African LanguagesHausa

Buhari ya nuna amincewarsa da takarar Tinubu a gangamin zaben jam’iyyar a Adamawa, wanda ya saba wa zargin wani mai amfani da tiwita

Zargi: Shugaba Muhammadu Buhari bai amince da takakarar Bola Ahmed Tinubu na kujerar shugabancin kasar a karkashin inuwar jam’iyyarsa ta APC lokacin gangamin da su ka yi a jihar Adamawa ba

<strong>Buhari ya nuna amincewarsa da takarar Tinubu a gangamin zaben jam’iyyar a Adamawa, wanda ya saba wa zargin wani mai amfani da tiwita</strong>

Zargin wai shugaba kasa bai marawa takarar Tinubu baya ba, ba gaskiya ba ne, domin bincikenmu ya nuna mana cewa Buhari ya goyi bayan takarar Bola Tinubu.

Cikakken bayani

Jam’iyyar APC ta kaddamar da yakin neman zabenta a birnin Yola, jihar Adama ranar litini 9 ga watan Janairun 2023. Sa’anan a karon farko tun bayan da jam’iyyar ta fara gangamin zaben a birnin Jos na jihar Filato a bara, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarta.

Sa’o’i kadan kafin kaddamar da yakin neman zaben, wata mai amfani da shafin Tiwita NKEM #PeterObi2023(@Nkemchor) ta ce shugaba Muhammadu Buhari bai amince da takarar wanda ke neman shugabancin kasar a karkashin jam’iyyarsa ba wato Bola Ahmed Tinubu.

Mai shafin ta danganta wannan zargin na ta da wani bidiyo mai tsawon minti daya da dakiku biyu wanda aka nada a taron gangamin wanda ta samo daga wani shafin tiwitan na @MuchTalksBlog1, na wani mai suna Chinaza #PeterObi-HypeMan.

Kafin gangamin na Yola, wasu sun rika rade-radin cewa shugaba Muhammadu Buhari na kaucewa daga yi wa dan takarar jam’iyyar ta sa kamfe ne sakamakon wadansu shakkun da ake kyautata zaton ya na da su, abin da ya janyo zargin cewa ba haka kawai ne ake sa tafiye-tafiyen shugaba Buharin a dai-dai lokacin da jam’iyyar za ta je yakin neman zabe ba.

Domin sarkakiyar da irin wannan batu ya ke da shi musamman a lokacin zabe, da ma yadda batun ya dauki hankalin jama’a DUBAWA ta ga ya dace a tantance gaskiyar lamarin

Tantancewa

 Mun fara da binciken mahimman kalmomi wanda ya nuna mana cewa Buhari ya nuna amincewarsa da takarar Tinubu lokacin gangamin da aka yi a Yola. Wani bidiyo mai tsawon sa’a guda da mintoci 23 na gangamin jam’iyyar ta APC da mu ka gano a YouTube, wanda gidan talibijin na TVC ya sanya da ma gajejjerun da Channels da TV360 su ma su ka sa a shafin duk sun yi bayanin yadda shugaba Buhari ya nuna goyon bayansa ga Tinubu har ma ya nemi jama’a da su mara mi shi baya, da shi da abokin takararsa Kashim Shettima.

Haka nan kuma, shugaba Buharin a shafin na Tiwita ya sanar da dan takarar shugaban kasar na APC da abokin takarar ta sa a matsayin mutane masu rikon amana.

Bincikenmu bai kai mu ga rahotanni daga kafofin yada labarai masu nagarta da su ka amince da zargin ba.

Yayin da muka kalla mu ka kuma saurari dogon shirin gangamin da aka yi a Adamawa, mun kula cewa bidiyon da Nkemchor_ ya wallafa ya mayar da hankali ne a kan abin da shugaba Buhari kadai ya fada. Wanda ya hada bidiyon ya yanki wannan barin ne kadai domin ya fadada na sa manufofin.

A bidiyon mai tsawon sa’a guda da minti 23 wanda gidan talibijin na TVC ya wallafa a YouTube, mun ji shugaba Buhari yana cewa ya na jihar Adamawa ne domin ya gabatar da dan takarar mukamin shugaban kasa a jam’iyyarsa, Bola Tinubu ( Ya yi hakan ne yayin da ya ke daga hannun dan takarar) da dan takarar mukamin gwamna, Aishatu Binani. Bayan haka ne ya mika tutar jam’iyyar ga wa kowanne daga cikin ‘yan takaran biyu. Sa’annan ya kara da kira ga jama’a da su zabi APC, inda ya bayyana abubuwan da za su amfani jam’iyyar. Daga bisani kuma ya kara da kwatanta irin ‘yan takaran da ya dace wadanda su ka cancanci kada kuri’ar su zaba.

Shawarar da ya bayar kan irin ‘yan takaran da ya kamata a zaba ne aka yi amfani da shi a bidiyon da aka wallafa a shafin Tiwita.

Shugaba Buhari ya kuma yi magana da harshen hausa. Jawabin wanda wani ne ya fassara zuwa Hausar ya bayyana cewa shugaban kasar ya yi kira ga jama’a da su zabi Tinubu domin zai aiwatar da burin jam’iyyar. Ya kuma bukaci mutane su jefawa ‘yar takarar gwamnan a jihar Adamawa kuri’ar su.

A Karshe 

Zargin wai shugaba kasa bai marawa takarar Tinubu baya ba, ba gaskiya ba ne, domin bincikenmu ya nuna mana cewa Buhari ya goyi bayan takarar Bola Tinubu.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button