Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: wani mai amfani da shafin X ya wallafa hoton wasu mutane suna tserewa daga matsugunnensu tare da da’awar cewa karamar hukumar Zurmi ce a jihar Zamfara

Hukunci: Yaudara ce. Tsohon bidiyo ne kuma ba a Najeriya ya faru ba
Cikakken bayani
A ‘yan kwanakin baya-bayan nan, wani bidiyo ya bulla wanda ya ke nuna mutane da yawan gaske suna barin wani wuri kamar masu hijira, kuma an yada bidiyon sosai a kafofin sadarwa na soshiyal mediya. Ranar 16 ga watan Mayun 2024, wani mai amfani da shafin X da sunan Erimus (@FirstObidient) a wallafa wani bidiyo wanda ke da’awar cewa mutanen na barin matsugunnensu ne a karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara.
Tare da wannan bidiyon mai tsawon dakiku 29, akwai taken da ke bayyana damuwa kan rashin martani ko mataki daga wajen gwamnati ko fadar shugaban kasa tun bayan barkewar wannan rikicin. Taken ya yi bayani kamar haka “BREAKING (LABARAI DA DUMI-DUMI): Iyalai na tserewa suna barin matsugunnensu a Karamar Hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara bayan da ‘yan ta’adda suka kai hari kan al’ummominsu suka yi awon gaba da mutane 500. Kawo yanzu babu wani martani daga gwamnan jihar bare fadar shugaban kasa.”
A lokacin da muka fara rubuta wannan labarin, bidiyon ya dauki hankali sosai, inda alkaluma suka nuna mana cewa an kalla sau 75,000 sa’annan kuma an yi tsokaci kusan 615 a kafofin sada zumunta da dama.
Daga cikin irin martanonin da aka maida, Stride Networks (@NetworksStride) ta sanya alamar tambaya kan sahihancin bidiyon. Mai amfani da shafin na X cewa ya ui “wadannan mutanen tserewa suke yi ke nan abi.. Ke nan mutumin da ke tserewa daga abun da ke da mummunar hatsari haka ya ke tafiya ke nan, to ku cigaba…” yayin da wasu kuma irin su Viva XY (@VivaDido), kai tsaye suka fara sukar gwamnati, musamman saboda gazawarta a matsalar tsaron da kasar ke fama da ita, “gwamnatin da ta gaza. Tsarin da ya gaza.” wani kuwa, shi ma mai amfani da shafin AAW.(@vicayz) AAW. Ya yi shakkun wurin da ake zargi abu na faruwa, wanda kuma ya janyo mahawara tsakanin wadanda suka kalla bidiyon. Mai amfani da shafin na X rubutawa ya yi cewa “Babu wani abu cikin bidiyon nan da ya nuna cewa Najeriya ce. Ko adi ni ne ban kalla da kyau ba.”
Bacin haka, an wallafa wannan bidiyon amma an gajarta shi an kai shi dakiku 13 a shafin Serah Ibrahim (@TheSerahIbrahim) kamar haka ana jaddada yawan mutanen da ake zargi an kwashe, inda ake cewa mutane 500 aka dauka. A nan ma taken da aka wallafa da bidiyon ya jaddada rashin martani daga mahukuntan jihohi da na tarayya, tare da nanata mahimmancin daukar mataki na gaggawa. Taken ya yi bayani kamar haka “BREAKING: Ba mutun daya ko biyu ko 50 ba, mutane 500 aka kwashe daga karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara. Ko uffan ba mu ji daga wajen gwamnoni ko fadar shugaban kasa ba. Iyalan da ke rayuwa a kewaye da yankin ne suke tserewa daga maharan zuwa wani wurin da ba’a san ko ina ne ba.”
Yayin da muke hada wannan rahoton mun lura cewa masu amfani da shafukan soshiyal mediya sun yi ma’amala sosai da labaran domin an kalla sau 498,000 bisa alkaluman da ke kan bidiyon abin da ke nuna cewa mutane sun firgita suna ta yayata bidiyon dan jan hankalin mahukunta su yi wani abu a kai, a can a jihar ta Zamfara.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da binciken yanar gizo da mahimman kalmomin da ke da alaka da Zamfara da tsaro amma ba ta sami wani bayani ba.
Daga nan sai ta yi amfani da InVID plugin, wata manhajar da ake amfani da ita wajen tantance mafarin bidiyoyi, inda ta gano cewa bidiyon ya dade yana yawao a yanar gizo tun shekarar 2021 kuma ba Najeriya ba ce.
Bincike ya nuna cewa an fara daukar bidiyon ne lokacin wani harin da aka kai kan kauyen Solhan da ke Burkina Faso a shekarar 2021, inda ‘yan bindiga suka kashe fararen hula da dama suka kuma daidaita mazauna. Haka nan kuma mun gano cewa ba ma a Najeriya kadai ba, masu son tayar da zaune tsaye sun dade suna amfani da bidiyon a kasashen Afirka da dama dan yada bayanan karya dangane da rikici, musamman a yankunan Afirkan da ke fama da rikicin kabilanci.
Kungiyar SAIDA International e.V, wata kungiyar tallagin Jamus ce ta fara wallafa bidiyon ranar 8 ga watan Yunin 2021. A wannan lokacin, taken da aka wallafa da bidiyon a harshen Jamusanci aka rubuta wadda fasarar ke bayani kamar haka: #solhan na tserewa dan neman mafaka a cikin kasarsu: sai ka ce al’ummar Burkina Faso wadanda ke cikin kasashe mafi talauci a duniya basu da matsalolin da suka riga suka yi musu yawa.”
Haka nan kuma labarin na Facebook ya zo daidai da rahoton gidan talibijin na Al Jazeera wanda ya rawito cewa iyalai fiye da 7,000 syn guda daga Solhan, wani kauye a Burkina Faso, bayan kisar da aka yi wadda ita ce mafi muni a cikin shekaru shidan da aka shafe ana tawayen jihadi a yankin. Bacin haka kafofin yada labaran Burkina Faso a yanar gizo irin su Lobs Paalga su ma sun dora bidiyon mai tsawo a shafinsu na YouTube oranar da abun ya faru.
Tun ba yau ba kungiyoyin binciken gaskiya sun tantance sahihancin wannan bidiyon kamar yadda za ku iya gani a wdannan shafukan, DUBAWA, AFP, da The Cable, dTun shekarar 2021 sadda lamarin ya fara afkuwa.
A Karshe
Bidiyon da ake da’awar wai mutanen Zamfara ke kokarin tsira da rayuwarsu, ba ma a Najeriya ba ne, tsohon bidiyo ne wanda ya fito daga Burkina Faso.
Wannan bincike an yi shine a shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 karkashin shirin kwararru na Kwame KariKari Fellowship da hadin gwiwar Crest 91.1FM, Ibadan, and News Verifier Africa, a kokari na fito da “gaskiya” a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin Najeriya.