza, masu da’awar neman maza da mata lokaci guda da masu sauya halittarsu da ‘yan kungiyar ta (LGBTQ), irin wadannan abubuwan ne suka sanya Najeriya ke jan kafa ga batun sanya hannu a yarjejeniyar.
A kwai ma batun rashin samun daidaito kan yarjejeniyar kasuwancin. Najeriyar na ganin abin da za ta mora bai taka kara ya karya ba daga yarjejeniyar. Wannan zai shafi tattalin arzikin kasar da harkokin kudadenta.
A karshe yadda yarjejeniyar ke da sarkakiya wajen aiwatarwa kamar yadda ke kunshe a yarjejeniyar na iya zama barazana ko nauyi ga gwamnatin Najeriya da harkoki na kasuwanci a cikin gida. Tsarin na iya hana Najeriya shiga harkokin bisa dalilan tsare-tsarenta na cikin gida.
Amma shin akwai mafita?
Tun da sharudan da aka kafa na Samoa ba su dace da abubuwan da Najeriya ke muradi ba, abu guda kuma da za a duba anan shine kulla dangantaka tsakanin kasashe biyu da wasu muradunsu na cikin gida sun fi wahala da ma tsada wajen aiwatarwa, za a fi amfana da Najeriya fiye da abin da za ta amfana daga nahiyar da take.
Haka kuma abubuwan da ba ta gamsu ba ana iya tattaunawa a samu maslaha, Idan kuma anan gaba gwamnatin Najeriya ta fahimci cewa yarjejeniyar na zama barazana ga harkokin siyasarta da tattalin arziki da zamantakewa da al’ada, tana iya ficewa, sai dai abin ba lallai ya zamo mai sauki ba.
Wannan ya sanya Najeriya sai ta yi nazari a tsanake kan irin alfanu da za ta iya samu idan ta shiga yarjejeniya da tattaunawa da irin sharudan da ake gudanarwa ta yadda kasar za ta samu damar hada-hadar kasuwanci bisa daidaito ba tare tarin kalubale ba na kasuwanci.
Najeriya cikin nutsuwa tana bin tsare-tsarenta da za su taimaka mata wajen cin moriya ta duk wata yarjejeniya da za ta shiga yayin da a gefe guda take taka tsan-tsan da duk wata matsala da ka iya tasowa, idan aka cika wadannan sharuda ne na samar da ci gaba da walwala yarjejeniyar ta Samoa ke iya zama abar soyuwa