African LanguagesHausa

Da gaske ne! Mawaka za su yi wasa a dandalin Eagle Square dan fadakar da jama’a kan rajistan zabe da PVC

Zargi: Masu amfani da WhatsApp na zargin wai hukumar zabe ta INEC, za ta yi wa wadanda ba su riga sun karbi katunan zabensu ba, rajista tsakanin ranakun 20 zuwa 25 na watan Yuni a dandalin Eagle Square kuma a wadannan ranakun ta gayyato mawakan da za su kayatar da mahalarta

Da gaske ne! Mawaka za su yi wasa a dandalin Eagle Square dan fadakar da jama’a kan rajistan zabe da PVC

Bincikenmu ya tabbatar ma na cewa lallai za’a yi rajistan zabe a dandalin Eagle Square kuma mawaka za su kasance a lokutan da hukumar INEC din za ta yi rajistan, wato daga ranakun 20 zuwa 25 na watan Yunin

Cikakken labari

Hukumar Zabe mai Zaman Kanta, INEC, tare da hadin gwiwar kungiyar YIAGA Africa, da Kungiyar Tarayyar Turai suka gudanar da wani gagarumin bikin rajistan katin zabe wato PVC a dandalin Tafawa Balewa da ke jihar Legas ranar asabar 12 ga watan Yunin 2022.

Daga bisani an gudanar da wani kamfen da ke fadakar da matasa dangane da mahimmancin kuri’unsu a zabukan Najeriyar tun daga ranakun 6 zuwa 10 ga watan Yunin. Burin wannan gangami dai shi ne fadakar da al’ummar ba ki daya musamman matasa kan mahimmancin shiga a dama da su a tsarin zabukan kasar.

Kwanan nan wani sako na daban ya sake bulla a WhatsApp inda jama’a a manhajar su ke sanar da ‘yan uwa da abokan arzikinsu cewa INEC da kawayen na ta za su sake shirya wani bukin makamancin wannan a dandalin Eagle Square da ke Abuja daga 20-25 June.

Tantancewa 

DUBAWA ta fara da binciken mahimman kalmomi wanda ya kai ta ga rahotannin da ke sanar da bukin da aka yi a Legas a jaridun The Guardian, The Nation, Vanguard da kuma Business Day amma babu wani abu dangane da Abuja.

Haka nan kuma ba mu ga wani abun da ke sanar da bukin a shafin tiwita na hukumar ta INEC ba. Har wa yau, babu komai kuma a shafin ta na yanar gizo, dan haka sai muka tuntubi  kwamishanan yada labarai da wayar da kan masu zabe Mr Festus Okoye.

Mr. Okoye ya tabbatar mana da labarin inda ya ce za’a gudanar da bukin ranar asabar 25 ga watan Yuni ne bayan an kammala rajistan zaben wanda za’a fara daga 20 ga wata har zuwa 24 ga watan Yunin.

“Bukin mawakan na rajistan katin zabe zai fara ranar litinin 20 ga watan Yunin 2022, za’a yi wakokin ranar 25 ga wata a dandalin Eagle Square.”

Kungiyar YIAGA Africa ma ta sanar da hakan a shafinta na tiwita ranar talata da rana, tana amfani da kalmomin da kwamishanan INEC din ya yi. Mun kuma ga sanarwar a shafin shirin Kungiyar Tarayyar Turai na tallafawa shugabancin dimokiradiyya a Najeriya (@EU_SDGN)

A Karshe

Bincikenmu ya nuna mana cewa labarin fadakarwa dan rajistan katin zabe da bukin da za’a yi da zarar an kammala rajistar gaskiya ne, kuma za’a yi shi ne daga 20 zuwa 25 na watan Yunin 2022

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button