Zargi: Wani mai amfani da shafin Facebook na zargin wai kamfanin da ke kula da tashoshin POS na bayar da tashoshin kyauta ga ‘yan Najeriya
Bincikenmu ya nuna cewa Opay ba ta bayar da wasu tashoshin POS kyauta. Sai dai ta yi hakan a baya a matsayin talla dan jan hankalin jama’a amma tun daga makon farko na watan Yuli aka dakatar dan haka zargin ba daidai ba ne
Cikakken labari
Kwanan nan wani mai suna Atoshu Elias ya shiga wani shafi a Facebook wanda ake kira “NIGERIA POLICE FORCE ALONE” inda ya sanar cewa kamfanin Opay na bayar da tashoshin POS kyauta hade da ma alkawarin yin rajista kyauta ya kuma bukaci duk wadanda ke sha’awa da su rubuta hakan a karkashin labarin tare da lambar wayar tarhonsu da inda suke zama.
Ga abin da ya fada a sanarwar ta sa: OPAY NA BAYAR DA NA’URAR POS KYAUTA, DUK MAI SHA’AWA YA RUBUTA LAMBAR WAYA DA UNGUWA, RAJISTA KYAUTA NE.”
Ba tare da wata tantama ba, mutane 60 suka rubuta bayanansu a karkashin sanarwar.
Opay kamfanin da ke da mazanin shi ne a Najeriya wanda dandali ne na samar da kudi a hannu inda kwastamomi ke iya ajiye kudi ko cirewa a duk inda su ke so ba sai sun je banki ba.
Kamar yadda yake rubuce a shafin kamfanin, babban bankin Najeriya ce ta ba shi lasisi kuma ana iya samun shi ko’ina a Najeriya tun bayar da aka kirkiro kamfanin a shekarar 2018.
Yanzu da amfani da POS ya zama babban hanyar samun kudaden shiga a Najeriya, ba abin mamaki ba ne a ga jama’a sun nuna sha’awar dama irin wannan. To sai dai DUBAWA ta lura cewa mayaudara ma kan yi amfani da irin wadannan hanyoyin wajen zambatar mutanen da ba su ji ba su gani ba. Wannan ne ya sa DUBAWA ta ga cewa ya dace a tantance gaskiyar lamarin.
Tantancewa
Da farko DUBAWA ta duba shafin Facebook na kamfanin Opay inda ta lura cewa babu wani bayanin da ke da alaka da wannan batun. Haka nan kuma ta kara da duba shafin kamfanin inda nan ma babu wani abun da ke bayanin cewa kamfanin na kyautar da wani abu.
Daga nan ne DUBAWA ta tura sakon email zuwa ga manejan sadarwar kamfanin Mr. Hanson Olorunfemi, wanda ya tabbatar cewa lallai ba da dadewan nan ba ya bai wa wadansu kananan ‘yan kananan ‘yan kasuwar da ke tunanin amfani da na’urorin gajerun tashoshi, wadanda ake kira mini POS. Mr. Olorunfemi ya ce sun bayar da kananan tashoshin kyauta ne ga duk wadanda ke tunanin amfani da na’urar a sana’o’insu nan gaba a fadin kasar.
Sai dai ya ce wa’adin yin hakan ya riga ya cika tun daga makon farko na watan Yulin 2022.
“Wanda ke da sha’awa na iya sauke manhajan Opay sa’anan ya tambaya a ba shi tahsa. Daga nan ne za’a hada shi da wanda zai bude mi shi tashar.”
“Domin samun dama, wajibi ne mutun na da wajen yin sana’ar kuma sai ya cika sharuddan KYC (wato bayanann da za su taimaka wajen fahintar kwastomomi) musamman KYC 3.
Mutun na uku a nan shi ne zai kasance daya daga cikin wadanda aka tantance su rika bayar da tashoshin na POS bisa bayanin da Mr. Olorunfemi ya yi.
A Karshe
Bincikenmu ya nuna mana cewa Opay ba ta bayar da kyautar tashoshin POS a yanzu haka. Ko da shi ke kwanan nan ta bayar da wadansu kananan tashoshi dan talla, amma tun a farkon watan Yuli aka gama wannan tallan.