African LanguagesHausa

Karya ce! Yin tsalle baya sa fitsarin da ya makale ya fita a mafitsarar maza

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani bidiyo da ya bazu a shafin WhatsApp ya nunar da cewa yin tsalle sau 15 zuwa 20 na sanyawa a samu saukin yin fitsarin da ya makale a wajen mazaje.

Karya ce! Yin tsalle baya sa fitsarin da ya makale ya fita a mafitsarar maza

Hukunci: Babu wata sheda a kimiyance da ta nuna cewa idan mutum yayi tsalle yana samun saukin fitar fitsarin da ya makale a maza, don haka wannan da’awa karya ce.

Cikakken Sakon

A baya-bayan nan wani sako a shafin WhatsApp ya yadu, sakon da ke da’awar idan mutum na yin tsalle akai-akai sau 15 zuwa 20 zai iya samun saukin yin fitari.

Shi yanayi na makalewar fitsari, yanayi ake samun kai fitsari yayi wahalar fita ko kadan-kadan ko baki daya, abune sananne ga mazaje masu shekaru tsakanin 60 zuwa 80.

Mai waccan da’awa ya yada labarin wani mutum dan shekaru 70 wanda ya farka daga bacci ya gaza yin fitsari sai ya kira wani abokinsa masani kan mafitsara, wanda ya fada masa cewa ya tashi tsaye yayi tsalle sau 15 zuwa 20,  sai dattijon ya aikata haka, bayan yin tsallen sau 5 zuwa 6 sai ya ji alamun yin fitsarin. Wannan labarin ya yada shi a group-group da dama.

False! Jumping does not relieve urine retention in men

A baya shirin gano gaskiya na DUBAWA kan yi watsi da irin wadannan labaru da ake yadawa a shafukan WhatsApp wanda yake bayyanawa da cewa karya ne, amma yadda wannan labari ya yadu da illar da zai iya yi kan harkokin kula da lafiya  DUBAWA ya tsara gudanar da bincike a kansa. 

Tantancewa

A cewar cibiyar kula da lafiya ta kasa, shi makalewar fitsari ( urinary retention) ana danganta shi da fitar fitsarin kadan-kadan ko kuma yaki fita baki daya daga mafitsara, ko kuma mafitsarar ya zamana ba ta da karfin da za ta iya tura fitsarin ya fita.

A shekarar 2019 wani bincike (research) da Steven Kaplan,  dan Amurka masanin ilimin abin da ya shafi mafitsara ya gano cewa makalewar da fitsarin kan yi na faruwa ne bayan lokaci mai tsawo, wani lokacin yana nuna alama wani lokacin kuma babu wata alama da zai nuna, abin da ke sawa ya zama yana da wahala a gano. Wasu daga cikin alamun sun hadar da idan mutum yana fitsari cikin mafitsarar (bladder) sai ya gaza kammala shi baki daya. Ko a rika fitsari kadan-kadan a yi ta zuwa bandaki, ko ya zama yana da wahala mutum ya fara fitsari wannan ake kira hesitancy a Turance, da yin fitsarin yana zuwa kadan-kadan, a rika jin zafi yayin gudanar da fitsarin.

Masana a wannan fannin (Urology specialists) sun bayyana cewa wayewa idan mutum ya gaza yin fitsari ko jin zafi a kasan cibiyarsa shine ya je yaga kwararrun likitoci a wannan fanni.

A wani binciken research da Joseph Dougherty, Stephen Leslie da Narothama Aeddula suka yi kan abin da ya shafi mafitsarar, sun bayyana karin wasu dalilan da suka hadar da kashin kwibi da kwibi da mafitsarar da rudani da ake samu a matattarar fitsarin ko wasu ciwuka da aka samu lokacin da aka yi wa mutum aiki.

Babban magatakarda a babban asibiti na kasa a Abuja  Johnson Udodi,  ya fada wa DUBAWA cewa wannan da’awa karya ce , ya ba da shawarar cewa mutum da ke samun wahala kafin fitsarinsa ya fita ya je asibiti saboda rashin iya fitsarin na iya zama saboda dalilai da dama ciki kuwa har da ciwon daji da kan shafi mafitsara.

“Rashin samun damar fitar fitsari na iya zama saboda wani tangarda a hanyar mafitsarar , wannan kuwa na iya zama saboda dalilai da dama  kamar kumburar matattarar fitsarin ko wani dutse da wasu abubuwan da kan shafi mafitsarar. A lokacin da maza shekaru ke karuwa halittar da ke cikin mafitsararsu da ake kira prostate gland sannu a hankali za ka ga tana girma.

Mutumin da ya kai shekaru 70 idan yana kasa yin fitsari ya je asibiti saboda ta yiwu saboda wasu dalilai ne ya gaza yin fitsarin  kamar yadda aka bayyana a baya koma dalilin cutar kansa ne,” a cewarsa.

Dr. Udodi yace abune mai wahala “kace abin da wani ya gani karya ne domin ba za ka ce bai faru a gare shi ba, kawai dai irin wannan matsala shekaru ne, tsalle ba zai zama mafita ba, don haka yadda aka nunar zai zama mafitar karya ne.” A cewar Dr. Udodi.

Shima da yake nasa sharhin kamar Dr. Udodi, Babagana Modu, wani ma’aikacin lafiyar a Abuja ya ce ga duk wanda ke jin wata matsala a mafitsararsa ya je ya ga likita don samun taimako.

“Akwai tarin dalilai da ke iya kawo mutum ya kasa yin fitsari, musamman ga mazajen da suka manyanta, bayyana wata mafita guda daya tilo ba gaskiya ba ne, abu mafi kyau shine a je a ga kwararren likita idan aka ga wasu alamu, a cewarsa.

A Karshe

Babu wata hujja daga masana kimiya cewa idan mutum yayi tsalle sau 15 zuwa 20 zai samu saukin yin fisari. Da’awar karya ce.

Wannan rahoto an fitar dav shi ne karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 karkashin shirin kwararrun masu gano gaskiya labari na Kwame Karikari da hadin giwa da Premium Times/UNILAG, a kokarin da ake yi na mutunta fadin gaskiya a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a Najeriya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button