African LanguagesHausa

Mahukuntan Burtaniya ba su kama tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura wajen Ekweremadu ba

Zargi: Wani mai amfani da shafin Facebook na zargin wai tawagar da gwamnatin tarayyar Najeriya ta tura zuwa Burtaniya domin samo wa Ekweremadu lauyoyi sun shiga hannun mahukuntan kasar

Bincikenmu da kuma tabbacin da mu ka samu daga jagorar tawagar wadda ba ta riga ta bar Najeriya ba, sun nuna mana cewa wannan zargin ba gaskiya ba ne

Cikakken labari

Ranar 23 ga watan Yuni aka sami labarin cewa jami’an ‘yan sanda a Burtaniya sun kama Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar tare da mai dakinsa Beatrice bisa zarginsu da daukar gabobin jikin dan adam ta haramtaciyyar hanya.

‘Yan sandan sun tuhumi Mr. Ekweremadu da laifin fataucin wani mai suna David Nwanini da nufin cire kodarsa.

Da ta ke mayar da martani dangane da wannan batun ranar laraba 29 ga watan Yuni, majalisar dokokin ta ce za ta tura wata tawaga daga kwamitin da ke kula da harkokin ketare a majalisar domin su je Landan su ga Ekweremadu da matarsa.

Bayan samun wannan labarin ne wani mai amfani da shafin Facebook, Inakede Denis ranar lahadi 3 ga watan Yuli 2022 ya wallafa wani zargi, inda ya ce tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura domin ta dauko wa Ekweremadu lauyoyi ta shiga hanun gwamnatin Burtaniyar.

Sarkakiyar da wannan batu ke da shi ya sa ya ke da mahimmanci jama’a su sami bayanan gaskiya da ma irin lahanin da wannan zai iya yi ga kimar mutanen da ke tawagar da ma kasar baki daya ne ya sa DUBAWA ta ke so ta fayyace gaskiyar wannan labarin.

Tantancewa

Da muka yi binciken mahimman kalmomi ba mu ga wani rahoto dangane da batun a shafukan labaran gida da waje ba.

Sai DUBAWA ta tuntubi mai magana da yawun ma’aikatar kula da harkokin waje, Ferdinand Nwoye ta hanyar sakon text da waya ba tare da yin nasara ba.

Mun kuma tuntubi Uche Anichukwu mai magana da yawun Mr. Ekweremadu, shi ma ta hanyar text da waya amma ba mu yi nasara ba har zuwa lokacin da muka wallafa wannan labarin.

A shafukan ‘yan sandan Burtaniya da ma na gwamnatinsu, ba mu ga wani rahoto dangane da batun ba kuma babu wata sanarwar manema labarai dangane da batun. Dan haka ne muka tuntubi ofishin ‘yan sandan Burtaniyar ta hanyar sakon text da waya. Ya zuwa lokacin da muka wallafa wannan labarin ba mu ji daga wajensu ba.

DUBAWA ta kuma tuntubi shugaban kwamitin kula da harkokin kasashen wajen da ke majalisar dokoki, Adamu Bulkachuwa ta hanyar whatsapp, wanda shi ne ma ya kasance jagorar tawagar da tafi Landan. Mr Bulkachuwa ya tura amsa mu ya kuma karyata zargin inda ya ce mana tawagar ba ta ma bar Najeriyar ba ma tukuna.

“Ni ne shugaban tawagar kuma sai gobe za mu tashi,” ya ce, “Ta yaya za’a ce tawagar da ba ta ma tashi ba an cafke ta a Burtaniyar?

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya ce ziyara ce kadai tawagar za ta kai wa Ekweremadu ba lauyoyi za ta je saman mi shi ba kamar yadda ake zargi. Mr. Lawan ya kuma kara da cewa ofishin jakadancin Najeriya ta riga ta daukar mi shi lauyoyin da za su je kotu da shi sadda ake bukatan shi ya je kotu.

Wani rahoton da jardar Premium Times ta rubuta ya ce lokacin da Mr. Ekweremadu ya bayyana a kotu ranar alhamis 30 ga watan Yuni 2022, wata babbar tawaga daga ofishin jakadancin Najeriya ta kasance a kotun tare da yaran sanatan guda biyu.

A Karshe

Bincikenmu da ma jagorar tawagar dun sun fayyace man cewa tawagar na nan cikin koshin lafiya kuma babu wanda ya cafke ta.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button