African LanguagesHausa

Ba duk dan takaran da Obasanjo ya mara wa baya ne ya ke nasara a zabukan Najeriya ba

Zargi: Wani mai amfani da shafin tiwita, Arch Angel Jesse Halliday (@AaJessejaliday) ya yi ikirarin cewa duk ‘yan takaran da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya mara wa baya ya yi nasara a zaben shugaban kasa.

Ba duk dan takaran da Obasanjo ya mara wa baya ne ya ke nasara a zabukan Najeriya ba

Wannan ba gaskiya ba ne

Cikakken bayani

Najeriya ta shirya gudanar da zabukan gama gari a watan Fabrairun 2023, inda za ta zabi shugaban kasa da mataimakinsa da mabobin majalisun dattawa da na wakilai da na gwamnoni da ma ‘yan majalisar jihohi.

‘Yan takarar shugabancin kasar da ke kan gaba sub gada da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki, Atiku Abubakar na jam’iyyar adawa ta PDP da Peter Obi na jam’iyyar Leba sai kuma Rabi’u Musa Kwankwaso na NNPP.

Al’ada ce ‘yan takara su girmama dattawan kasa, shugabannin gargajiya, ‘yan siyasa da sauransu domin samun goyon baya.

A watan Fabrairun 2022, Atiku Abubakar na PDP ya ziyarci tsohon shugaban kasar wato Olusegun Obasanjo a gidan shi da ke Abeokuta jihar Ogun.

A watan Agustan 2022, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu shi ma ya ziyarci Olusegun Obasanjo.

Haka na kuma a watan Satumban 2022, shi ma dan takarar jam’iyyar Leba ya ziyarci Obasanjon a gidan shi na Abeokuta.

Ranar daya ga watan Janairun 2023, tsohon shugaban Najeriyar, Olusegun Obasanjo, a budaddiyar wasikarsa ta sabuwar shekara ya bayyana dan takarar jam’iyyar Leba Peter Obi a matsayin wanda zai zaba a zaben na watan gobe.

Kwanan nan wani mai amfani da shafin tiwita Arch Angel Jesse Halliday (@AaJessejaliday) ya yi bayanin da ke zargin wai Peter Obi zai ci zabe tun da oasanjo ya mara masa baya.

“Duk wadanda Obasanjo ya taba marawa baya a zaben shugaban kasa ya yi nasara, Baba ya nuna amincewarsa da Peter Obi dan haka Peter Obi zai yi nasara,” ya bayyana. Wanna batun ya dauki hankali sosai bisa la’akari da yawan mutanen da su ka yi ma’amala da labarin shi ya sa DUBAWA ta ga ya dace ta tantance gaskiyar labarin.

Tantancewa

Bisa bayanan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) nasarar kowane zabe ya danganci shirin da aka yi da kuma yadda aka gudanar, misali: tantance wadanda su ka cancanci kada kuri’a, zabe, irga kuri’u hadawa da kuma bayyana sakamako.

A wani rahoton da aka yi a jaridar ThisDay, kwamishan INEC ta kasa mai kula da sashen illimantar da wadanda suka cancanci yin zabe da samar mu su bayanai Barr. Festus Okoye, ya ce wanda zai yi nasara a zaben watan gobe dole sai ya sami mafi yawan kuri’s da kuma kashi 25 cikin 100 na jimilar kuri’un a kashi biyu cikin uku na jihohi 36 da ke tarayyar.

“Bisa bayanin sashe na 34 na kundin tsarin mulkin kasa, inda akwai ‘yan takarar shugabancin kasa fiye da biyu, kafin a tabbatar da wanda ya yi nasara, dole sai ya sami mafi yawan kuri’un da aka kada a zaben da kuma kashi daya cikin hudu na kuri’un da aka kada a kowane akalla kashi biyu cikin uku na duka jihohin kasar da birnin tarayya.”

A zaben shugaban kasa na shekarar 2007 Obasanjo ya goyi bayan tsohon gwamnan jihar Katsina na wancan lokaci wato Umaru Musa ‘Yaradua wanda ya yi nasara.

A 2011 Obasanjo ya goyi bayan Goodluck Jonathan, wanda daga baya ya ci zaben, A zaben da ya biyo baya (Zaben 2015) Obasanjo ya goyi bayan Muhammadu Buhari wanda shi ma ya yi nasara.

Sai dai a shekarar 2019 tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar wanda ya yi takara a inuwar jam’iyyar adawa ta PDP ya sha kaye a zaben bayan da ya yi takara da shugaba Muhammadu Buhari duk da goyon bayan da ya samu daga Obasanjo.

A Karshe

Bisa bayanan da muka yi a sama, ba daidai ba ne a ce duk wanda Obasanjo ya marawa baya ya yi nasara a zaben shugaban kasa

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button