African LanguagesHausa

Babban taron fid da gwani na APC: Alkaluman da ke nuna yawan kuri’un da Tinubu ya samu daga kowace jiha na bogi ne

Zargi: Wani labarin da Joe Igbokwe, jigo a jam’iyyar APC mai mulki ya wallafa ya yi bayani dalla-dalla na yawan kuri’un da tsohon gwamnar jihar Legas Bola Ahmed Tinubu ya samu a kowace jiha lokacin babban taron fid da gwanin (convention) da jam’iyyar ta yi a Abuja

Babban taron fid da gwani na APC: Alkaluman da ke nuna yawan kuri’un da Tinubu ya samu daga kowace jiha na bogi ne

Wannan zargin ba gaskiya ba ne. An jefa kuri’un cikin sirri ne kuma ba’a a yi amfani da jihohi wajen irga kuri’un ba

Cikakken labari

Bayan jam’iyyar APC ta zabi Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda zai yi takarar kujerar shugabancin kasar a zaben 2023 da ke tafe, wasu masu amfani da soshiyal mediya a ciki har da daya daga cikin jigogin jam’iyyar APC a Legas na yada bayanan da ke nuna yadda wakilai ko kuma delegates a kowace jiha su ka zabi Tinubu

A lokacin zaben fid da gwanin, Tinubu ya yi nasara da kuri’u 1271, inda ya doke abokan hamayyan da suka hada da Rotimi Amaechi, Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan da sauransu.

Domin nuna murna, wasu magoya bayan Tinubu su ka raba alkaluman da ke bayyana kason kuri’un da dan takarar ya samu daga kowace jiha.

Bayanin wanda aka bayyana a karkashin rukunan yankunan kasar ya kunshi sunayen jihohin da kason kuri’un da suka sanya.

Ko da shi ke da yawa sun yarda da sakon, akwai wadanda ke sanya alamar tambaya kan inda Igbokwe ya sami labarin da ma sahihancin shi. Shi ya sa DUBAWA ta dauki nauyin gano gaskiya.

Tantancewa

DUBAWA ta gano cewa delegates din da aka zaba da wadanda suka cancanci jefa kuri’a sakamakon matsayin da su ke da shi a jam’iyya ne kadai suke da damar yin zabe a babban taron. Dan haka a jimilce, mutane 2,260 ne kadai suka cancanci kada kuri’a a matsayin delegates.

Daya daga cikin hotunan bidiyon taron da DUBAWA ta samu sun nuna masu zaben suna jefa kuri’unsu cikin kwalaye 40 din da aka tanadar a filin zaben.

DUBAWA ta kuma gano cewa babu kwalin da aka ajiye da sunan jihohi kowa ya jefa a inda ya ke so ne dan haka babu yadda za’a iya tantance jihohin da delegate din ya fito.

Haka nan kuma zaben na sirri dan haka ba wanda zai san na wani idan dai ba shi ne ya fito ya nuna ba.

Kamus na turanci wanda kamfanin buga litattafai na Cambridge ya buga ya kwatanta zaben sirri a matsayin “salon zaben da ya tanadi masu zabe da su rubuta dan takarar da su ke so a kan dan takarda su rufe kafin su jefa a wurin da aka tanadar ba tare da wani ya san zabin su ba.”

Mun yi nazarin yadda aka gudanar da zaben cikin bidiyon da muka samu, wanda ya nadi yadda aka gudanar da zaben fid da gwanin bisa wannan karin bayanin da muka samu kuma mun ga cewa babu yadda za’a san jihohin ko kuma ma yawan mutanen da suka jefa kuri’a daga wata jiha domin kowa ya jefa kuri’arsa ne a cikin sirri kuma a cikin duk kwallin da ya zaba daga cikin kwaleya 40 din da aka girke dan karbar  kuri’un.

A Karshe

Bayanin da aka fitar ana zargin wai yawan kuri’un da Tinubu ya samu daga jihohi ke nan karya ne. DUBAWA ta gano cewa an yi amfani da salon zaben sirri ne kuma ba’a jera kwalayen karbar kuri’u da sunan jihohi ba.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button