African LanguagesHausa

Sabanin abin da wani mai amfanin da shafin X ya wallafa, a cikin kasashen Afurka akwai wadanda ke  biyan mafi karancin albashi sama da Naira N400,000  

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X, Kawu Garba (@KawuGarba), yayi  da’awar (claimed) cewa babu wata kasa a Afurka da ke biyan N400,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Sabanin abin da wani mai amfanin da shafin X ya wallafa, a cikin kasashen Afurka akwai wadanda ke  biyan mafi karancin albashi sama da Naira N400,000  

Hukunci: Karya ce! Kasashe kamar  Seychelles da Libya da  Morocco na biyan sama da N400,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Cikakken Sakon

Gwamnatin Tarayyar Najeriya na fuskantar matsin lamba daga hadakar kungiyoyin kwadago na NLC da TUC a dangane da mafi karancin albashi da za a biya ma’aikata a kasar. 

Kawo yanzu mafi karancin albashi a kasar shine N30,000 a duk wata wanda aka kara shi daga 18,000 a 2019 karkashin mulkin tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari.

A lokacin yakin neman zanbe na 2023 wanda ya kai Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan karagar mulki , yayi alkawarin cewa zai tabbatar da ganin cewa ma’aikata na rayuwa mai tsafta a kasar ta hanyar biyansu albashi mai kyau. Jaridar PremiumTimes ta jiyo shugaban na cewa (quoted) `Na samu dama da daukaka ta jagorantar wannan kasa tun daga ranar 29 ga watan Mayu, ma’aikata za su samu albashi da za su rika rayuwa mai kyau su rika sama wa iyalansu ababen masarufi.”

Sai dai duba da halin tattalin arziki da ake ciki ‘yankwadagon sun amince cewa mafi karancin albashi N30,000 ba zai wadatar da ma’aikaci ba.

Hadakar kungoyoyin kwadagon dai sun nemi da gwamnatin tarayya ta biya mafi karancin albashi 615,000, suka kuma ba wa gwamnatin wa’adi zuwa 31 ga watan Mayu idan ba a biya ba za su tsunduma yajin aiki a fadin kasar.

An dai zauna tattaunawa da bangarori masu zaman kansu da  gwamnati kan kudin da za a biya a matsayin mafi karancin albashi, amma dai zaman da aka yi ba a cimma wata nasara ba.  

A ranar 31 ga watan Mayu gamayyar kungiyoyin kwadagon sun ayyana ( declared )yajin aiki a kasa baki daya inda aka fara a uku ga watan Yuni bayan da kwamitin mai bangarori uku ya gaza cimma matsaya kan mafi karancin na albashi ga kuma ta’azzarar farashin lantarki.

Wannan yajin aiki ko da yake an dakatar da shi (suspended) bayan da bangaren kwadagon da bangaren gwamnati suka cimma wata matsaya. Ta bayyana cewa an cimma wata matsaya da bangaren na gwamnati, bayan da ta bayyana gwamnatin karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu  ta bayyana (expressed) shirinta na samar da kari akan N60,000 da gwamnatin ta bayyana mafi karancin albashi tun da fari.

Anan kuma a ranar ta uku ga watan Yuni sai wani mai amfani da shafin X, Kawu Garba (@KawuGarba), claimed, yayi da’awar cewa babu wata kasa a Afurka da ke biyan N400K a matsayin mafi karancin albashi.

Ya zuwa ranar biyar ga watan na Yuni, wannan wallafa ta samu mutane miliyan daya da suka kalla ( views) an samu wadanda suka sake wallafawa su 257 baya ga masu sharhi 362 da masu kafa hujja 17. Da dama ‘yankasar na cewa ma’aikata a Najeriya sun cancanci abin da yafi wanda gwamnati ke cewa za ta basu duba da halin tattalin arziki da kasar ke ciki.

DUBAWA ya shirya gudanar da bincike kan wannan da’awa da ke cewa babu wata kasa a Afurka da ke biyan mafi karancin albashi N400,000.

Tantancewa

DUBAWA ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi ta nemi bayanai kan mafi karancin albashi a nahiyar ta Afurka. Mun samu a ranar 23 ga watan Maris jaridar BusinessDay ta fitar da rahoto inda take kwatanta mafi karancin albashi na Najeriya ( Nigeria’s minimum wage) N30,000 da wasu kasashe na Afurka. 

Rahoton ya nunar  (shows), inda ya kwatanta bisa kiyasi idan ana siyar da kowace dalar Amurka 1,500, to ma’aikaci a Najeriya bayan kwashe kwanaki 30 yana aiki zai tafi gida da Dalar Amurka $20.

“Yayin da takwarorinsa a 2023 a kasashe irin su Seychelles, Libya, Morocco, Gabon, South Africa, Mauritius, da  Equatorial Guinea suke da  $456, $325, $315, $256, $242, $240, and $224, daya bayan daya. Abin da kowannensu zai samu kenan a karshen kowane wata.”

Ga yadda kiyasin zai nuna idan aka kwatanta da yadda Babban Bankin Najeriya ke canza kudin kasar daga Dala zuwa Naira a ranar 4, ga watan Yuni 2024:

KasasheAsalin kudinA rubanya (sau) N1,474
Seychelles$456₦672,144
Libya$325₦479,050
Morocco$315₦464,310
Gabon$256₦377,344
South Africa$242₦356,708
Mauritius$240₦353,760
Equatorial Guinea$224₦330,176

A ranar 16 ga watan Agusta ma 2023, jaridar The Nation ta fitar da irin wannan bayani (report) Hakanan Business Insider Africa’s report a ranar 4 ga watan Maris, 2024, ta tattaro bayananta daga Wisevoter, ta kuma zayyano Seychelles da Libiya da Marocco a matsayin kasashe da ke a saman teburi da suka fi biyan kudi a matsayin mafi karancin albashin. Wisevoter wani dandali ne da ke tattara bayanai da wasu abubuwa kan mutane da masu zabe da jami’an da aka zaba, DUBAWA ya ziyarci shafin Wisevoter don tabbatar da bayanan da ya gano inda nan ya ga yadda aka bayyana Seychelles a matsayin wacce ke biyan mafi karancin albashi na  $465.4  a duk wata, inda ta kasance ta 38 a duniya, Libiya ita ce ta biyu a Afurka inda take biyan  $321.83 ta kasance ta 45 a duniya, sai kuma Morocco wacce ta zama ta uku tana biyan mafi karancin albashi $314.7 ita ce ta 47 a duniya.

A Karshe

Da’awar cewa babu kasar Afurka da ke biyan  N400,000 a matsayin mafi karancin albashi karya ne kasancewar akwai wadannan kasashe Seychelles, Libya da Morocco duka suna biyan sama da wannan adadi a matsayin mafi karancin albashi.

Wannan rahoto an fitar dav shi ne karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 karkashin shirin kwararrun masu gano gaskiya labari na Kwame Karikari da hadin giwa da Hope Newspaper a kokarin da ake yi na mutunta fadin gaskiya a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a Najeriya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button