Zargi: wani hoton da ya bazu a shafukan yanar gizo na nuna hotunan zanen yatsu daban-daban wadanda aka kasa gida biyu da zargin rukuni daya na dauke da hotunan yatsu masu inganci a yayin da dayan ke dauke da wadanda su ka lalace

Bincikenmu ya nuna mana cewa duk hotunan zanen yatsun da aka sanya a hoton duk sun halatta, sabanin bayanin da aka yi a kan hoton na cewa wadansu na da inganci amma wadansu sun lalace.
Cikakken bayani
Yayin da zabukan 25 ga watan Fabrairu ke kara kusantowa, za’a cigaba da yin bayanai dangane da zabe domin wayar da kan duk wadanda su ka cancanci kada kuri’a sai dai duk da haka, za’a sami bayanan da za su yaudari jama’a.
Kwanan nan wadansu hotunan zanen yatsu kala-kala su ka bayyana kuma aka rika rabawa a WhatsApp, Tiwita, da Facebook dangane da hotunan zanen yatsu masu inganci da marasa inganci.
Bisa bayanan da aka wallafa da hoton, bayan an dangwali tawadan, zanen yatsun da ke cikin wurin da aka kebe dan danna yatsosti a gaban tambarin jam’iyya ne kadai za su kasance da inganci, amma da zarar yatsun su ka fita ko kuma suka taba layin kuri’ar ta lalace ke nan.
Yayin da wadansu su ka amince da wannan zargin har sun cigaba da rabawa da abokai, wadansu masu amfani da Tiwita sun nuna rashin amincewarsu da zargin wai inda aka dangwala yatsa zai lalata kuri’a, inda su ka yi bayanin cewa kuri’ar za ta lalace ne kadai idan har aka gaza gane daidai wurin da aka dangwala yatsar.
Mahimmanci wannan batun da bukatar tantance rudanin da ya ke janyowa ne ya sa DUBAWA za ta duba wannan batun.
Tantancewa
Mene ne mahimmancin hoton zanen yatsa?
Zanen yatsa alama ce ake yi da tawada a bayan babban yatsa daga sama. Yana dauke da alamu na musamman wadanda ke banbanta kowane dan adam.
Kashi na hudu sashi na 52 karamin sashe na biyu na dokar zabe na 2022 ya ce Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta za ta yi amfani da tawada irn wanda ba ya fita da wuri, wajen sanya alama a zanen hannun da masu zabe za su dangwala a kan katunan zaben.
Karamin sashi na daya na wannan bangaren ya ce “a inda mai zabe ya yi wani rubutu ko ya sanya alama a kan takardar zabe saboda a gane shi ko ita, dole ne a yi watsi da wanann takardar idan dai har abin da aka sanya a wurin da aka tanadar na dangwala yatsar bai yi kama da irin alamar da ake bukata ba.
Da wace yatsa ake dangwalawa?
INEC ta fayyace cewa ana iya amfani da kowane yatsa a dangwala a zaben gama garin.
Bisa bayanin da aka yi a kundin bayanan ayyukan INEC, wajibi ne a sanya tawada daga kasar kunbar yatsar da aka yi amfani da ita wajen dangwalawar.
Lokacin zaben gama gari, ana iya sanya tawadar a kowanne daga cikin yatsu biyar din da aka zaba amma idan irin zaben da za’a yi shi kadai ne za’a sanya alamar a kasar kumban babbar yatsar hannun hagu ne.
Yaya ya kamata a dangwala yatsar?
Mun tuntubi kwamishanan INEC kan labarai, Festus Okoye, wanda ya bamu kundin bayanan hukumar na 2022 wanda jami’an zabe ke amfani da shi.
Bisa bayanan wannan kundi, zanen yatsun da aka dangwala a tsakiyar tambarorin jam’iyyu biyu ne ko kuma inda aka zabi tambarori da yawa a maimakon guda daya kamar yadda ya kamata, za’a iya cewa kuri’ar ta lalace.
A daya hannun kuma, zanen yatsun da aka sanya a wurin da a kebe dan dangwala yatsun, da wanda aka sa a kan tambarin jam’iyyar ko kuma a tsakiyar tambarin da wurin da aka kebe dan dangwala hannu duk halatattu ne ba abin da ya same su.
Tsarin tafiyar da zaben a ranar jefa kuri’ar
Jefa kuri’a a runfunan zaben a ranar zai bi wannan tsarin:
Mataki na 1 – shiga layi a runfar zabe inda jami’an INEC za su tabbatar mu ku cewa kuna wurin da ya dace su kuma tantance katin zaben da ku ka gabatar shi ma su tabbatar na ku ne.
Mataki na 2 – Jami’in INEC zai karbi katin da kuka gabatar ya yi amfani da na’urar karanta katin ya tabbatar cewa katin ba jabu bane. Za’a bukace ku ku sanya yatsa guda a kan na’urar karanta sahihancin katin.
Mataki na 3 – Jami’in INEC zai karbi katin zaben ku ya tabbatar ko sunayenku na cikin babban jaddawalin sunayen wadanda su ka cancanci kada kuri’a. Bayan nan za’a sanya alama a sunayen ku sai a shafa muku tawada a daya daga cikin yatsun ku.
Mataki na 4 – Shugaban zaben a wannan runfan zai buga hatimi, ya sanya alama ya kuma amince da takardar zaben. Daga nan za’a ba ku takardar zaben a nannade da inda aka yi rubutun ta ciki sai a tura ku zuwa killataccen wurin da za ku iya dangwalawa ku zabi jam’iyyar da ku ke so.
Mataki na 5 – Da zarar ku ka shiga wurin zaben, sai ku dangwali tawadar ku danna yatsa ku zabe dan takarar da ku ke so ku zaba, bayan haka sai ku ake nannade takardar kamar yadda aka ba ku.
Mataki na 6 – Ku bar dakin jefa kuri’ar ku je ku sanya takardar a cikin akwatin zaben a bainar jama’a
Mataki na 7 – Ku bar runfar zaben ko kuma ku jira idan ku na so, cikin oda da lumana, dan kallon yadda za’a tafiyar da zaben har zuwa sadda za’a sanar da sakamakon
A karshe
Bincikenmu ya nuna mana cewa duk hotunan zanen yatsun da aka sanya a hoton duk sun halatta, sabanin bayanin da aka yi a kan hoton na cewa wadansu na da inganci amma wadansu sun lalace.