African LanguagesHausa

Shin shan ruwa a daidai lokacin da ake cin abinci na da lahani?

Zargi: Wani mai amfani da shafin tiwita na zargin wai shan ruwa yayin da ake cin abinci na da hadari ga jikin dan adam.

Wani mai amfani da shafin tiwita mai suna Sirwoley (@SirWoley) kwanann nan ya yi zargin cewa bai dace mutun ya sha ruwa a lokacin da ya ke cin abinci ba domin yin hakan na da lahani ga jiki. Ya ba da shawarar cewa ana iya shan ruwa minti 30 kafin a zauna cin abinci ko kuma sa’a guda bayan an gama.

“Yanzun nan na ji cewa wai shan ruwa a lokacin da ake cin abinci ba kyau. Dan haka sai dai a sha ruwa minti 30 kafin a fara cin abincin ko kuma sa’a guda bayan an gama,” ya rubuta.

Wani shi ma mai amfani da tiwitan Ayo Bami (@olufowose_ayo) ya yi tsokaci dangane da batun ya goyi bayan hakan, ya kuma kara da cewa cin abinci ba ruwa ma na da wahala. 

Wata mai suna Sweet Nectar (@Lily_retta) kuwa tambaya ta yi cewa a fada mata tushen zargin.

“Wannan gaskiya ne amma dai yana da wahala,” in ji @izu_sylva. ODINAKA (@solomonOdinaka2) wani mai amfani da tiwitan shi ma ya karfafa zargin.

Ganin cewa wannan zargin na @SirWoley wanda ke da ma’abota 18,000 a shafin tiwita ya ja hankalin mutane da yawa kuma har wasu sun yi tsokaci a kai ya sa DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiyar wannan zargin.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da binciken mahimman kalmomi abin da ya nuna cewa jaridar USA Today ta taba binciken wani batu makamancin wanann a shekarar 2020 inda ta karyata zargin.

Shi ma shafin Healthline wani shafin kiwon lafiya da ya yi suna sosai ya ce akwai jayayya guda uku da mutane kan yi wajen yin zargin cewa shan ruwa lokacin da ake cin abinci na iya janyo illa ga cikin mutum.

Na farko shi ne shan giya ko wani abin da ke da giya a ciki lokacin da ake cin abinci kan sa yanwu ya bushe, idan haka ya faru kuma sai jikin mutun ya gaza narkar da abinci. Yawan yawun mutun kan ragu da kusan kashi 10 zuwa 15 cikin 100 a duk sadda mutun ya kurbi giya. Sai dai wannan ya shafi irin giyan nan mai karfin gaske ba kamar giyan kwalba wanda akan sarrafa da hatsi ko inabi ba, bisa bayanan wani binciken da PubMed Central ta wallafa. 

Na biyu kuma shi ne idan aka sha ruwa yayin da ake cin abinci, a kan surka sinadaran da suke taimkawa wajen narkar da abinci, dan haka sai narkewar abincin ya zo da wahala. A cewar binciken PubMed Central, ruwa kan shiga ya fita cikin mutun da sauri idan aka kwatanta da yawan lokacin da abinci mai nauyi zai dauka kafin ya fita daga jikin mutun. Dan haka ruwan ba shi da wani tasiri kan tsawon lokacin da abinci zai dauka kafin ya narke.

Na ukun kuma wanda aka fi sani shi ne idan ana cin abinci da ruwa a lokaci guda, nan da nan abincin zai fita daga cikin mutun

Haka nan kuma wani binciken ya sake karyata zargin cewa wai kaurin abinci ko yawan ruwan da aka sha zai yi tasiri kan sinadaran da ke taimakawa wajen narkar da abincin da ke cikin mutun.

A waje guda kuma, wani shafin Indiya mai suna Entertainment Times ya rawaito cewa shan ruwa lokacin da ake cin abinci na da illa.

Wadannan ra’ayoyi mabanbanta da muka gani, ya sai mu ka yanke shawarar tambayar kwararru.

Ra’ayoyin Kwararru

Adedeji Moses, kwararre kan abinci mai gina jiki wanda kuma shi ne darektan Adedamz Nutrition Consult ya bayyana mana cewa jikin mutun na iya shan ruwa a ko da yaushe, wato  ko a lokacin da ake cin abinci ko kafin a ci ko bayan an gama. 

“Babu wani banbanci ko da an sha ruwa kafin a ci abinci ne ko bayan an gama. Shan ruwa yayin cin abinci ba shi da wata alaka da yadda cikin mutun ke narkar da abinci,” a cewarsa.

Emmanuel Oyebamiji, shi ma kwararre ne kan abinci mai gina jikin a asibitin koyarwa na Ibadan wanda shi ma ya ce ana iya shan ruwa lokacin da ake cin abinci.

“Ko da shi ke akwai wadanda ke cewa idan mutun ya sha ruwa a lokacin da ya ke cin abinci, ruwan zai zauna inda ya kamata abincin ya shiga, amma wannan ba gaskiya ba ne, ana iya shan ruwa duk sadda ake so ko da kuwa sadda ake cin abinci,” ya ce.

A karshe

Bincike ya nuna cewa shan ruwa sadda ake cin abinci ba shi da wani lahani. Kwararru ma sun ce shan ruwa tare da abinci ba shi da lahani. Dan haka wannan zargin ba gaskiya ba ne. 

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button