African LanguagesHausaMainstream

Babu Hujjar cewa Peter Obi ne mahaifin yaron da aka gani tsaye kan tutar Najeriya cikin wani hoton da ake ta yadawa

Zargi: Hoton wani mutumi mai sanye da riga mai launukan ‘yan awaren Biafra, wanda ke tsaye a wani taron da ya yi kama da gangami a wata kasa ta daban wadda ba  Najeriya ba, na dauke da bayanin da ke zargin wai wanda ke cikin hoton Oseloka Obi ne wanda mahaifinsa ke takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Leba wato Peter Obi

Babu hujjar da ke nuna cewa mutumin cikin hoton dan Peter Obi ne, bacin haka masu magana da yawun Peter Obi sun ce ba su san hoton ba kuma dan takarar ba shi da wata alaka da wanda ke ciki

Cikakken labari

Ranar lahadi 3 ga watan Yuli shafukan sohsiyal mediya suka cika da hotunan wasu samari biyu an jera su gefe da gefe, a wani yunkuri na bayyana Oseloka Obi, wanda mahaifinsa ke takarar neman shugabancin kasar a karkashin inuwar jam’iyyar Leba wato Peter Obi. Hoton ya nuna saurayin yana tsaye kan wata tutar Najeriya  yana kira da a tabbatar da jamhuriyar Biafra a matsayin kasa mai cin gashin kan ta.

Yayin da ba’a tabbatar da sunan saurayin da ke hoton farko ba, wanda ke tsaye a kan tutar Najeriyar, saurayin da ke dayan hoton Oseloka Obi ne kuma fuskar ce kadai a hoton.

An yi ta raba hoton a shafukan Facebook da Tiwita masu tsokaci na tofa albarkacin bakin su suna cewa Peter Obi ba irin mutumin da za’a yarda da shi ba ne har a danka mi shi makomar Najeriya.

Daya daga cikin shafukan da suka wallafa hoton sun yi mi shi taken “2023: Peter Obi da matsalar gina kasa – Mutumin da ke cin mutuncin tutar Najeriya a cikin wannan hoton Gregory Oseloka Obi ke nan. Mahaifinsa ne ke takarar neman kujerar shugabancin kasar a jam’iyyar Leba, @peterobi. Ku yi tunani mai zurfi kafin ku mika wa mahaifin wannan mutumin Najeriya.”

DUBAWA ta kula cewa hoton ya janyo mahawara tsakanin magoya bayan Peter Obi da masu amfani da soshiyal mediya.

Wani mai amfani da shafin Tiwita ‘Bettors Companion ya bukaci dan takarar da ya nemi gafara daga wurin jama’a saboda hoton na nuna dan sa a irin yanayin da bai dace ba.

Ya rubuta: @peterobi, idan ka yarda, ka zo ka nemi gafara dan wannan labarin ya sanya dan ka a wani yanayin da bai dace ba.

Wani mai amfani da tiwitar kuma @OKARIA cewa ya yi “shekarun shi nawa?  shi yaro ne ko babba? Idan har shi babba ne shi ya kamata ya dauki nauyin amsa laifukan da ya aikata. Ku na korafi kan mutumin da ya tsaya a kan tutar ne, ba wadanda su ka harba harsasan da suka la’anta tutar ba. #cheap blackmail#

Sai dai wadansu daga cikin masu amfani da soshiyal mediyar ba su yarda da abubuwan da aka fada ba inda su ka ce lallai hotunan na bogi ne kuma ba su da dangantaka.

Tantancewa

Da DUBAWA ta gudanar da bincike kan hoton da ya nuna mutumin da ke sanye da rigar da ke da tambarin ‘yan awaren Biafra a manhajar binciken hotuna ta google, sakamakon ya nuna cewa hoton ya bulla a karon farko ne ranar daya (1) ga watan Satumba 2021 cikin wani sakon Tiwita a shafin da masu ra’ayin ‘yan awaren Biafara suka kirkiro a watan Ogostan 2020.

Shafin ya yi wa hoton taken “Wannan tutar gidan dabbobi (Zoo) ce. Da kyau”

Karin bincike ya nuna cewa ba wannan ne karon farkon da magoya bayan ‘yan awaren Biafarar ke amfani da hoton ba.

A cikin hoton, akwai wata motar ‘yan sanda a bayan fagen. Nan ma bincike ya nuna cewa motar ta ‘yan sanda ce a jihar Munich na kasar Jamus.

Daga nan DUBAWA ta yi amfani da kalmomin “zanga-zangar Biafra a Jamus” wanda ya kai mu ga wani rahotan da saharatareporters ta wallafa mai taken: “Magoya bayan Biafra sun afkawa ofishin jakadancin Burtaniya a Jamus sun bukaci a sako  Nnamdi Kanu.”

A cewar rahoton, magoya bayan ‘yan awaren Biafran  sun yi zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Burtaniyan da ke birnin Berlin na kasar Jamus dangane da kame shugaban kungiyar wato Nnamdi Kanu da gwamnatin Najeriya ta yi.

Wadansu hujjojin da aka dauko daga bidiyon da aka hada da rahoton ya kai DUBAWA zuwa wani bidiyon da aka wallafa a shafin Biafran da ke Facebook. Bidiyon na dauke da taken “IPOB ta bukaci sake Mazi Nnamdi Kanu da kuma kuriar jin ra’ayin da za ta tabbatar da girkuwar Biafra a matsayin kasa mai cin gashin kanta, wato #Biafraexist”

DUBAWA ta kuma duba kasidun da aka yi amfani da su da ma yanayin muhallin wurin da aka dauki hoton ta yadda ta sami tabbacin cewa da hoton da bidiyon da ta gani duk a wuri daya aka dauke su.

Da DUBAWA ta sake gudanar da bincike dangane da hoton na biyu ta sami tabbacin cewa hoton na Oseloka Obi ne wato dan Peter Obi.

DUBAWA ta gano cewa Oseloka Obi dan wasa ne a Hollywood kuma mamba a kungiyar ‘yan wasan kwaikwayon Burtaniya wanda ake wa inkiya da ELOKA IVO

Da mu ka kwatanta hoton Oseloka Obi da na mutumin da ke sanyan da kayan da ke da tambarin tutar Biafra mun ga cewa akwai bambambanci sosai tsakanin mutanen biyu musamman a siffa da wasu abubuwa da dama.

Duk da cewa DUBAWA ba ta iya samun cikakken bayani dangane da mutumin da ke tsaye kan tutar Najeriyar ba, binciken da ta yi ya nuna mata cewa lallai wannan mutumin ba Oseloka Obi ba ne kuma ba abun da ya hada shi da wannan mutumin da masu amfani da soshiyal mediya ke kokarin kwatantawa da shi. Bugu da kari Oseloka na zama a Burtaniya ne a yayin da zanga-zangar kuma a Jamus aka yi.

Baya ga haka, DUBAWA ta tuntubi Valentine Obienyem, mai baiwa dan takara Mr. Obi shawara kan kafofin yada labarai wanda ya kwatanta labarin a matsayin “sharrin ‘yan adawa”

Mr. Obienyem ya hakikance kan cewa Oseloka bai taka tutar Najeriya ba.

Ya kara da cewa: “Matashin da ya yi hakan ba dan Mr. Peter Obi ba ne wanda saboda irin tarbiyar da aka yi masa, yana da fahimtar abin da ake nufi da alhakin da ya rataya a kan kowani dan kasa.

“Mr. Oseloka na da tsawon kafa 6 ya ma fi mahaifin shi tsawo alhalin wanda aka yi amfani da shi a hoton iyakacin tsawon shi kafa 5.”

A Karshe

Babu wata hujjar da ta nuna cewa mutumin da ke cikin hoton da ya bi gari yaron Peter Obi ne. Masu baiwa dan takarar shawara kan kafafen yada labarai sun ce hotunan da aka sa basu da wata alaka a yayin da DUBAWA ta gano cewa an dauki hoton ne a Jamus.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button