African LanguagesHausa

Babu hujjar cewa Mark Zuckerberg ya gargadi masu amfani da shafin Facebook da su daina daukar hotunan sakonninsu wato chats

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da soshiyal mediya, Emmanuel Hush Seoh ya wallafa wani labari a shafin Shaking Table Association da ke Facebook ya na cewa wai  Mark Zuckerberg ya yi gargadi kan daukar hotunan chats a shafin Facebook

Babu hujjar cewa Mark Zuckerberg ya gargadi masu amfani da shafin Facebook da su daina daukar hotunan sakonninsu wato chats

Hukunci: Babu hujjar da ke tabbatar da cewa Mark Zuckerberg ya yi irin wannan gargadin. Bincikenmu ya nuna mana cewa IGV ne suka fara wallafa wannan da’aawar. Sai dai duk da haka, su kansu ba su bayyana tushen labari ba ko kuma dai wata majoya sahihiya inda suka dauko labarin.

Cikakken bayani

Facebook na zaman daya daga cikin dandalolin sadarwar da aka fi amfani da su a duniya baki daya. Masu amfani da shafin na iya sada zumunta da ‘yan uwa da abokan arziki cikin sauki. Haka nan kuma ana iya amfani da shi wajen yada bayani, ilimi da nishadi.

To sai dai ranar 18 ga watan Afrilun 2024, wani Emmanuel Hush Seoh, ya wallafa wani bayani a kan shafin Shaking Table Association inda ya ke da’awar cewa shugaban Facebook Mark Zuckerberg ya gargadi mutane kan su daina daukar hotunan sakonninsu.  

A cewar Seoh cwannan mataki ne mai kyau wa mutanen Laberiyan da ke amfani da shafin.

“Mark Zuckerberg ya gargadi masu amfani da shafin Facebook kan daukar hotunan sakonninsu. Wannan na da kyau, musamman wa al’ummar Laberiya,” ya bayyana.

Wannan labarin ya ja hankalin jama’a, mutane 41 sun yi ma’amala da shi wasu 32 sun yi tsokaci kan labarin a sadda muke rubuta wannan labarin.

A cikin wani sakon da aka rubuta, wasu sun karyata batun suna kiran shi danne hakkin fadar albarkacin baki a bangaren Mark Zuckerberg, wasu kuma kai tsaye suka ce karya ce ba zai taba yiwua a ce hakan ba.

No evidence Mark Zuckerberg warns Facebook users not to screenshot chats

Wadannan ra’ayoyi mabanbantan ne suka sa DUBAWA gudanar da bincike. 

Tantancewa

Wajen tantance wannan da’awar. DUBAWA ta yi amfani da manhajar tantance hotuna na Google Reverse Image dan gano asalin wannan labarin. Bincikenmu sai ya nuna mana cewa an fara wallafa batun ne a shafin IGV, Innovative Global Vision da turanci wanda wani shafi ne na talla, ranar 23 ga watan Fabrairun 2024, kafin aka sake sabunta shafin da wasu karin bayanan ranar 19 ga watan Afilu.

Cikin labarin da suka wallafa ba su bayyana inda Mark Zuckerberg ya yi wannan bayanin ba. 

Dan haka ne mai wannan binciken ya tuntubi kamfanin na Meta wadda ta mallaki Facebook da sauran shafukan sada zumuncin dan jin ta bakinta amma ba ta sami amsa ba ko bayan da aka tura sakonnin imel da dama. To sai dai da aka duba shafukan Mark Zuckerberg wadanda ya ke amfani da su a hukumance mun kura cewa babu wani gargadi makamancin wannan domin idan da da gaske ya fada tabbas zai sanya a shafukansa wadanda aka tantance kamar wannan na Facebook page da Instagram alhali kuma babu batun a cikinsu

Da muka sake duba shafin  Facebook, ko daya babu labarin ma samsam. 

A Karshe

Bincikenmu ya nuna mana cewa babu hujjojin da za su iya tabbatar da sahihancin wannan batun.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button