African LanguagesHausa

Ba Bukola Saraki ba ne a bidiyon da ya nuna wani dan siyasa na shan duka

Olubukola Saraki wanda aka fi sani da Bukola Saraki dan siyasa ne a Najeriya wanda kuma ya kasance shugaban majalisar dattawa na 13 daga 2015 zuwa 2019. Kafin zaben shi zuwa majalisar dokokin a shekarar 2011, ya yi wa’adi biyu a matsayin shi na gwamnan jihar Kawara.

Kama daga lokacin da ya ke rike da mukamin siyasa, zuwa yanzu da ba shi da wani mukamin gwamnati Saraki ya rika kasancewa a tsakiyar batutuwan da su ka shafi takaddamar siyasa. Yawancin wadannan batutuwan sun shafi zargin cin hanci da rashawa ko da shi ke ya musanta.

Kwanan nan wani bidiyon da ya yadu a shafin Facebook ya yi zargin wai dan siyasar ya ci duka a hannun masu zanga-zanga a titunan Burtaniya. Bidiyon wanda Joy Ese Joshua, mai amfani da shafin Facebook ta wallafa yana dauke da taken da ke bayyana cewa mutumin da ke cikin bidiyon Saraki ne.

“Bukola Saraki ya ci dukan da bai taba ci ba a rayuwarsa a hannun ‘yan Najeriyan da ke zama a Turai, a kan titunwan Burtaniya. Dara ta ci gida.”

Masu amfani da Facebook sun kalli bidiyon sau dubu 70 kuma ya janyo tsokaci sosai da cece-kuce tsakanin jama’a mutane sun kuma sake raba labarain sau dubu 30.

Ba tare da wata shakka dangane da zargin ba, wasu masu amfani da shafin wadanda suka yi tsokaci kan batun sun ce tsohon dan majalisan ya cancanci ya sha dukan, wasu ma har sun tabbatar cewa lallai mutumin da ke cikin hoton Saraki ne lokacin da ya yi tafiya tare da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar zuwa Landan a shekarar 2019.

“Shi ne, amma ba kwanan nan ba ne, shekarar 2019 ne lokacin da ya kai ziyara Landan tare da Atiku,” in ji Michael Ajibola.

Wadansu kuwa irinsu Temitope Akinwumi, kai tsaye suka kira shi labarin karya wato “Fake News.”

A Kulluyaumin ‘yan siyasa na kasancewa cikin labarai masu daukar hankali musamman a lokutan da zabe ke karatowa. Shi ya sa DUBAWA ta dauki nauyin bincika wannan zargin dan gano gaskiyar lamarin

Tantancewa

Lokacin da DUBAWA ta gudanar da bincike kan bidiyon a manhajar InVid, sakamakon binciken ya nuna mana cewa tun ba yau ba ake amfani da hoton bidiyon a kafofi daban-daban kuma duk sadda aka yi amfani da bidiyon, akan danganta shi da wani labarin na daban. 

A Shafukan YouTube da Facebook, an yi amfani da bidiyon wajen fadada zargin cewa wai dan Tinubu ne aka kama aka yi mi shi duka a Landan. Wannan a watan Oktoba ke nan na shekarar 2020 lokacin zanga-zangar #Endsars a Najeriya. 

A wancan lokacin manyan ‘yan siyasa irinsu Tinubu sun sha suka domin an yi ta dora mu su alhakin yawan shekarun da aka shafe ana fama da gurbataccen shugabanci da zaluncin ‘yan sanda.

Wannan hoton bidiyon ne kuma ya sake bayyana a shafin Facebook inda ya sami martanoni daban-daban a shekarar 2019. Wancan lokacin an yi zargin cewa mutumin da ke bidiyon gwamnan Kinshasa a Jamhuriyar Dimokiradiyyar Kwango ne wanda mutanen Kwangon suka kai mi shi hari sadda ya je siyayya a wani kanti a birnin Paris.

“Gwamnan Kinshasa ya je sayayya a Paris. Mutanen shi na Kwangon da ke zama Faransa suka jira shi a waje har ya gama sayayya kafin suka dira a kan shi,” a cewar taken da aka yi wa bidiyon.

A shekarar 2019 kusa da lokacin da bidiyon ya fara fitowa, mambobin al’ummar Kwangon da ke Faransa sun gudanar da zanga-zanga lokacin da shugaba Felix Tshisekedi ya kai ziyara Paris.

Bukola Saraki sananne ne a Najeriya, dan haka ya kamata idan abu haka ya faru a ce ya dauki hankalin kafofin yada labarai. Sai dai ko daya babu wannan labarin a kafofin yada labarai na gargajiya bare taskokin blog na yanar gizo. Wannan ne ya sanya babban alamar tambaya dangane da sahihancin labarin.

A Karshe 

Binciken mu ya nuna cewa tun shekarar 2019 aka wallafa wannan bidiyon kuma sau da yawa ake amfani da shi ana zarge-zarge da shirya labaran karya ba tare da an bayyana mafarin shi na gaskiya ba. Dan haka wannan labarin karya ne. 

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button