|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wata wallafa a shafin Facebook (claims) ta yi da’awar cewa gwamnan Zamfara ya tura ‘yanbijilanti da aka fi sani da Askarawa 500 don shawo kan matsalar tsaro ta hanyar “ shiga yaki da ‘yanfashin daji ko ‘yanbindiga maimakon jira sai sun kawo hari.’’

Hukunci: Babu isassun shedu, duk da cewa gaskiya ne an kaddamar da Askarawan a watan Janairu, 2024 a matsayin dakaru daga bangaren gwamnatin jiha wadanda za su mara baya ga sojoji da ‘yansanda, babu wata sheda da ta nuna gwamnan Zamfara ya tura ‘yan bijilanti 500 da za su je yakar ‘yan fashin daji su kadai.
Cikakken Sako
Jihar Zamfara Arewa maso Yammacin Najeriya ta kswashe kimanin shekaru 10 tana fama da hare-hare (ruthless armed attacks) dalilin ayyukan ‘yanbindiga wadanda ayyukansu ya bunkasa ya zama na ‘yanta’adda. Guggun ‘yanbindiga kan afkawa gari ko su tare hanya ko su kama mutane su nemi kudaden fansa. Tun daga shekarar 2011 tarin (waves) hare-hare irin wadannan sun sanya mutane da dama sun kauracewa muhallansu wasu kuma da dama an halaka su.
Hukumomin jinkai sun yi kiyasi (estimate) cewa akwai dubban al’umma da aka raba su da muhallansu(displaced) a sassa daban-daban na jihar.
Wani mai amfani da shafin Facebook @D English Alhaji, yayi da’awar cewa gwamnatin jihar (Zamfara State) ta amince da tura ‘yan bijilanti ko ‘yankato da gora 500 da za su tunkari ‘yanfashin daji.
A wani bidiyo ya nuna wani mutum na cewa “Gwamnatin Zamfara ta yi nata bangare a kokari na tunkarar matsalar tsaro da jihar ke fuskanta. Ana kiransu da suna Askarawa, ko kuma masu yaki da matsalar tsaro a jihar inda suke gudanar da aikinsu a jihar ta Zamfara. Ba suna jira ba ne a kawo hari kafin su yi abin da ya dace, yanzu suna tunkarar ‘yanbindigar ne.” Ya yaba da kokarin da suke yi inda yace dama Najeriya irin wannan kokari take fatan gani.
Bidiyon na nuna mutane akan babura wadanda mai bayanin yace su kusan 500 ne wadanda gwamnatin ta basu ababen hawan.
Ya zuwa ranar 25 ga Satumba,2025 wannan bidiyo ya samu wadanda suka kalla 69,000 (views), da wadanda suka sake yadawa 155 (shares) da wadanda suka yi tsokaci 4,300 (comments).
Mun duba tattaunawa da masu amfani da shafin na Facebook ke yi kan wannan batu ga kuma abin da wasu daga cikinsu ke cewa:
@Kingston Samuel ya rubuta cewa , “ Idan lamura suka kwanta, suka kuma tarwatsa gungun, ina fatan gwamnatin jihar Zamafara za ta ba da bayani na dukkanin kayan aiki da aka ba wa ‘yanbijilantin.”
@Chibuzor Patrick yace, “‘Yansiyasa marasa amfani nan ba da dadewa ba za su bayyana bukatar ganin gwamnatin Zamafara ta janye mutanenta suna da’awar cewa ‘yanbindigar sun tuba.”
@Moor Moor yayi tsokaci da cewa “Ba da wata-wata ba za su mika wadannan babura ga ‘yanbindigar.”
@Brazy Slime na mai ra’ayin“ Su tabbatar da ganin cewa babu ‘yanfulani a cikin mayakan, idan ba haka ba za a yi nasara a kansu, zai zama kunar bakin wake idan ya kasance akwai Fulani a wannan tafiya, suna nan a cikin sojoji ma na kasa da na sama da na ruwa suna kawo cikas.”
Wasu da dama cikin masu tsokaci na nuna shakkunsu a dangane wannan da’awa. Destiny Charles yace shin kana Zamafara ne ka tabbatar da wannan da’awa ko dai kawai kana zuba surutu ne mara amfani. Shi kuwa @Nonso Ogbonna yace “dan’uwa a ina kake samu wadannan bayanai? Ni ina zaune ne a Gusau jihar Zamfara. “
Ganin irin wannan da’awa da irin tsokaci da mutane ke yi hakan ya sanya DUBAWA ganin wajibcin nitsawa da bincike don tantance wannan da’awa.
Tantancewa
DUBAWA ta fara gudanar da bincikenta ta hanayar amfani da wasu kalmomi daga abin da aka wallafa a shafin na Facebook alal misali “Gwamnan Zamfara” da “masu yakar ‘yanbindiga” da “dakarun Askarawa” abin da binciken Google ya gano ya hadar da wasu da’awowin irin wannan a shafukan X da Facebook.
Wani a shafin X, @Future President, a ranar 13 gacwatan Satumba,2025 ya yada cewa “Gwamna Dauda Lawal ya fara lugude kan ‘yanbindiga inda ake amfdani da dakarun da jihar ta samar na Askarawa da ‘yankato da gora CJTF.”
A shafin Facebook ma, (@Shehu Umar) ya yada labarin irin wannan (similar) a dai wannan rana.
Domin tantance bidiyon ta hanayar amfani da dabarun gano asalin bidiyo a Google da Yandex , babu wata kafa da za a ce ga asalin inda aka samo bidiyon, abin da kawai ake gani shine wannan dai bidiyo da aka wallafa a shafin na Facebook ko na X, kamar dai yadda aka gani a bincike ta hanayar amfani da muhimman kalmomi da aka yi a Google tun da fari, duka dai abu guda ake gani da taken labarin iri daya. Wannan ya nuna cewa wannan bidiyo tun da fari da aka gani a kafafan sada zumuntar guda biyu su kenan babu wata kafa a hukumance ko wata kafar yada labarai sahihiya da ta yi labarin.
Da muka kara bincikawa sai muka ga cewa akwai kafa ta hukuma da ta nuna yadda a ranar 31 ga Janairu,2024 Gwamna Dauda Lawal ya kaddamar (launched) da rundunar ba da kariya ga al’umma ta Community Protection Guards (CPG), wadanda aka fi sani da Askarawa, Kafafan yada labaran sun bayyana CPG a matasayin rundunar tsaron da ta samu goyo bayan gwamnatin jiha da nufin tallafawa jami’ai na gwamnatin tarayya.
Karin bayani a yayin kaddamarwar jami’an su 2,645 ne da suka kammala (completed) samun horo na farko inda aka bayyana za a samar da karin wasu inda ake sa ran samar da mambobi 5,200, wanda yawansu ma yafi adadin da aka bayyana a wallafar ta Facebook.
Wasu rahotannin kuma sun bayyana cewa gwamnan jihar ta Zamfara Dauda Lawal ya bada motoci da babura ga jami’an tsaro na cikin gida, A ranar 16 ga Agusta,2022 jami’an gwamnatin jihar sun raba ( distributed) babura 1,500 da motocin sintiri 20 don samar da tsaro a yankunan al’umma, haka kuma a ranar 13 ga watan Mayu,2025 gwamnan jihar ya mika (handed) sama da motoci 140 zuwa ga huumomin tsaro.
Duk da cewa wannan na nuna irin kokarin gwamnati na bunkasa tsaro, babu wata sheda da ta nuna cewa an yi wanann rarrabawa a baya-bayan nan, kamar yadda masu amfani da shafukan na sada zumunta suka nunar.
A karshe mun gano cewa su jami’an na CPG suna aiki ne (works) tare da sojoji da ‘yansanda a wurare da ke da wahalar sha’ani, wannan yasa suke aiki tare a wurare irin su dajin Sunke inda aka ga dakarun na CPG suna gudanar da ayyukansu a wuraren da ‘yanbindigar (bandits) ke buya. Kamar yadda me fadin ke cewa gwamnati ke nuna yadda za su yi aiki wato cewa “ku karbi aikin ku danna cikin dajin” wato su kadai ba haka bane.
Bayanin Mahukunta
DUBAWA ta tuntubi gwamnatin jihar Zamafara ta hanyar adireshinta na e-mail wato (zitda@zamfara.gov.ng) amma har zuwa lokacin kammala wannan aikin gano bayanan gaskiya babu wata amsa daga bangaren na gwamnati.
Haka kuma ita ma lambar da ke kan shafin intanet na gwamnatin mun tuntuba babu amsa, sai kuma a karshe muka tuntubi jami’in hulda da jama’a a rundunar ‘yansanda ta jihar Zamfara don neman karin bayani, shima ana tsaka da tattaunawa da shi ya katse tattaunawar, kuma duk yunkuri na sake kiransa babu amsa.
A Karshe
Binciken DUBAWA ya tabbatar da cewa akwai dakarun na Askarawa ko CPG wadanda aka kafa su a watan Janairu,2024 a kokarin gwamnatin jihar ta Zamafa na tallafawa ayyukan tsaro na jami’an soja da ‘yansanda, sai dai babu wata sheda da ta nuna cewa gwamnati ta ba su umarni su je su kai wa ‘yanbindiga hari su kadai ba tare da soja ko ‘yan sanda ba.



