African LanguagesHausa

Yaya gaskiyar batun wai Atiku ne ya jagoranci kungiyar kula da tattalin arzikin da ta biya basussukan Najeriya?

Bashin Najeriya na farko daga Paris Club mai yawan dalan Amurka milliyan 13.1 ta karba ne daga hannun gwamnatin Italiya a shekarar 1964 domin gina Madatsar Ruwan Neja.

Kasar ta cigaba da cin bashi tun daga wannan lokacin ko da shi ke ba ta ci da yawa sosai ba sai har sai sadda aka gano man fetur tsakanin 1971 da 1981 wanda ya kara yawan kudin da aka ciyo bashi. To sai dai da farashin man ya karye a kasuwannin duniya a shekarar 1982 sai Najeriya ta gaza biyan basussukan da ta ciyo.

Da karuwan da aka samu a kudaden ruwa da kuma tarar da aka rika ci sai kasar ta shiga wani yanayi na rikicin bashi. Wannan haka ya cigaba da kasancewa a duk gwamnatocin sojin da aka rika yi sai da ya zo kan mulkin Obasanjo wanda ya kaddamar da yakin rage bashin da ke kan kasar.

A karshen watan Disembar 2004 bashin da ke kan Najeriya ya kasance dalan Amurka biliyan 36 wanda ke zaman nera triliyan 4.82 idan aka yi amfani da darajar nera da dala a wancan lokacin a kan Nera 134 wa dala guda.

Ranar 29 ga watan Yunin 2005 yunkurin da ake yi na rage bashin ya yi nasara lokacin da Paris Club da Najeriya su ka cimma wata yarjejeniyar da ta rage mata bashin da dala biliyan 18.

Kwanan nan wani sako ya fara yawo yana zargin cewa dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP Alhaji Abubakar Atiku wanda ya kasance mataimakin shugaban kasar a wancan lokacin ne ya jagoranci tawagar tattalin arzikin da ta biya bashin. Wannan batu ya janyo mahawarori shi ya sa DUBAWA za ta binciki gaskiyar batun.

Yaya za’a kwatanta Economic Managemant Team ko kuma kungiyar gudanar da tattalin arziki?

Kungiyar gudanar da tattalin arziki (EMT) kungiyar kwararru ce wadanda ke gudanar da ma’adinai, kudi, kudaden shiga, da kudaden da ake batarwa a kasa domin baiwa shugaban kasa shawara dangane da batutuwan da suka shafi manufofin tattalin arziki.

A halin yanzu mataimakin shugaban kasa ne ke jagotantar EMTn Najeriya tare da Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren kasa da mataimakin shi, da Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Ministan Noma, Ministan Yada Labarai da Al’adu, Gwamnan Babban Banki, Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki, Darakta Janar na ofishin kula da kasafin kudi, Darekta Janar na ofishin kula da basussuka da kuma Darekta-Janar na ofishin kula da yawan al’umma.

Shin haka wannan tsarin ya ke a lokacin da Atiku Abubakar ya kasance mataimakin shugaban kasa?

Me Kundin Tsarin Mulkin Najeriya Ya Ce?

EMT wanda a kundin tsarin mulki aka bayyana shi a matsayin Economic Managemant Council wato  Majalisar/Mashawarta kan gudanar da tattalin arziki yana karkashin reshen majalisar zartarwar gwamnatin tarayya. Wannan majalisa ta na karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa

Kadan daga cikin abin da kundin tsarin mulkin kasar ya fada dangane da wannan batun:

H- Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa

18. Majalisar gudanar da tattalin arzikin kasa zai kunshi mambobi kamar haka:

  1. Mataimakin shugaban kasa wanda zai kasasnce jagora
  2. Gwamnonin kowace jiha a gwamnatin tarayyar; da
  3. Gwamnan babban bankin Najeriyar wadda aka kafa a karkashin dokar ta babban bankin Najeriyar da aka samar a 1991 ko kuma duk wata zartarwa da ta maye gurbin wannan dokar.

19. Majalisar gudanar da harkokin tattalin arzikin na da ikon bai wa shugaban kasa shawara kan duk batutuwan da suka shafi tattalin arzikin kasar da ma musamman duk irin matakan da su ka kasasnce wajibi a dauka wajen aiwatar da shirye-shiryen tattalin arziki a gwamnatocin da ke tarayyar.

I. Majalisar Shari’a Ta Kasa

20. Majalisar Shari’a ta kasa za ta kunshi mambobi kamar haka

  1. Babban mai sharia wanda zai kasance shugaba
  2.  Alkali mafi girma a kotun kolin kasar bayan babban mai sharia, wanda zai kasance mataimakin shugaban majalisar

A wani rahoton da jaridar The Punch ta rubuta, Mr. Abubakar ya ce shi ya shirya kwamitin tattalin arzikin, a wani labarin kuma wanda jaridar The Guardian ta rubuta ta ambato Mal. Abubakar din na cewa shi ya jagoranci kwamitin.

Duk da cewa kundin tsarin mulkin kasar ta bayyana mataimakin shugaban kasar a matsayin wanda ke da hurumin jagorantar majalisar gudanar da tattalin arzikin kasa, bincike ya nuna cewa Dr. Ngozi Okonjo-Iweala wadda ke shugabancin Kungiyar Cinikayya Ta Duniya WTO a yanzu, ita ce ta jagoranci kwamitin na EMT, wanda ya wanke Najeriya daga basussukan Paris Club.

Bisa bayyanan da aka bayar a tarihin rayuwarta da ke shafin WTO, Okonjo-Iweala wadda ta kasance ministar kudi a Najeriya sau biyu, daga 2003 zuwa 2006 da  2011 zuwa 2015, ita ta kaddamar da tattaunawa tsakanin Najeriyar da masu bayar da bashin na Paris Club.

“A matsayinta na ministar kudi a Najeriya, ta kaddamar da tattaunawa tsakanin Najeriya da masu bayar da bashi a Paris Club wadda har ta kai ga biyan bashin Najeriya na dala billiyan 30, har da wani billiyan 18 din na dala da aka yafe baki daya,” a cewar tarihin rayuwar. 

Wani rahoton da aka yi ya kuma bayyana cewa Okonjo-Iweala ce ta jagoranci kwamitin tattalin arzikin shugaba Olusegun Obasanjo.

A cewar wata takarda daga Ofishin Kula da Bashi wato Debt Managemant Office (DMO) dangane da Yarjejeniyar Bashin Najeriya da Paris Club,” An yi nasara ne sakamakon hadin gwiwar da aka yi tsakanin Shugaban Kasa, Ma’aikatar Kudi, Majalisar Dokoki, DMO, EMT da sauran masu ruwa da tsaki a kasar.

Dan haka idan aka ce mataimakin shugaban kasa shi ne shugaban majalisar gudanar da tattalin arzikin kasa daidai ne amma ba daidai ba ne a ce shi ne ya jagoranci tattaunawar da ya kai ga biyan bashin da Najeriya ta ci daga Paris Club.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button