African LanguagesHausa

Ba Marigayiya Osinachi ce a bidiyon da wani ke dukar wata mata da dutsen guga ba

Zargi: A wani bidiyon da ake ta yadawa inda wani mutumi ke dukar wata mata da dutsen guga, ana zargin wai irin cin zarafin  da mijin Osinachi, mawakiyar nan mai rasuwa, ta rika jurewa a aurenta ke nan da mutumin da ya yi sanadiyyar ajalinta.

Shafukan soshiyal mediya sun shiga wani yanayi na cece-kuce inda mutane suka rika mahawara suna bayyana ra’ayoyi mabanbanta sadda aka sanar da rasuwar Osinachi Nwachukwu,  shahararriyar mawakiya irin na bishara. 

Bayan rasuwar Osinachi wadda ta kasance jagorar mawakan cocin da aka fi sani da Dunamis, daga farko an ce cutar daji ta makogwaro (cancer) ce ta yi ajalinta. To sai dai daga baya bayanai da dama  daga ‘yan uwa da abokan arziki su ka bayyana a shafukan soshiyal mediya wadanda su ka karyata hakan su ka yi zargin cewa mijinta ne ya kashe ta garin irin duka da cin zarafin da ya rika mata a gidan auren.

Sakamakon wannan labarin, wani sabon bidiyo ya bulla a WhatsApp da sauran shafukan soshiyal mediya. Bidiyon ya nuna wani mutumi a fusace yana dukan wata mata da dutsen guga. Ita kuma matan wadda ta riga ta jigata tana ta ihu a gaban kananan yara tana kuka. Ana cikin haka mutumin zai kai mata wani dukan sai ta ruga, ya ko bi ta a guje zuwa wani daki. Inda bidiyon mai tsawon sakon 11 ya tsaya ke nan.

Jama’a na zargin wai mutumin cikin bidiyon mijin Osinachi ne ya ke nakada mata duka, sa’annan bayanin da ke kan bidiyon ya nuna cewa daya daga cikin yaranta maza ne ya nadi bidiyon.

“Bidiyon mijin Osinachi yayin da ya ke dukanta, dan ta ne ya nada. Yaya za’a yi a ce namiji na dukan matarsa haka, matar da ta haifi yaranka, yaya za’a yi wannan dolon ya ce ba shi da hannu a kisar matarsa Osinachi. Mr Peter Nwachukwu,” a bayanin da taken ya yi.

A daya daga cikin dandalolin WhatsApp inda aka sanya bidiyon, wadansu sun nuna takaicinsu da mijin Osinachi suna kiran shi “shaidan” da kuma “mai dutsen guga” saboda dukan da yayi da dutsen guga.

“Wannan mutumin shaidan ne. Yaya za’a yi ka duki matarka da dutsen guga? Ba abin mamaki ba ne yadda ta hallaka. Allah sa ta huta,” a cewar wani mai amfani da shafin.

Tun bayan da Osinachi ta rasu ake samun bayanai mabanbanta, wadansun su ko daya ba su da tushe. Wannan ba sabon abu ba ne musamman idan labari na da sosa rai, sai dai wadansu kan yi amfani da wannan damar su rika baza karya dan haddasa tsoro da fushi a zukatan mutanen da ke al’ummar.  

Tantancewa

Da DUBAWA ta fara tantance bidiyon a manhajar InVid wanda ke gano asalin hotunan bidiyo, smun gano cewa tun shekarar 2020 aka yi bidiyon dangane da wani batu na daban wanda kuma ba shi da wata alaka da ita mawakiyar mai rasuwa. 

Hasali DUBAWA ta bi diddigin bidiyon inda ta gano cewa ya fara bayyana a Tiwita ne a shafin wani mai suna David (@davidnart) wanda ya wallafa bidiyon ranar 21 ga watan Yunin 2020 da taken:

“Mugunta mai tsanani ne mutumin nan ke yi. Ina fata zai sami hukuncin rai da rai. Mugu kawai.”

Banda haka, wata mai amfani da shafin Tiwitan da sunan Zußy (@zubykelz) ta sake sanya labarin a shafinta ranar 31 ga watan Yunin 2020 tana bayar da labarin cewa matar da ke bidiyon na zargin mutumin da ke dukanta da yi mata fyade ne ba cin zarafi a cikin aure ba.  

“Kamar ‘yan Najeriya ba su iya banbanta cin zarafi ta hanyar duka a gidan aure da fyade ba. Domin fayyace wannan batun… wannan bidiyon batun cin zarafi da duka ne kuma ba ta zarge shi da haka ba, ta zarge shi da fyade ne. Sai dai ba ta taba fada mana wani abu kan fyade ba,” a cewar taken labarin.

Wannan bidiyon ne aka sake wallafawa a wani rahoto a shafin jaridar Pulse.ng ranar 23 ga watan Yunin 2020 da taken

“Bidiyo mai daukar hankali na wani mutumin da ke dukar matarsa da dutsen guga a gaban kananan yaransu ya tayar da hankalin masu amfani da soshiyal mediya.”

Rahoton ya bayyana yadda mutumin da ke cikin bidiyon, (wanda ba’a san ko shi wane ne ba) ke dukar wata mata da dutsen guga. Amma kuma a cikin duk shafukan da aka wallafa bidiyon a shekarar 2020 babu inda aka ambato sunan Osinachi, wato mawakiyar mai rasuwa.

A Karshe

Wannan bidiyon tun shekarar 2020 aka yi shi kuma an dade ana wallafa shi a shafuka daban-daban da labarai iri-iri kuma babu inda aka ambato Osinachi da mijin ta a wancan lokacin. Dan haka wannan zargin karya ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »